👧 SHUGABA👑

1.2K 90 4
                                    

'''TYPING'''📱

* _ 👑SHUGABA👸 _*
(Cigaban Zulfa )

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence _

*_Mhizzphydo_*

*_Page 1_*

✏"Har yanzu tak'i yin magana neh? "Wani jibgegen k'ato ya tambaya da k'aton muryansa wanda ko kadan ba shi da dadin ji.

Cikin Tsananin ladabi ya rusuna yana fad'in "Eh oga har yanzu bata ceh komai bah duk da uban azaban da muke gana ma ta! "

Wiwin hannunsa ya zuk'a tare da furzar da hayakin cikin takaici, "yanzu kawai gobe da safe ku je ku aiwatar da abin da ya dace akan ta kuma bana son kuskure saboda kusan Mai gida akai na zai huce"

Ya fad'a had'e da jan tsaki yana tunanin wacce irin hallita ceh ita da ta ke da jinin wahala a jikinta"An gama ran ka shi dade"

Wannan din ya katse sa, kallon bangaren da dan aikin nasa ya ke ya yi kafin "Je ka na sallame ka! "

Hannunsa ya dunkula yana mai nuna alaman darajawa ya ce"Godiya na ke ran ka shi dade"

Ba tare da ya sake magana bah ya fice daga cikin wajen yana sak'e-sak'e aransa ga me da kyakyawan budurwan da ke kulle a kurkukun su! Duk in da ya ratsa sai sun tsaya yin barkwanci da wa'inda ya hadu da shi kaman ba shi neh ya gama rusunewa kaman mai jiran karban hukunci dazu bah!.

✏✏Zaune ta ke akan kujera tana sauraran lectures din da yake gudana, jefi-jefi kuma ta kan kalli kofar shigowa kaman mai jiran mutum.

"Zad Boy mutumiyar mu fah in ban manta bah yau ta ke cikan kwana na biyar da ba ta shigo makaranta bah!"wani dan gaye ya fad'a wa dan uwansa da ya shagala da kallon wannan yarinyar

Bushasshen lebbansa ya lasa kafin ya ce"Ashe bani kadai na lura da hakan bah!"

Balantonin kan sa ya shafa tare da kai bakinsa wajen kunnen Zad boy, magana ya ma sa a kunne nan kuwa suka sak'i dariyan daya jawo hankalin mutanen cikin 500seaters Hall din!

Kallon su wani hadadden gaye mai wanka taward'a wanda kammanin sa da Mourad(Yay Mou din ZULFA) har ya b'aci saboda hasken fata kawai Mourad zai nuna mai yayi had'e da girgiza kan sa cikin takaicin halin wasu daga cikin daliban na sa, juyawa ya yi wajen Allo ya rubuta"Gwaji" wanda ya sa duka ajin daukan kananun surutu daga kowani kusurwa...

"DanAllah ko kun san abinda ya hana k'awata zuwa makaranta? "

Kallon-kallo suka hau yi cikin son danne dariyar su jin ta ce wai _kawarta_ kafin karami daga cikin su cikin isa ya ce"Amaya kou?"

Gyada kai budurwan tayi da sauri, kallon wanda ya kawar da kai gefe daya wanda yayi maganan ya yi tukunna ya ce"ba ta nan neh"

Harara Amaya ta gallara mai kafin ta ce"Ai da tana nan da bazan tambaye ku bah! "

Dayan gayen dake ta kawar da kansa neh ya ceh" Jad! Lokaci na kure wa fah ka fad'a ma ta tafiya ta yi! "

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now