50

317 43 5
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 50*


Cirewa nayi ya rage daga ni sai gutun doguwar riga mara hannu, ganin hakan bai mun ba yasa na fita daga restaurant din gabadaya

Wayan sa ya dauk'a ya mara mun baya dasauri, ina fita waje naji wani irin iska yana ratsa ni wanda hakan yasa na fara sauk'e ajiyar zuciya masu karfi

"Miye kike yi haka?? Miye sa kike son fidda tsiraicin ki ne?? Kefe Muslima ce ko kin manta ne??"

Ba tare da na kalle shi ba nace "Ina ruwan ka??"

"What?? Ina ruwana?? Maybe kin manta! Bari na Tina miki! Nidin nan ogan ki ne! Kuma duk abinda na fad'a miki sai kin bi! Moreover ni ba sa'an ki bane!" Ya fad'a cikin b'acin rai

Wata irin kallon da yasa hanjin cikin sa kad'awa na sakar mishi cikin takaicin sa

Bud'e motan sa nayi na dauk'i jakar bayana sannan na ajiye mai magangunan da ya siya mun a wajen

Kaman mai fad'a da motan haka nayi banging din kofan nayi gaba abuna ina barin sa da sak'in baki galala kaman soko

Kwafa yayi cikin b'acin rai ya shiga motan sa , abincin da basu ci ba kenan kowa yayi hanyar sa

Ta ma riga sa komawa barrack wanda hakan ya bashi mamaki sosai Saboda babu pass a tare da ita! Amma ta ya suka bari har ta wuce?? Abinda bai sani ba shine babu lungu da sakon barrack din da bai san da wanzuwar ta ba!

Sunfi sati 2 basu sake had'uwa ba Saboda bata bari ko hanya sure had'a

Jinjina mun yake yanda na iya avoiding din mutum har haka,abinda bai sani ba shine nasan yasa wani yaron sa ya dinga reporting duk abinda nake yi duk wayewar gari har zuwa dare

Iya monitoring dina yayi har masters yayi a wannan fagen Saboda zai iya cewa halayena dad'aya ne bai da masaniya akan su...

"In babu busa ai akwai zagi kou??" Ya fad'a yana Zama a gefena

Banyi magana ba sai ma abincin da nake ci a hankali kaman bana so,

Ba tare da damuwa ba ya jawo.tray din abincin sa shima ya fara ci

Karan chokalin sa naji ya fara damuna wanda hakan na daga cikin abinda yasa bana cin abinci a lokacin da sauran sojojin ke ci

Chokalin hannuna na buga akan karamin farantin silvern da abinci na yake

Adan razane ya kalle ni, mik'e wa nayi daga wajen da farantina, sannan na miyar inda ake ajiye wa

Shima mik'e wa yayi yana tambaya na ko miye sa na ajiye farantin

Sanda na bari na kaisa inda babu kowa kafin tokare shi da kafata da duk karfin da Allah ya bani batare da nasan harda na Ara ba

Kasa yayi cikin zafin ciwo yana runtse idanuwan sa tare da girgiza kansa, nan da nan Idanuwan sa sukayi jazir saboda nasan kiris ya rage hawaye su zubo mai

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now