52

308 45 3
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 52*


✍️Raba runguman tayi tare da karb'an papern a hannun sa sannan ta ture shi kad'an kafin tayi hanyan waje ba tare da ta furta koda kalma daya ba

Yana ganin zata fita yace"I love you!" Da karfi

Ta dai ji amma yanda tayi bazai sa kayi tunanin cewan maganan ya shige ta ba,

Yana ganin ta fita a zube a kasa a wajen tare da runtse idanuwan sa

Wutsil-wutsin da baby keyi yasa ya kalle ta, dariya yaga yarinyan tana masa wanda hakan yasa yaji zuciyan sa na karaya sosai

Wajen babyn ya karasa tare da daukan sa yana rungume ta ajikin sa...

Lokacin da ta fita daga gidan direct sabon gidan su Amaya tayi, gabadaya ma ta manta da papern da ya bata saboda saboda acikin jaka ta jefa shi, ba tare da ta damu da taga saki har nawa ya mata ba

Mamakin ganin ta Amaya tayi inda ta kuma karb'e ta cikin mutuntawa,

Kasancewan akwai bak'in zuwa biki agidan shiyasa bata samu had'uwa da maman Amaya a lokacin ba

A d'akin ta ta sauke ta inda take tambayan ta inda ta shiga har na tsawon lokaci mai yawa

Kwantawa tayi akan gado inda cousins din Amaya da kuma kawayen ta suka bita da Ido

Murmushi Amayan tayi saboda daman bata yi tunanin Jin amsa daga gare ta ba

"Na kawo miki abinci ne?? Kokuma wanka zaki fara yi tukunna??" Ta sake tambaya a hankali tana kallon ta

Juyawa mata baya tayi tana jan gutun tsaki mai nuna cewan an dame ta

Tab'e baki kawayen tan sukayi suna exchanging glance da juna amma babu wacce tayi magana kuma daga gani gulma na cin su kaman miye...

Bacci take son tayi amma gabadaya hayaniyan su dakuma shewan su bai bari ba dukda cewan Amayan tana ta ce musu suyi a hankali

Zama tayi a bakin gadon tana rik'e kanta da hannu cikin son calming kanta down

"Scissors!" Ta fad'a a hankali dalilin ciwon kan da yake neman hargitsa mata tunani, mik'ewa Amayan tayi da dasauri cikin fad'uwar gaba

Dankwalin kanta ta cire ta ajiye akan gadon tare da cire baby ribbon din da aka kama mata dashi

Nan fa gashin nan ya barbazu, sai ji kake suna ta wow-wow kaman jiniyan yensanda

Lumshe idanuwa tayi tana jiran Amayan, cikin sanyin jiki ta tafi dauk'o scissors din

Tana kawowa kuwa ta koma gaban mirror tana jan tsaki saboda haka kawai take Jin haushi

Ba tare da tayi wani tunani ba ta kama Yanke gashin kanta kaman ba nata

Zaro idanuwa kowa yayi cikin mamakin ta, gashi ba halin yin magana saboda basu ga fuskan ba

Tana gama yankewa ta juya ta kalle su tana mai cire gashi daga jikin scissors din

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now