59

307 47 6
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 58*


Dube-dube ya soma yaga wayam, babu su babu alaman su, juyawa yayi yaga nan ma babu su

Wasu irin zufa ne suka fara karyo mai, kaman wani zararre haka yasoma kiran sunan ta acikin harabar makaranta

Securities da suka gansa ne suka matso suna tambayan sa ko lafiya

Nan ya musu bayanin cewan yar sa ne ya hango yanzu kuma kafin ya rufe motan sa har ta b'ace

Galala suka saki baki suna kallon sa ganin yanda ya wani damu kaman ance mai mutuwa yarinyan tayi

Aiko basu sake Shan mamaki ba sai sanda suka ga ya d'auki waya yana magana

"Masoyiya! Masoyiya!! bangan ta ba! Ta b'ace... Naga Azeee tazo! Kafin na juya har sun b'ace!miye zanyi masoyiya?"

Daya daga cikin securities dinne ya tafi ya kira wo headteacher din makarantan

Direct security room aka wuce don duba CCTV footage, amma abun mamaki gabadaya CCTV din bai yi capturing din su ba, abun sai ya dawo kaman Almara saboda kaman wani ne yagoge clip din daidai lokacin b'acewan su

M² kam kiris ya rage ya fashe da kuka, idanuwan sa sunyi mugun ja, tashin hankalin da sun bayyana b'aro-b'aro akan fuskar sa sai uban zufa yake yi kaman wanda yayi workout mai shegen wahala

Wayan sa da yayi ringing ne yasa ya fara juye-juye wai yana nema not knowing cewan wayan na rik'e a hannun sa

Daya daga cikin securities din ne daya ga wayan sai ringing yake yi gashi mai wayan ya rikice yasa shi nuna hannun M² yana cewa

"Wayan ka na ringing!" Wanda hakan yayi daidai da yankewan kiran

Kiran ne yasake shigowa wanda akayi sa"a ya d'auka

"Kana ta ina Masoyi?" Yaji mamansa ta tambaya, wani irin shuru yayi kaman wanda ruwa ya cinye

Banda nishin sa babu abinda take ji wanda hakan yasa hankalin ta mugun tashi

"Mai sunan Baban sa!??"ta kira sa da dan karfi

"Haryanzu bamu ganta ba!"ya fad'a kaman an fixgo maganan daga bakin sa bayan ya dawo daga guntun shurun da yayi

"Kana ina??"ta sake tambayan sa

"Ina zuwa!" Ya fad'a maganan na yankewa daga bakin sa

Waje ya fita yana balla buttons din gaban shirt dinsa saboda ji yake kaman Zaiyi hauka saboda irin zafin da yake damunsa

Da sauri ta tare sa cikin tashin hankali saboda tana Jin cewan yarinyan ta b'ace tayi saurin kiran Mourad sannan tasa driver ya fito da ita

Polisawa aka sanar wa cikin gaggawa nan suka bazama wajen neman ta

Gabadaya familyn su da abokan arziki babu wanda baisan cewan Baby ta b'ata ba

M² da su ZulynMourad an kasa zaune an kasa tashe,sai zuwa akeyi ana dawowa kaman jigida...

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now