23

318 47 5
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 23*


Ganin yanda katuwar macijin keyi ne yasa Mourad yin jarumtan fad'in

"Bismillah! Ya kai maciji! Nan asibiti ne! Inda marasa lafiya suke, idan wasu suka ganka zasu mugun tsorata! Kaga iyalaina ma ka tsoratar su! DanAllah ka tafi!"

Ai ko nan macijin ya juyar da kansa tare da nufan wajen window, sukuma suka sauk'e ajiyar zuciya, suna kara kallon wajen windown suka ga wayam babu komai

Ba tare da damuwan komai ba ko wannen su ya nemi zama

★★★★★

"Ya za'ayi kuce baku ga gawan ta ba??kunsan miye hakan yake nufi kuwa?? Hakan na nufin wani ya taimaka mata kuma tana da 50% chance din rayuwa tinda an same ta! Don haka ku bincika asibitocin da ke garin nan! We mustn't lose her!"Shine abinda Mr Dakhil ya fad'a cikin b'acin rai

Apple dake hannun sa ya datsa wanda hakan yayi making sound

Kallon dan nasa yayi tare da kawar da ido yana cewa"lafiya da sassafen nan!"

"Dad! Ya batun yarinyan nan ne wai! Wallahi ina son ta ne dagaske!"wannan gayen na wajen airport ya fad'a cikin seriousness

"Haba Fareed! Duk wannan tashin hankalin da muke ciki baisa ka sarara mun ba?? Ka dai san yarana bazasu iya binciko ta haka kawai ba! Ka bari in sun gama aikin su zasu nema maka ita! Kuma za'a sameta I promise you!"

Lumshe idanuwan sa yayi yana taunan Apple cikin kwarewa da nutsuwa wanda hakan zai nuna maka cewa yasha ruwan yen gayu ya koshi, chan ya bud'e idon tare da mik'ewa ya nufi katuwar dinning room dinsu wanda yake d'auke da yar karamar dinning table mai zaman mutane 4 wanda hakan zai nuna maka cewan Mutane 4 dake zama acikin gidan

Kopi ya ajiye tare da fara zuba ruwa acikin, sub'ucewa goran yayi wanda hakan yasa ruwan splitting a dayan hannun sa dake rufe cikin hands glove

"Sshit!"ya fad'a cikin rashin jin dadi,a hankali ya cire hands glove din wanda hakan ya bayyana ya mutsatsiyar hannun sa wanda yake d'auke da kunan man gyada 

Murmushi yayi tare cewa"ka gaji kou?? Bari na bar ka kasha iska kafin mu fita!"

"Ina kuma zaka je??"babansa ya tambaya daga inda yake

Kallon baban sa yayi kafin yace"Ohh! Nima fa wai zan taya su duba ta ne cikin style dina saboda bana son lokaci yayi ta kurewa! Na matsu na ganta"

Mik'ewa baban yayi yace"madallah!"

★★★★★★

Jugum suka yi dukkansu sai sauke ajiyar zuciya suke yi akai akai saboda tsoro

Mourad ne yayi ta maza ya cire ZulynMourad daga jikin sa yana cewa"bai kamata mu tsaya haka har sai ta tashi ba! Nasan baza'a rasa wani abu game da ita ba!"

"Bayan wanda muka gani yanzu??"BabynMourad ta fad'a cikin rawar murya

"Erh zamu sake ganin wani abu daban nasani!"Mourad ya fad'a

Karasa zazzaga jakan yyyi nan bindigan ta dakuma silencer sai kuma waya ta fad'o

"Hmmmm! bindiga?"suka fad'a cikin had'in baki

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now