The unexpected...

361 39 2
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 16*


'''The unexpected...'''

✏️Kwance yake akan gado ya lumshe idanuwan sa kaman mai bacci amma a zahirin gaskiya ba baccin yake yi din ba

Zama tayi a gefen sa cikin damuwa tare da cewa" ni dai nasan ba bacci kakeyi ba! So you better stand up and tell me what's wrong!"

Habawa wani irin bugawa kirjin sa yayi wanda yasa shi dafe kirjin da sauri

Cikin tashin ta matsa gefen sa, a hankali kaman mai tsoron magana tace"abun yayi tsanani kenan??"

Mik'ewa zaune yayi yana kallon kyakyawar fuskar matar tashi kaman yau ya fara ganin ta, runtse idanuwan yayi yana jin kaman ya kurma ihu ko hakan zai sa shi jin saukin rad'adin da zuciyar sa keyi

Cikin tausayawa dukkan su biyun ta rik'o hannun sa wanda hakan yasa shi bud'e idanuwan sa dake runtse

Saita idanuwan nata wanda har sun fara cika da hawaye tayi a cikin nasa

"You're a strong guy you know??" Ta tambaya tana shafa hannun

Girgiza kansa yayi alaman a'a, ware hannun ta daya tayi tace

"Come to me!"ba musu ya rugume ta kaman yanda take nufi din

"Good boy! Oya zaka iya yin kuka iya son ranka! I won't stop you!"ta fad'a a hankali

Kansa ya d'aura akan kafadar ta yana jin wani irin sanyi na rasta sa

Cikin rawar murya yace"Am sorry Mine!ban tab'a tunanin hakan zai faru ba forgive me please"

Wani irin kuka ne ya sub'uce mata wanda hakan yasa shi matse ta a jikin sa

Hawayen da taji ya d'igo kan kafadar ta ne yasa ta kara sautin kukan nata

Cikin sauri ya share hawayen sa saboda baya son ya kara mata wani zafin

"Am genuinely sorry Mine!"

Cirosa tayi tace" you don't have to, nima am sorry da nayi tunanin cewan zuciyan ka nawa ne ni kad'ai, na manta cewan zuciya bata da kashi!"

Girgiza kai yayi yana jin zafin zuciyar sa na karuwa, tukunna ma ya haka yi zuciyar sa ya buga akan wacce ba Zulynsa ba?? Gaskiya zuciyar sa bata mai adalci ba, har ya mutu bai tab'a fatan yaji son wata y'a mace ba wacce ba Zulynsa ba! Amma how comes??

M² dake kokarin shigowa d'akin tin dazu ne ya juya cikin sanyin jiki, ga kuma tausayin iyayen nasa wanda ya lullubesa musamman ma his Masoyiya wanda bashi da masaniya akan irin abin da take ji ba!

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now