👑SHUGABA👸 8

402 53 3
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 8*

'''Bayan watannin 3'''

✏️Zaune take a kan gado, tana ganin ta zaka san bata duniyar mutane,

Cikin rashin Jin dadin yanda yarta ta dawo a cikin watannin 3 kacal matan ta karasa shigowa yar madaidaiciyar d'akin su

Tagumin da Amayi tayi maman ta ta cire nan Dan zabura saboda tsoro

Cikin tsananin tausayawa maman Amaya ta ce"Haba Amaya ya kike son nayi ne? Abin da ya faru ya riga da ya faru DanAllah kiyi hakuri ki bar komai a hannun Allah kar wannan tunanin da kike yi ya zamo wani abu na daban!"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da share gutun hawayen da suka silalo mata

"Mama har yau abin ya kasa barin kwakwalwa ta"ta fad'a cikin gajiyawa

"Ai daman dole ya kasa bari saboda babu wacce maza uku zasu mawa fyade a lokaci daya kuma ta mance,amma danAllah ki mik'a lamarin ki zuwa ga Allah InshaAllah zaki samu saukin abin da ke damun ki" maman ta sake fad'a cikin son kwantar mata da hankali

Gyada kai tayi tare da cewa"InshaAllah zan yi kokarin na daina sa abin a raina!"

"Yauwa yar albarka! Allah zai saka miki kinji? Yanzu ya batun komawa makaranta?"Maman ta tambaya

"Mama anya zan iya komawa kuwa?? Kin ga a makarantan mu wa'inan din suke !"ta fad'a a hankali

Rik'o hannun ta maman ta tayi ta ce"Kar ki samu damuwa InshaAllah babu abin da zai sake samun ki kuma kinsan duk abin da ya sami mutum a duniyar nan to duk yana cikin daga cikin kaddaran sa , ki karbi kaddaran ki hannu bi-biyu ki kuma gode wa Allah da kalan naki kaddaran"

★★★★★★★★★★

✏️✏️Da sallama d'auke a bakin sa ya shigo cikin d'akin, amsawa nenne tayi tare da karb'an bahon hannun sa, shi kuma ya juya

Cikin kwarewa nenne ke goge mata jikin ta da kuwa da kuma tsumma

Tana gamawa ta sanya mata wata doguwar riga mai laushi wanda iska zai samu shigan ta

A lokacin ne ta Lura da motsawa da bakin ta yayi,murmushi kawai nenne tayi tana cewa

"Sai yanzu kika ga daman dawowa da ita *Ara*?"

"Kin san jiki da jini!"wata Murya mai mawa Shugaba magana ta amsa

"Tabbas haka ne!" Nenne ta fad'a had'e da mik'e wa tana cewa

👑👑SHUGABA👑👑Место, где живут истории. Откройте их для себя