Arsh's last wish

346 37 0
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 18*

#*_Arsh's last wish_*
B

asu hankara ba kawai suka ga BabynMourad ta hau kan ruwan cikin Nurse Jaziya

Nan fa kokawa ya kaure a tsakanin su, dakyar aka samu aka banb'are BabynMourad ajikin Nurse Jaziya

"Ki bari mana baby!"Ahzab ya fad'a cikin takaici, kuka babynMourad ta fashe dashi wanda hakan ya basu mamaki saboda babu karya Nurse Jaziya ta bugu kuma ita suke jira tayi kuka amma suka ga akasin hakan

"Wallahi kabarni, ai yau zata san uwata ta zaga!"

"It's okay!"

"Kaii ba wani nan wallahi sai nayi shari'a da ita!"Ta fad'a tana share hawayen fuskar ta, saboda abin ba karamin zafi ya mata ba, taya za'ayi tana raye wata sakarya ta zagi mamanta?, wani kukan ta sa cikin takaicin ganin bata gurji bakin Nurse Jaziya dakyau ba

Hannun Nurse Jaziya Mourad yaja tare da yin waje da ita

Juyawa wajen Nurse Haisama dake kokarin b'uya BabynMourad tayi sannan tace

"Ke k'awa ce kokuma miye?? Ke yanzu in tambaye ki? In baban ki zai k'aro wa maman ki abokiyar zama sai k'awarta na bata shawarin banza akan yanda yazata kuntata wa uwarki ya zakiyi?in tarbiyan da uwarki ta baki kenan toh am sorry cutarki tayi!Kuma let me tell you kema wallahi sai kinsan kinyi kuskuren bada shawara saboda bazan kyaleki ba!"

Tana gama fad'in haka suka fice, inda aka bar Nurses din wajen da kus-kus,ajiyar zuciya Nurse Haisama ta sauk'e cikin rashin sanin abinyi saboda su fa basu zaci haka abin zai juyo musu ba

Tattara kayayyakin ta tafara cikin sauri saboda daman sun gama dutyn su(night-Morning) saboda har wanda zasu karb'e su sun fara zuwa (Morning-Afternoon)

★★★★★★★★★

"Ke ki tsaya yanzu in kika yi abinda ke ranki mutane zasu d'auka ke mayya ce! Karki manta gaggawa aikin shaidan ne!"

Taji Ara ta fad'a, tsaki taja tare da tokarin sa da booth din kafarta da karfi

"Ki wuce dashi gida ina zuwa!"tana gama fad'in haka ta wuce tana barin sa yana rokan ta gafara

Cikin Class ta koma wajen Arsh dake kokawa da numfashin sa

M² da yayi mutuwar tsaye saboda abinda ya ke gani yanzu ne yayi ta maza tare da yin wajen su

Karasawa wajen su yayi tare da yin gyaran murya sannan yace

"Ku taimaka mun a kaisa asibiti!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now