the End

482 60 6
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 66*


Mik'ewa tayi tana zuge zip din gaban Abayan ta da sauri gudun kar babyn ta gani

"Ba'a koya miki sallama bane??"shine abinda ta fad'a kaman wacce bata da gaskiya

"Ban san Zan samu kofan a bud'e bane!"ta fad'a a hankali tana nufan katon gadon su

Kallon M² dake chan edge din gadon Shugaba tayi wanda shima ita yake kallo yana mata ido akan kar ta bari baby ta kwana dasu

B'aki ta tab'e itama tana hawa kan gadon irin aikin gama ya gama dinnan, jawo babyn tayi zuwa jikin ta tana cewa

"Na baki story sai muyi bacci??"

Jikin Ummun nata ta shige tare da wrapping hannun ta a kasan hammatan ta tana cewa"Eh Ummuh na!"

Cuddling dinta itama tayi sosai, ajiyar zuciya suka sauk'e gabadayan su wani irin kauna yana ratsa dukkansu

A hankali take bata labari har sai sanda taji yarinyan ta sassauta rikon da tayi mata

Zame jikin ta take kokarin yi taji babyn tace"Ummuh na!?"

Waro Ido tayi tare da cewa"hmmm babynah!"

"Karki kwana da bak'in kaya a jikin ki! Mummyn Taheerah tace mana babu kyau saboda bak'akken aljanu!"

"Ohhh tou! Yi baccin ki Bari naje na cire!"

"Ummuh na ki dawo in kin gama cirewa! Bana son ki kara bari na!"ta fad'a cikin magagin bacci

"InshaAllah babu inda zanje! Gobe a gefen ki zaki same ni"

"Ina son ki Ummunah!"

"Nima ina ki son babynah!"ta fad'a tana pecking din goshin yarinyan cike da tausayin ta

Ahankali ta sauk'a daga kan gadon tare kallon M² da baccin wuya ya kwashe shi bayan yagama wasa da bedside lamp

Ba tayi magana ba ta shige cikin toilet, fitsari tayi tukunna tare da cire pant dinta gabadaya saboda b'acin da yayi

Kayan jikinta ta cire tare da daura towel din da ta gani sannan ta wake pant dinta

Tana fitowa ta gansa a bakin kofa ya hard'e hannayen sa a kirjin sa

"Baka yi bacci bane dama??"ta fad'a a hankali in a whisper

"Kina tunanin Zan iya bacci acikin wannan Daren ne??"ya fad'a yana jawo ta jikin sa

Runguman sa tayi tana cewa"Tou da miye zai hana??"

"Tambaya kike ko neman sani??"

"Tambaya nake yi Saboda ina son na sani!"

Jan hannun ta yayi zuwa cikin toilet din yana cewa"bari na baki amsan ki!".....

Washe gari kuwa da safe ta farka ta samu Ummun ta chan gefen Abuu dinta yayi wrapping hannun ta a kugun ta sai ya zamana Ummun ta ne a tsakiyar su bayan dama ita din ce a tsakiya

Murmushi tayi cikin jin dad'in cewan Ummun ta na nan babu inda taje

Da rarrafe ta sauk'a daga kan gadon tare da yin hanyan waje, bud'e kofa tayi a hankali ta fita gudun kar ta tashe su

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now