My name is Azizat

340 51 6
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 26*


#My name is Azizat
✏️Gyada kai yayi a hankali cikin sanyin jiki,"tou yanzu ya zamuyi??"

BabynMourad ta fad'a, kallo securities din sukayi exchange kafin wani yace

"Yanzu dai mu bamusan yanda za'ayi mu nemo wacce bata da suna ba!"

Cikin hasala BabynMourad tace"Yaaa! Bamu ce bata da suna ba! Taya za'ayi kuce bata da suna?? Kai bakasan wanda bai da suna doesn't exist bane?? Don haka yi withdrawing din maganan da ka fad'a yanzun nan"

"Allah ya baki hakuri!"securities din suka fad'a gudun kar asamu matsala da customers yanzun nan cos sun lura yarinyan akwai zafi

Gabadaya duk sunyi jugum babu mai magana acikin su, jefi-jefi kuma baby na share hawaye saboda gabadaya ta d'aura laifin b'acewar ta akanta ne

Tasan ita ya kamata ta rik'e ta gam yanda bazata kubuce mata ba amma ta kasa kasancewan bata saba rik'e hannun mutum acikin supermarket ba sai dai a rik'e nata

"Wayyo!"ta fad'a cikin kuka kaman wacce akace uwarta ta mutu

Tsugunawa M² yayi daidai wajen ta tare da fara share mata hawayen fuskar ta

Ahankali cikin jarumta yace"Yi shiru zamu same ta InshaAllah!"

"Yaya!"ta fad'a tana runguman sa, gabadaya sun had'a scene awajen cos wasu sun tsatsaya wasu kuma sun wuce wasu kuma na taya su jaje

Cikin tashin hankali suka karaso wajen su, suna ganin iyayen su suka ji wani hawaye ya taso musu lokaci daya

Rungume baban ta tayi tana cewa"bamu iya Kare ta ba! Bamusan lokacin da ta bar wajen mu ba"

Shafa kan M² ZulynMourad tayi tana mai magana da ido at the same time kuma tana share hawayen fuskarsa

"Yallabai Muje control room!"wani ya fad'a cikin girmamawa

Nan suka dunguma zuwa control room din gabadayan su

Ba b'ata lokaci aka fara duba ta,

Chan wajen da ake siyarda kitchen wares suka hangota azaune

"Gatan chan!"babynMourad ta fad'a in a relieved tune

Ajiyar zuciya suka sake gabadayan su, kafin suka musu godiya tare da ficewa

Azaune take sai bud'e wukake takeyi tana kallo cike da Sha'awar su,

"Ke!"M² ya kira ta cikin b'acin rai,

Cikin zaro ido take kallon sa , chan kuma ta saki dariya tareda yin wajen sa tana cewa

"Kaga wukake dayawa! Masu kyau sosai, inason dukkan su...ta fad'a cikin nishad'i

Da sauri BabynMourad ta rungume ta tana fad'in"señoritan Yaya miye sa kika tafi baki fad'a mana ba??"

Jan hannun ta ZulynMourad tayi tana cewa"ai ke ba haka akeyi ba! In mutum zai tafi wani waje tambaya akeyi kinji??!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now