Soldier-woman

337 46 6
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 20*

*#'''Soldier-woman'''*
✏️Wasu hawaye masu zafi ne ya silalo wa Amayan da idanuwan ta already sun yi suntum tsantsan kuka

Maman sa kamma sumewa tayi, baban kuwa hannu yasa a fuska kuma ko  tantama babu hawaye ne suke neman fallasa shi

Kanin sa ma mutumin mutumi ya dawo dama kuma tin zuwan su ko magana baiyi banda bin mutane da idon da yake yi kaman wani wanda baisan abinda ke faruwa ba

Mik'ewa Shugaba tayi tare da komawa gefe, da baban yaga kukan ba na karewa bane yasa yace

"Allah ya jikan ka Arsh!"

Ameen suka amsa cikin kuka.

Sanda akayi kwana bakwai kafin su Shugaba suka dawo bayan an cika su da arziki mai yawa...

★★★★★★★★★★

✏️✏️Bayan sun isa gida kowa yayi hanyan sa, d'akin da Arsh yake kwana ta fara shiga tana mai k'are wa wajen kallon kasancewa yau ce rana ta farkon da ta fara sa kafar ta acikin sa

Fess d'akin yake banda yen kuran da suka hau kan abubuwan d'akin dalilin rashin shigan sa da aka kwan biyu ba'ayi ba

Wata teburin dake d'auke da System dakuma wani akwati ta nufa

Ba tare da ta damu da kuran dake kan kujeran ba haka ta hau ta zauna

Akwatin ta bud'e nan taga sabuwar pistol dinsa harda silencer agefe(shine yake hana bindiga kara idan anyi harbi)

D'auka tayi tana tina ranan da suka taho daga Italy, inda Arsh ya d'age akan in babu silencer bazai tab'a rik'e bindigan ba

Yar murmushin gefen baki tayi tare da cewa"Allah sarki, kenan sun dawo nawa kenan?"

Ta fad'a tana ajiyewa a kan tabur, system ta bud'e tare da kunna wa sannan tasa password, cikin kankanin lokaci missed calls dakuma messages suka dinga shigowa rututu kaman dama jira suke yi

Bata kai ga bud'ewa ba ma, sai ga wani kiran, kaman wacce bata san yanda ake picking ba ta dawo, sanda yakusa katsewa ta d'auka

Ya bud'e baki kenan zai fara zuba ruwan mita kaman yanda yasa ba yi yaga ba marainin wayon sa bane

Cikin sauri ya ajiye kopin dake hannun sa yana kuma mik'ewa kaman wanda yaga Shugaban kasa a bazata

Sanin cewan bazata yi magana ba yasa shi yasa mata

"Big Boss!(Shugaba)Bari na fad'a masa!" Ya fad'a cikin ladabi sannan ya bar wajen, ko minti daya ba'ayi ba suka had'a system din ajikin projector nan hoton ta ya bayyana a jikin garun dake d'auke da white silk

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now