39

305 44 3
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 39*

_Not edited_
✏️Atsorace BabynMourad taja ta tsaya tana mai kokarin reverse saboda yanayin yanda AzeeeChoco tayi magana ya bata tsoro ba kad'an ba

Smirking tayi ta sake cewa"kina so kenan??... I will make it easy"

Wani irin ihu BabynMourad tasa tare da rugawa a guje, juyawa tayi abinta ta shiga cikin d'aki kaman ba ita ta firgitar da yar mutane ba

Cikin mamaki suke kallon ta musamman ma yanda har ta fara kuka

"Miye ne?" Maman ta tambaye ta cikin tashin hankali

Runguman maman ta tayi tana cewa"tsoro nake ji mamanmu!"

Rik'e Ammi Smallie tayi da kyau cikin tsoro, inda babynzuly kuma ta matsa wajensu tana cewa

"Tsoron miye kuma??"

Shigowan su M² ne ya hanata magana, ganin Mijin ta agefen d'an uwanta yasa ta rugawa a guje zuwa wajen sa tana sak'in wani sabon kuka

"Ke bamu son shirita fa!"ZulynMourad ta fad'a cikin jin haushi ganin taki fad'a musu

Kanta ya shafa yana musu alama da ido akan miye same ta

"Muma bamu sani ba!"Smallie ta fad'a a sanyaye cikin larabci saboda Ahzab baijin hausa

"Calm down! Miye ne!?" Ya tambaye ta

"Mubar gidan nan! Bazan iya kwana acikin gidan nan ba!"ta fad'a tana Jan hannun sa

"Ki bari tou muyi dinner saimu tafi!"ya fad'a cikin jin dadi saboda sosai yake son su keb'ance amma babu dama.

Ganin yayan ta yayi hanyan d'akin ne yasa ta a kwala mai kira

Juyowa yayi yana cewa"ai wannan sai kisa mutum ya d'auka wani mugun abu ne a bayan sa"

Aranta tana cewa ai abin da zaka tarar ne mugun abu

"Ina zaka je??"ta tambaya kama. Bata san d'aki zai shiga ba

Baki bud'e yake kallon ta, daga baya kuma ya soma juye-juye, ganin ba kowa a bayansa yasa shi nuna kansa yace"dani kike yi??"

"Isn't that obvious??"Smallie ta fad'a ganin wani tambayan rainin hankali

"Ohhh... Yaushe kika dawo so considerate akan mutum haka??"

Kawar da kai tayi tace"in d'aki zaka karka shiga! Kawai ka kirata daga bakin kofa!"

"Tou Sannu uwata!"ya fad'a tare da shigewa abinsa wanda hakan yasa su dariya...

Da Sallama d'auke a bakin sa ya shiga cikin d'akin

Baiji ko ta amsa ba amma yasan ta amsa  shi din ne kawai baiji ba

"Mijin ki ya dawo!"ya fad'a a hankali,dan juyowa tayi ta kalle sa

Chan ta mik'e daga kwancen da take tare da wucewa da bayan gida

Murmushi ya sake yana shafa gashin kansa sannan ya cire kayan sa saboda yasan had'a mai ruwan wanka taje yi

👑👑SHUGABA👑👑Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang