👑SHUGABA👸

546 50 2
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*_Page 3_*


✏️Juyawa suka yi gabadayan su, mikewa maman su tana cewa" pumpkin dina ya dawo"

Runguman sa tayi tare da sumbatar kumatun sa , rike ta yayi yana cewa"nayi kewar ki Mine!"

Girgiza kai yaran suka yi suna sakin dariya ganin yanda suke yi sai kace ba d'azu ya fita daga gidan ba

"Sannu da dawowa" suka fad'a cikin had'in baki

"Yauwa, ina fatan dai kuna lafiya"

"Lafiya kalau!"

Miyar da hankalin sa ya yi wajen babynMourad dake ta had'a rai ya ce"waye tab'a mun babynah! Na ga yau ko sannu da dawowa ba'a zo amun ba"

Cikin shagwaba take cewa"ba matar ka bane da masoyin ta!"

Zaro idanuwa ya yi yana miyar da kallon sa wajen maman su da ta sha mur

"Miye ku ka ma ta?" Ya tambaye M²

Girgiza kai yayi cikin takaici kafin ya ce"Ba zaka yarda in nace maka yarinyan nan kallon dan daudu take mun ba!"

"To kai ba dan daudun bane?"

Zaro idanuwa suka yi inda babynMourad ta rufe b'arin fuskar ta da hannu daya tare da fitowa da harshen ta irin tana mai gwalon nan

"Wayyo Masoyiya ta an gama ci mun mutunci yau dinnan!" Ya fad'a cikin rawar murya da alamun maganan ba karamin bugan sa ya yi ba

Cikin rashin jin dadi maman su ta ce"Ya za'a yi ka ce haka pumpkin? Gashi zaka sa mun Masoyi kuka! Zo abin ka Masoyi na ai mu duwawu ne in ba'a neme mun don Zama ba za'a neme mu don kashi!"

"Ai abin bai kai haka ba Mine,kin san bamu tab'a ganin sa yana waya da mace ba kin ga dole mu zarge sa ! Amma sorry I love you!"

Turo baki Maman su tayi tana cewa"sauran wannan rubebbiyan ta ce ya yi hakuri itama ai ko ba komai masoyi na ya girme ta!kuma kaima sanin ka ne Masoyi na ba wani babba bane ko ka manta a wani shekara ka fara soyayya ne na tuna maka?"

Kaman za ta yi kuka ta ce"Yay Mou dina yanzu fa na gama bada hakuri"

Shafa kan ta ya yi ya ce"Ki kara ba su hakuri in ba haka ba musha wahala dukkan mu a wajen Mine ke ma kin san halin ta! Kin ga tin ba'a je ko ina ba ta fara bada tarihi"

"Sorry I love you!"ta fad'a cikin turo baki

Harara Maman su ta cilla mata tana cewa"kar ma ki bada hakurin mana!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now