is she back??

311 53 4
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*


*Page 37*

_#Is she back??_
✏️A saba'in M² ya koma cikin gida don d'auko waya domin kiran yen sanda kaman yanda yar uwar sa ta bada shawara

Ihun da suka ji daga saman su ne yasa suka kalli wajen a tsorace,

Cikin firgita Smallie ta rungume maman su inda BabynMourad kuma ta bud'i baki cikin tsoro

"Wayyo zan fad'i!"ta fad'a cikin kuka da tsananin tashin hankali

"Ki tsaya awajen karki yi motsi,just stand still okay??bazaki fad'i ba!"babansu ya fad'a cikin son kwantar mata da hankali

Cikin kukan da babu hawaye ta tsuguna akan roof din sai kallon kasa take yi tana tunanin irin ciwon da zata ji in ta fad'i

Tunawa  tayi da wata da ta rasu a asibiti sanadiyan fad'uwa daga kan kujera aiko nan ta sake tsala ihu tana cewa

"Ku cire ni! Bana son na mutu!!"

M² da ya shiga d'auko waya ne ya dawo da gudu yana cewa bai gani ba

"Yaya! Matar ka!"BabynMourad ta fad'a ahankali wanda hakan zai nuna maka ma hankalin ta baya jikin ta, duk mata ukun sun gama shan kuka harma da M²

Lada aka d'auko aka ajiye a wajen, nan kuma wani sabon drama ya barke cos M² cewa yayi babu ma'aikacin da zai tab'a mai mata! inda su ZulynMourad suka d'age cewan bazai hau ba saboda yanda jikin sa yake b'ari kaman mazari

Haushi ne Yakama babansu nan kuwa yace ya hau in kuma sun fad'i babu ruwan sa acikin

Hannun Mourad Zuly ta damke cikin tsoro, kafada ya d'age mata alaman babu ruwan sa

Da Addu'a acikin zukatan su suka mai rakiya kaman wanda zai je filin yak'i

Cikin ikon Allah kuwa yayi ta maza yaje zai sauk'o da ita, daidai sun kusa gama sauk'owa ta sa ihu tana cewa ita bazata sauk'a ba

Nan fa hankalin su yasake tashi barin ma da suka ga ladan na rawa kaman zai fad'i duk da irin rik'ewan da ma'aikata mazan suka yi ta kasa

"Calm down! Bazaki fad'i ba!"M² ya fad'a cikin tashin hankali ganin zata nakasa su

Girgiza kai tayi tana cewa"mutuwa zamuyi! Macizan zasu sare mu in mun sauk'a!"

"Macizai??" Suka tambaya a tsorace,

"Baku ganin su ne kuke cewa mu sauk'o!? So kuke mu mutu ne!? Nikam bazan sauk'a ba!"

Duk iya dube duben su basu ga koda tsinke awajen ba, cikin son kwantar mata da hankali suke cewa

"Babu komai awajen Azeee ku sauk'o!"ZulynMourad ta fad'a

Ganin zai saukar da ita yasa ta fara haurawa sama tana cewa"ni kuna son in mutu ne?? Tace karna sauk'a! Ku barni danAllah!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now