Illusion

350 53 3
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*Shugaba_*
*_SAN(Uwa ta gari)_...(na kud'i ne)*

*Page 34*


#illusion
✏️Cikin sauri ta danna wa numbern kira
"Wifey!"taji an fad'a daga dayan bangaren

"What do you mean?? Miye wannan ka turo!"..."ki bawa mai wayan wayar ta!"

A hankali ta mik'a mata wayan, karawa tayi a kunne tace"miye hakan ka turo min??yaushe muka yi wannan maganan dakai ban sani ba??"

"Calm down! Tou miye abin tashin hankali aciki?? Kunya kike ji??"

"Can you hear what you are saying?? Miye sa kamun haka bada yarda na ba??" Ta tambaya cikin rawar murya

"Calm down okay?...cikin fad'a ta katse shi da cewa..."stop telling me to calm down and bring your ass here!"

Cillar da wayan hannun ta tayi hawaye na gangaro mata,

"Yaaa! Tou miye abin kuka anan DanAllah!" Smallie ta fad'a tana murguda mata baki

Wata harara ta watsa wa Smallie din tare da cewa"nifa ban kira ki ba! Ki fita karna sauk'e dukkanin haushin da nake ji a kanki!"

Tsaki Smallie din taja tana cewa"ace mutum sai shegen bak'in rai! Allah ya sauwaka wallahi!"

"Ameen tinda Addua ce kika mun, Allah ya tura k'eya!"Ko magana Smallie bata kara ba ta fice daga d'akin

Achan wajen su ZulynMourad ta hango AzeeeChoco tana chan chocolate, ba b'ata lokaci ta nufi wajen su tana cewa

"Wai mu kad'ai ne bamu san da d'aurin auren Babynbabanmu ne ba yau??"

Kallon ta ZulynMourad  tayi tace"nima sai jiya nasan da labarin!"

"Ohh! Atleast sai ki bamu head up tukunna ai!"ta fad'a tana turo baki

Hannu ZulynMourad ta had'a waje daya tare da yin fuskar tausayi tace"Tou ya mai girma grandma amun afuwa!"

Dariya suka sa gabadayan su, kallon Smallie din tayi tace"yaa... Ina yar uwar taki??"

"Tana d'aki tana kuka!"ta fad'a cikin sanyin murya

"Mene?"ta tambaya cikin zaro idanuwa had'e da mik'ewa da sauri

Gyada kai Smallie din tayi cikin yin fuskar tausayi,
"let me go and see daddy's daughter!"ta fad'a tare da wucewa

Akan gado ta same ta, a hankali ta karasa wajen ta tare da zama agefen ta tana cewa

"Ko dai kin daina son Ahzab ne"

Dasauri ta kalli maman ta tare da fashewa da kuka
"Oops ya akayi ban lura kin daina son sa ba?and I call myself your mother!... runtse idanuwan ta tayi tace... How sad! Am sorry babynPumpkin bansani bane!"

ZulynMourad ta fad'a cikin rashin jin dadi

D'agowa tayi da sauri tare da soma girgiza kan ta sannan ta rik'e hannun maman ta

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now