👑SHUGABA👸

630 56 3
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*_Page 2_*


_Barkanmu da Sallah,Allah ya karb'i ibadunmu Ameen_


✏Cikin tsananin tashin hankali yafara takowa wajen ta ,ko ina na jikin sa rawa suke yi, tsugunawa ya yi yana kallon raunin bayanta wanda zallan shatin bulalu ne shar a wajen, ko kyan gani bayan ta babu gashi kuma daman farar fata ce!

"Wannan sanyi-sanyin fa!? "Ya tsinkayo muryan ta tana tambayan sa, mikewa ya yi da sauri ya je ya d'auko ruwa da tawul harda maganguna irin su abonikin da zai shafa a bayan

A hankali ya tsuguna sannan ya fara gogewa a hankali kaman wanda ke rike da kwai, a hakan ma yana yi yana runtse idanuwan sa kaman a jikin sa ciwon ya ke, tana jin sanda ya gama ta mike abinta tare da wucewa bayan gida, karar kofa ne ya dawo dashi duniyar mutane, cikin sanyin jiki ya mike tare da ficewa da bahon ruwan hannun sa yana mai kallon ruwan ciki da ya koma jazir har Wani bak'i-bak'i ka ke gani...

★★★★★★★★★★

✏✏ Banda kalman Innalillahi babu abinda ka kejin yana tashi daga cikin kurkukun sanadiyar hango sa da suka yi akan gadon karfe muttace gashi kuma ya yi wani irin fari na ban mamaki ga kuma kan Labbansa da kake hango d'anin maciji Wanda hakan ya jefa zuciyar su cikin zulumi

"Macijiya ce ta sumbace shi!"Wani fad'a daidai karasowar ogan su

"Ban gane macijiya ba? Tukunna ma Ina ita yarinyan ta ke? "Ya tambaya cike da b'acin rai da firgici cikin katon muryansa, sunkuyar da kai suka yi gabansu na dukun uku-uku

"Ba da ku nake magana bane ba wai!? "Ya sake tambaya a fusace

Wani miyau mai d'aci mai gadin ta ya had'iye kafin yace"ta bukaci a kawo ma ta ruwa ne kafin na dawo nazo na tarar da shi! "

"Kana nufin tin jiya wannan abin ya faru? "

"Erh yallabai! "Ya amsa cikin sanyin murya yana mai sunkuyar da kansa kaman yanda sauran suka yi

"Tou a tattare shi daga nan kuma na baku kwana uku ku nemo min yarinyan! "

Arazane dukkansu suka d'ago suna kallon sa cikeda tsoro jin yace su nemo macijiya, shikam ba tare da damuwan komai ba ya fice abinsa....

★★★★★★★★★★

✏ ✏✏ "Haba danAllah k'awata yanzu saboda baki damu dani ba yasa ki ka b'ace har tsawon wannan lokacin baki dawo ba!" Amaya ta fad'a kaman zata yi kuka, kallon Amaya tayi sannan ta rik'o hannun ta alaman tayi shuru saboda yarinyan tana son ta! Ko ba komai ka damu da wanda ya damu da kai!

"Au ba zaki mun magana bane? Ko dai baki yin magana ne? "Amaya ta tambaya cikin kulawa, girgiza kanta tayi alaman tana magana

👑👑SHUGABA👑👑Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon