22

292 39 0
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 22*

Cikin kwanciyan hankali yake tukin mota, babansa na gefen sa , BabynMourad da maman su kuma na baya

Juyawa Mourad yayi yace"Babynah babu wani labarin da za'a bani ne??"

"Actually akwai amma mamana tace wai na bari ka huta yau tinda ka kwaso gajiya!"ta fad'a tana murmushi

"Ohh that's nice, kuma dagasken na gaji sosai!"

"Shine kuma muka fito?"ZulynMourad ta tambaya

Hannun ta ya rik'e tare da cewa"ai ni ko Dubai zamuje a yanzu in har kina nan a shirye nake"

"Love!Sweet love!"BabynMourad ta fad'a tana sa kanta a kafadar maman ta

"Yaa! Yaushe zan ga budurwan ka Yaya??"

Sanda ya saki murmushi tare da buga steering alaman tambayan ya mai dadi kafin yace"Yaseen in kika ganta sai kin suma tsantsan mamaki!"

"Ta kai yah Ahzab dina!"ta tambaya tana hararan sa

"Taya zaki had'a ta da wannan??shi din wani kyau gare sa?? Ko kin tab'a suma da mamaki saboda kyan sa!kokuma kin tab'a tsintan kanki cikin halin rud'ani saboda ganin sa??"

"Dallah duk zubamu kakeyi!"ta fad'a tana ya mutsa fuska saboda ita fa babu wanda kallon sa zai sata cikin rud'ani

"Ai dama man..."

Wani irin birkin da yaja ne ya katse sa daga abinda zai fad'a

"Lafiya??"

Full light ya kunna tare da cewa"Kaman mutum achan wajen??"

Bud'e kofa ZulynMourad tayi da sauri ba tare da taji miye suke fad'a

Nan dukkansu suka mara mata baya, chak gabadayan su suka tsaya suna binta da kallo

Zaro idanuwa yayi cikin kidima, kaman zaiyi kuka yace"S... Señorita!?"

"What?"suka fad'a cikin had'in baki

Sunguman ta yayi tare da yin gaba da yana mai had'awa da gudu...

Tafiya da dawowa yake yi acikin asibitin cikin tashin hankali jin wai akwai bullet ajikin ta

Suma dukkansu sunyi jugum, babynMourad kam ma kwanciyan tayi akan cinyar maman su saboda baccin da yake fizgan ta

Fitowan doctorn ne ya shi zuwan wajen sa da sauri yana tambayan sa yanda aka yi

"Karku samu damuwa yanzu mun cire bullet din kuma an samu matsala daya!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now