👑SHUGABA👸 9

327 49 4
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 9*


✏️Tsit ka ke ji ajin ya dau shiru kaman makabarta, mik'e wa su Arsh suka yi cikin kidimewa

"Shegiya,jaka,mayya,mai kama da Aljanu,kin tona asiri na a cikin jama'a kin ji dadi kou ba haka ba? Dama mama na tace bata yarda da ke ba ashe gaskiyan ta ne, a fuska kaman mutumiyar arziki, mai fuska biyu kawai...Sai kuma ta fashe da kuka... Allah ya isa tsakani na dake, bazan yafe miki tona min asiri da kika yi a cikin bainar jama'a ba! Muguwa munafika...
Ban ma san yaya na fara kawance da irin ki ba!
Na tsani ki!"Amaya ta fad'a tana huci

A hankali ta d'ago da fuskar ta wanda hakan yasa ta ja da baya da  sauri tana kuma kare fuskar ta da tafin hannun ta saboda wani hasken da ta ga ya fito daga idanuwan Shugaba

Cikin sauri su Arsh suka sauko gudun kar Sarauniya Ara ta sa ta aikata aikin dana sani a cikin mutane

Runtse idanuwan ta tayi da karfi kafin ta sake bud'e wa wanda a lokacin ne ya koma daidai

"DanAllah!"Arsh ya fad'a da sauri lokacin da ya karaso wajen ta

Mike wa tsaye Shugaba tayi kaman wacce kwai ya fashe mata a ciki

"Baki tsane ni ba!"ta fad'a cikin b'acin rai wanda hakan bai nunu a muryar ta ba

Wata iriyan harara mai cike da tsana Amaya ta hauna mata"Wallahi na tsane ki!"

"Tukunna dai!"Shugaba ta sake fad'a

Ganin Amaya zata sake magana ne yasa Arsh dakatar da ita cikin b'acin rai

"Baki ganewa ne??... A hankali ya matsa kusa da ita sosai ta yanda ita kadai ce zata ji abinda zai fad'a...kin san Wacece ita kuwa?? Kin deb'o ruwan dafa kan ki yarinya"

Wani irin tsoro ne ya ziyarci zuciyar Amaya amma dak'e tace" ban bukatan sanin Wacece ita saboda hakan bazai kare ni da komai ba!
Amma Allah zai saka mun lokacina da na b'ata a kan ku harda maloho irin ka mai bin mata a gindi"

"Saduwan Alkhairi!" Shugaba ta fad'a tare da yin gaba saboda in ta cigaba da jin abinda Amaya ke fad'i tou ba makawa sai ta nakasa ta a wajen

Mara mata baya suka yi inda ajin ya d'au kananun surutai game da abinda ya faru yanzun

M² kam ma sandarewa yayi a wajen cikin rashin sanin abin yi game da wasan kwaikwayon da ya kare yanzu

Zufan goshin sa ya share sannan ya fara koyar dasu darasin yau,

Bai ma musu wani koyarwan da yawa ba ya fice saboda jikin sa babu wani sauran kwari , har wani ciwon kai yake ji

★★★★★★★★★★

✏️✏️Banda kai da komowa babu abinda take yi, ga wasu zufan dake karyo mata dukda cewan ba wai tasa wani kayan kirki bane saboda sanye take cikin half vest da kuma dan guntun wando mara nauyi

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now