60

290 54 16
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 59*


✍️Tsohuwa mai kimanin shekaru 70 ce a tsaye a bakin titi, kayan jikin ta abin a tausaya mata ne balle kuma ita kanta, duk ta kod'e tayi baki Saboda wahalan duniya...

Ganin ya fito daga gate din gidan kurkuku yana jira abin hawa ne yasa ta mik'e da sauri

Bata tsaya wata wata ba ta sa hannu acikin jakanta ta ciro dutse

Kwal! Kake ji ta kwala mai akai, cikin jin zafin dutsen ya lailayo wani ashar ya watsa mata wanda hakan ya janyo hankalin mutane

Kasancewan cikin gari ne harda karamin kasuwa a gefen wajen yasa mutane suka ta-taso cikin son Jin ba'asin miye ya faru harda d'ura wa tsohuwa ashar

"Miye faru??" Shine abinda wani ya tambaye ta, kuka mai tsuma rai ta fashe dashi wanda hakan yasa Baban Fareed tsayawa cike da mamaki saboda daman bai so tsayuwa ba

"Saboda rashin adalci ace shekara biyar kawai?? shekaru biyar kawai yayi a kurkuku bayan ya kashe ya'ya na dakuma mijina!"

"Mene??"mutane suka fad'a cikin had'in baki

"Wannan da kuke gani ba mutumin kirki bane! Abubuwan jikin mutane yake siyarwa!"ta fad'a tana chakumo wuyan rigan sa

"Dama shine mutumin kwanakin baya??"

"Gaskiya ne, ga shi nan ma anan!"wani ya fad'a yana nuna musu hoton baban Fareed a wayan sa

"Wai tou da na ganshi anan nufin su shine har ya gama hukuncin sa kenan??"

"This no dey do I swear! What if he continue doing what he has been doing before??that means he's coming for more of us!" Wani inyamuri ya fad'a

"Abinda ya fad'a gaskiya ne! Gwanda mu dau mataki kuna ganin yanda idanuwan sa suka bu-bushe!"

Wani irin rawa yaji jikinsa na yi cikin tsananin tsoron da ya darzu acikin Zuciyar sa

Baya ya fara yi yana cewa"kuyi hakuri... Bazan sake ba! Yanzu na shiryu!"

Daga baya yaji an bashi wani duka a k'eya, tsayawa yayi cak tare da sa ihu yana mai shafa bayan wuyan sa saboda ji yayi kaman guduma aka kwada mai a wajen

"Guduwa zakayi?? A tunanin ka zaka mana wayo ne bayan kaga fuskokin mu?? Ai aradu mutumin nan na barin nan gabadaya zamu kad'e saboda sarai ya rik'e fuskokin mu! Har gidajen mu zai biyo mu ya kwamushe mu har da y'a y'an mu!ai mai Hali baya fasa halin sa"wani bayarbe ya fad'a cikin tsoro yana mai tura baban Fareed tsakiyan su da kyau yanda bazai samu gujewa ba

Shiko sai girgiza kai yake yi zufa na k'eto mishi, Allah ne kawai yasan iyakacin yanda jinin jikin sa yake gudu a secon daya

Tsugunar dashi sukayi inda tsohuwan ta bashi duka mai zafi a baya

Aiko kaman jira suke yi nan suka rufe shi da duka ba ji ba gani, jina-jina sukayi mai wanda ko ido bai iya bud'ewa

Gabadaya mutane sun cika a kamshi, masu videoing nayi masu d'ura mai ashar nayi, masu  dukan sa nayi

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now