44

241 34 1
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 44*

Cikin tashin hankali suka nufeta ganin yanda take yi a kasa, ga idanuwan ta sun juye kaman mai cutar farfadiya

Wani irin ciwon kaine ya kai wa Babynzuly farmaki lokaci daya

"Zulynahhh?"ta kira ZulynMourad cikin dishwasher murya

Rik'e ta ZulynMourad tayi da sauri tana tambayan ta miye ke damun ta

"Tan da iska ne?? shine baku fad'a mun ba!"ta fad'a da kyar yayin da zufa ke karyo mata

Fuskarta ta rik'e tana kallon cikin idanuwan ta, girgiza kai tayi tana cewa"wallahi bansan tana da su ba! Muje d'aki"

"Kafata ya rik'e"ta fad'a tana kuka,zaro idanuwa tayi tana cewa

"Not now! Kiyi hakuri muje d'aki tukunna!"

Kallon su M² yayi yace"bari na kira babanmu!"

Ko inda yake ZulynMourad bata kalla ba saboda wani irin b'acin rai dake cin ta

A hankali ta zaunar da Babynzuly a kasa tana tofa mata Addua saboda hakan ce take faruwa a duk sanda iska suka tashi a gefen ta shiyasa ma bata da kwashe kwashe saboda lafiyar kanta cos yanzu in sun yi wasa sai ta kai sati a zaune ba tare da kafan ya sake amfani ba saboda rik'e mata kafa iskan ta sukeyi

Gurnanin da Azizat keyi a kasa ne ya miyar da hankalin ZulynMourad kanta

Wani irin tsoro ne ya kama ZulynMourad musamman ma yanda taga kumatun ta ya kumbura, ko dayake ma bai kamata ace sunyi mamakin ganin tana da iska ba saboda in many ways zaka lura cewan ba ita kad'ai bane

Kukan da Baby tasa ne ya firgita ta wanda hakan yasa tayi kara tana maimaita kalmar Innalillahi

Wajen babyn taje ta d'auke ta daga kan keken da take da alamun wasan ya Ishe ta ne

Ba'a wani dad'e ba babban su ya shigo cikin gidan cikin tashin hankali

"Kai motar ka mota!" Mourad ya fad'a shikuma yana d'aukan Babynzuly dake kuka a hankali

Abu kaman tsafi, ko iya kamata bai iya yi ba saboda sai wani sab'ulewa take yi tana mi-mik'ewa

Har aka kai Babynzuly mota bai iya rik'e ta, ganin bai fito bane yasa baban ya koma kiran sa

"Miye faru??"..."na kasa d'aukan ta!" Ya fad'a a gajiye

Shima gwadawa yayi amma shuru kakeji daga karshe baban yace zai kai Babynzuly tukunna amma zai dawo da mai ruk'iya

Hakan kuwa akayi amma maimakon abin yayi sauk'i sai ya sake yin worst shi karan kansa malamin yasha mamaki kuma iska yak'i bayyana kansa sai wahalar da Azizat din takeyi kaman ba gobe

Cikeda tausayin ta yace ayi mata alluran bacci ko zata samu sauk'i

Amma ina ko runtse idanuwan bata yi ba, gabadaya dai babu wanda yayi bacci a cikin

BabynMourad da tazo washe gari taga abinda yake faruwa ne ta rubuta mata alluran bacci mai karfi

Da M² yaje siya ma basu basa ba saboda akwai wa'inda suke mugunta dashi saboda haka in babu takaddar asibiti basu bayarwa

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now