👑SHUGABA👸12

407 38 0
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 12*

✏️Wani akwati taga ya jawo, nan ya soma zuba kayayyakin ta a ciki

A hankali ta ce"Pumpkin abin fa bai kai haka ba!"

Ko kallon ta bai yi ba ya cigaba da abin da yake yi, daga karshe dai gyara kwanciyan ta tayi a kan gado tana kuma zuba mai idanuwa, kafin kace kwabo har bacci yayi gaba da ita...

"Yanzu miye zamu yi??"Babynmourad ta fad'a cikin takaicin abin da suka yi

"Muje gidan su daddy mu fad'a mai yanda akayi in taso ya bimu ya roka mana babanmu saboda yanda yayi magana yanzu akwai tsorotar wa kar mu je da kanmu ya wan-wanka mana mari

Nan ta amince da abinda ya fad'a, ba b'ata lokaci suka dunguma zuwa gidan Dady

★★★★★★★★★★

✏️✏️Zaro idanuwa Amaya tayi cikin firgicin jin abinda ya ce

"Ya ce zai aure ki!" Shugaba ta fad'a tana nazarin Amaya din

Girgiza kai Amaya tayi a lokaci daya kuma hawayen tausayin kan ta na zubo mata

"Bana son irin wannan auren! Nasan daga karshe muzguna mun zai yi"

"DanAllah kiyi hakuri wallahi bazan muzguna miki ba, wallahi ko aure bazan kara ba, ke dai ki taimaki rayuwa ta!"Zad boy ya fad'a cikin kuka sosai kaman ba namiji ba

"Kuna b'ata min lokaci!" Shugaba ta fad'a cikin kaguwa

Arsh ne yayi gyaran murya yace"A tafi ta wa'inan biyun a musu bulalu 99 kaman yanda hukuncin su yake a rubuce a takaddar hannun su"

Nan aka fitar da su suna kuka, rarrafawa wajen Amaya Zad boy yayi yana rokan ta akan tayi hakuri ta yarda,

Dakyar da sud'in goshi Amaya ta hakura, suma ba b'ata lokaci a ka wuce dasu....

★★★★★★★★★★

✏️✏️✏️"DanAllah masoyiya kiyi hakuri wallahi bamu da masaniya akan abin da ya faru!"M² ya fad'a a marairaice

Cike da tausayin su take binsu da kallo ga Mourad sai wani tsare gida yake yi

Sallaman Alhaji Iqbal wato Dady ne ya miyar da hankalin su kan kofa

Cikin sauri babynMourad ta mik'e tare da karasawa wajen sa

"Ya naganku da Akwati??? Kar dai ta koya maka yanda ake tserewa??"Dady tambaya cikin zolaya yana mai mik'a wa Babansu hannu don yin musabaha

Kallon ku kuka kirawo sa babansu ya musu, nan suka fara girgiza kai suna mai hadiye miyau mai d'aci

"Ya na ga akwati kuma??"Dady ya tambaya kaman bai san komai ba

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now