Unexpected marriage

335 46 2
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*Shugaba_*
*_SAN(Uwa ta gari)_...(na kud'i ne)*

*Page 33*

'''#Unexpected marriage'''
✏️Marin da maman Shazy ta kwad'a wa Shazia yahan ta karasa maganan bakin ta

Rik'e kumatun tayi cikin kidima tana kallon uwar tata da take huci cikin tsananin b'acin rai

Cikin dauriya tace"Tou karya nake yi ne?? Ni Wallahi ki fad'a mun waye ubana!"

Aiko maman Shazy bata san yaushe ta jawo Shazian jikin ta, nan fa ta fara k'irban ta cikin bakincikin

Ihun da Fareed yake ji yasa shi saukowa, nan idanuwan sa ya sauka akan Maman Shazy dake jibgan Shazia kaman ta samu jaka

Cikin sassarfa ya karasa wajen su, dakyar yasamu ya janye Shazia daga wajen maman ta

"Ka barni na kashe yar banza!"..."ki kashe ta kuma??"ya tambaya cikin tsananin mamaki saboda abinda bai tab'a ganin ya faru ba yau sai gashi yana gani

Sake janyo Shazia tayi daga jikin Fareed tana kokarin kara mata wani dukan

Nan ya sake janta jikin sa yana ture maman Shazy,"Fareed babu ruwanka! Wannan tsakanin uwa da y'a ne don haka ka fita daga ciki"ta fad'a cikin huci

"Fine!ki kashe ta in kinga dama"ya fad'a yana hankad'a Shazia dake kwakume shi wajen maman ta

"Wayyo yaya kamun rai! Kashe ni zata yi! Wayyo babana! Wayyo!!!" Sune abinda take fad'a cikin kuka da tashin hankali saboda ba karya ta jibgu kam

Ko fim Fareed bai sake cewa ba sai ma zaman da yayi akan kujera yana kallon su kaman TV

Ganin cewan Shazia ta daina kuka da ihun neman taimako yasa gaban sa fad'uwa saboda sai yanxu ma ya tina cewa bata da lafiya mik'ewa yayi da sauri cikin fargaba yana cewa

"Ta daina kuka fa!"...tsayawa Maman Shazy tayi tana kokarin dawowa da nutsuwar ta

"Ta mutu!"Fareed ya sake fad'a lokacin da ya sa hannu a hancin Shazia don jin ko tana numfashi

Atsorace maman Shazy tace"Mene?"..."bata numfashi!kin kashe ta!"ya bata amsa

Kuka maman Shazy tasa cikin tsinkewar zuciya da rashin sanin abinyi

Da sauri ya d'auke ta yayi waje da ita yana cewa d'auko key!

"Yes key!?" Ta fad'a a rud'e tare da soma dube dube

Ganin fa ba fitowa Maman Shazy zata yi ba yasa shi yin hanyan waje da ita a hannu

Sanda yayi tafiya mai tsayi da ita a hannu kafin ya samu taxi saboda a estate suke....

Lokacin da ta farfado yen gidan su ta fara gani , ganin yanda maman ta ke kallon ta ne yasa ta lumshe idanuwan ta tana cewa

"In baki fita ba zan kira babanmu na fad'a mai yanda kika kusan kashe ni!"

Cikin sanyin jiki maman Shazy ta fice daga ward din aranta tana hamdalan cewan bata kashe yarta...kaii harta ga uban ta yana peppersoup da ita, murmushin gefen baki Fareed ya sake kafin yace"duk kin gama tsurar damu wallahi!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now