41

321 45 2
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 41*

✏️Mutuwar tsaye Farid yayi a wajen daga baya kuma yaji kafan sa ya gagara d'aukan sa nan yayi zaman d'abas a kasa

Wani hawaye ne yaji ya zuba daga cikin idanuwan sa saboda har ga Allah da aure yake son BabynMourad

Yaso ace itace zata zamo matar sa amma she broke his heart

Hannu yasa ya rik'e saitin zuciyar sa, yakai awa daya awajen kafin yasamu yayi composing kansa ya shiga cikin asibitin

A Zaune ya sameta da alaman shi take jira ya dawo,

"Tin dazu?" Ta tambaya tana kallon idanuwan sa, dan shuru tayi sannan tace

"Kana lfy kuwa??"

Key din motan sa ya d'auka yace"maman ki zata zo ta kwana dake!"

Kafin ta kai ga yin magana har ya fice daga d'akin wanda hakan ya jefa zuciyan ta cikin zulumi saboda abinda bai tab'a faruwa ba kenan tin da suke

In har an bata gado shike kula da komai dinta har a sallame ta shiyasa ma take d'ad'a kaunan sa

Cikin rashin jin dadi ta kwanta abinta tana mai sharar kwalla

'''Washe gari...'''

Ahankali take bud'e weak eyes dinta wanda suka yi wani irin jaaa saboda rashin hawaye

Sosai ya bata wahala sai kace ba Mourad din da tasani ba, tashi daya yazamo wani daban

Murmushi yasakar mata lokacin da yaga ta bud'e idanuwan ta

Tunawa da abinda ya faru a tsakanin su jiya yasa ta runtse idanuwa tana mai b'uya a fadadden kirjin sa

Dariya mara sauti ya sake yana cewa"kunya kike ji ne??"

Gyada kai kurun tayi tana mai yin lamo ajikin sa

"Ai babu kunya tsakanin mata da miji! Ko bakiji Ammi ta fad'a ba!?"ya tambaye ta

Shuru tayi bata basa amsa ba,ba tare da ya damu ba yace

"Lokaci na kurewa! bari na had'a miki ruwa kiyi wanka!"

Dan matsawa tayi ya samu ya tashi yayi bayan gida, lumshe idanuwan ta tayi

"Miye sa kika biye masa??" Taji an tambaye sa

A hankali ta bud'e idanuwan ta tana mai kallon ceiling din d'akin

"Mijina ne!" Ta fad'a a takaice

"Ohhh haka zaki ce??"... fitowan sa ya hana ta magana

D'aukan ta yayi in a bridal style ya shiga da ita bayan gidan

Dakansa ya gasa ta sosai inda sai kuka mara hawaye mai basa dariya take yi

Saboda tinda yake bai tab'a ganin wacce take kuka tsakani da Allah amma hawaye yak'i fitowa ba

Bayan ya gama mata wakan ya barta tayi wakan tsarki sannan ta dauro alwala tazo tayi sallahn asuba

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now