66

469 66 10
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 65*


'''#Sorry... Not edited!'''
Sun isa Abuja lafiya inda daman a airport sukayi parking din motocin su

Acikin motan Qudsiyah aka saka ta inda babyn ta ke mak'ale ajikin ta saboda kin bari su Ateefa su d'auke ta tayi

Su Kuma suna motan da M² ke tukawa saboda babynMourad cewa tayi ita babu abinda zata tuka , nan ba don yaso ba ya karb'i tuk'in, a hakan ma yana yi yana mita wai yakamata yayi ta cika ladanta itakuma tace in shi ne mai bada ladan ya hana ta

Su dai suna baya sunyi shuru suna Jin yanda suke ta exchanging magana kaman wasu  kananan yara wanda hakan yasa sukayi looking cute

Hannu Faty tasa a saitin zuciyar ta sannan ta Adda Hanifa tana cewa"zuciya ta na bugawa da karfi!"

"Nima haka!"Asiya ta fad'a a hankali

Juyowa babynMourad tayi tana cewa"ayyerh emmata aikin wannan mayen ne kuyi hakuri"

Shuru sukayi suna kallon juna su cikin mamaki wai taji su,"it's ok! Ba ku ne na farko ba!"ta sake fad'a tana kefta musu ido

Ware idanuwa Faty tayi da Jin abinda tace, shidai baice komai ba Banda murmushin da yake ta  dokawa kaman wanda akayi mai albishiri da gidan Aljanna

Bluetooth dinsa yayi connecting da wayan"babyn babanmu please kimun dialing numbern masoyiya!"ya fad'a saboda wayan yana hannun ta ne

"Kaiii ka cika takuri Wallahi!"

"Kema kinsan da ba don masoyiya ta hana ni tuk'i da waya a hannun ba da bazan ce kiyi ba!"

"Babu abinda Zan Danna ka bari mu isa gida tukunna, ai naga mun kusa!"

Kwace wayan yayi ya cilla baya yana cewa"sorry sisters wata ta dan yi long press akan 1"

"Ok"kawai Ateefa tace tare da yin abinda ya sata

Ko ringing biyu baiyi ba ta d'auka

"Masoyiya mun kusa isowa!"shine abinda ya fad'a

Basu ji miye tace ba sukaji yace"shikenan masoyiya!ki jira mu acikin compound, ke nake son nafara gani in mun shigo!"

Abin mamaki ya basu cos d'azu da suka iso Maiduguri akan idanuwan su ya kira masoyiyan kuma da zasuyi boarding din jirgi ma ya kira ta, da suka sauk'a ma ya kira ta yanxu ma ya sake kiran ta!

Gaskiya they're so curious to see waye wannan masoyiyan cos da fari ma sun d'auka ko dayan matan sa dake gida ne, har Faty take cewa Allah ya kara musu hak'uri saboda da ita ne kam ma kishin cewan uwar gida aka je daukowa baxai bari ta bar wayan ta a kunne ba balle ya dame ta da kira

Sai daga baya da suka tambayi Shugaba take ce musu ai maman sa ne! Abin ba karamin ba basu shiyasa suke Allah Allah su isa

Wallpapern sa yayi mugun burgeta inda hoton Zane baby ne wanda yayi mugun yin kyau

Kasancewan yarinyan nada katon Ido shiyasa hoto yaso yayi iri da na cartoon cos na mussaman ya kara mata girman ido abun so cute cos sai ka lura sosai zaka san cewan baby ce awajen

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now