61

283 49 5
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*



*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 60*

Labarin kashe baban Fareed bai wani Dad'e ba ya iso su, sosai mutuwan ta tab'a su

Fareed kuka harda majina saboda yasan cewan baban sa bai shiryu ba! Yasan cewan baban sa bai tuba ba!

Sosai yake kuka harda vibrating lokacin da suka kalli inda aka kona baban nasa wanda toka kawai ake gani awajen ga polisawa sun cika wajen

Daga cikin motan nasa ya soma buga kansa da steering din mota wani irin tsoro na samun matsuguni acikin Zuciyar sa

So yake ya fita yaje ya kwaso sauran burbud'in baban nasa amma babu hali

So yake yaga fuskan wa'inda suka kashe mai uba amma gabadaya babu wanda yayi kaman yana wajen lokacin da ake hukunta shi

Gabadayan su sunyi focusing akan abubuwan siyarwa su kaman basu bane wasu kuma sunyi gaba abinsu, yen tsira-ra da suka rage awajen ma bawai suna nan lokacin da abin ya faru bane

Wasu kam sai da labari ya bazu kafin suka iso bawa idanuwan su abinci

Duk wanda yazo sai Allah ya wadai yake yi akan tokan wanda hakan yana daga cikin abinda yasake tsinke zuciyan oga Fareed

Gashi ba halin yaje wajen mutane suce *ABOKIN B'ARAWO* (Next book dina) a had'a dashi bayan bai shirya ba

Har yamma yana wajen, yana gani aka tsintsince sauran baban sa ana sawa a cikin container

Cikin sanyin jiki yaja motan sa ya bar wajen yana mai jimamin baban sa acikin Ranshi...

★★ ★ ★★

✍️✍️ Sororo suka yi suna kallon ta bakin su bud'e kaman sunci babu

Kallon baban ta tayi tace"Ummuh na ne ta turo maka letter??"

Maimakon ya bata amsa sai ya buge da cewa"kike ce miye sunan Ummun ki??"

Kafin ta bada amsa har babynMourad tace" kina nufin kice LIEUTENANT colonel na rank din sojoji?? Kokuma nickname dinta kenan??"

"Sunan ta ne! Haka nagani ajikin uniform dinta!...kallon baban ta tayi cikin mamaki tace"baka san sunan Ummuh na bane?? Baka san sunan matan ka bane??"

Kallon juna suka fara yi cikin wani yanayi mai wuyan fassara, ZulynMourad ne ta shafa kan babyn tana cewa

"Haba mai suna! Wannan wani irin tambaya ne?? Kawai dai mu bamu san ta da wannan matsayin bane shiyasa!"

👑👑SHUGABA👑👑Onde histórias criam vida. Descubra agora