43

325 49 9
                                    


'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 43*

Cikin tsananin tashin hankali yake jijigata amma tuni ta gama ficewa a hayyacin ta

Sureta yayi da sauri yayi hanyan waje da wani irin mugun gudu

A bayan mota ya ajiye ta yaje ya shiga yaja su suka bar haraban gidan

Duk Acn dake cikin motan akan bai hana zufa zuba daga jikin dukkansu ba

Allah ne yayi zasu isa asibitin lafiya dalilin irin gudun da yake shararawa don ma ya ci sa'a dare ne da yen sanda sun kama shi, yanzun ma don sun ga akwai patient a bayan motan shiyasa basu tsare shi ba

Yana isa asibiti aka karb'e ta inda likitan ta dinga fad'a kaman an ari baki sanadiyar fita da itan da yayi

Yen gidan su ya kira ya sanar da su halin da ake ciki....

Har safiya bata haihu ba gashi tayi loosing jini mai yawan gaske

Daga karshe dai aka yanke shawaran yi mata C's amma abin mamaki suna shiga theater room din ta sambad'o mana katuwar baby girl!

Stitches aka mata kafin suka fito da ita duk ta koma wani iri, har wani fari-fari ta dawo

Ta gama shan wahala, hannu daya jini ake karawa while dayan kuma ana kara ruwa saboda yanda tayi uban laushi saboda a yanzu haka in aka ce zata tashi tou sun yi babban karya cos babu ko karfi ajikin ta

Ga dayan kafanta da ya kumbura wanda hakan ya basu mamaki cos duk iya dubawan su basu ga komai a kafan

Yarinyan da ta haifa basu bari an d'auke ta ba tukunna saboda wai tana fama da jaundice shiyasa suka tafi da ita baby care

Dama kuma basu bi ta kanta ba saboda gabadaya hankalin su ya koma wajen mai jegon ne

Wuni tayi tana bacci sai ajiyar zuciya take sauk'e wa akai akai saboda ita karan kanta tasan abu ya fita daga jikin ta, dukda ba wai wani nauyi chanchan takeji ba amma she felt lighter!

Ahankali take bud'e idanuwan ta,dishi dishi tafara gani, tass ta ware idon ya mutsa fuskar ta

"Kin tashi!?"ZulynMourad ta fad'a cikin zumud'i

Nan gabadayan su suka karaso wajen ta ana tambayan miye take so

Girgiza musu kai tayi at the same time tana ya mutsa fuska saboda zafin da kasan ta yake yi

Ruwa aka kai mata bayan gida, Ammi da kanta tayi mata wanka amma da taimakon BabynMourad

Wani irin iska take ji yana shigan ta dalilin wankan da ta samu

Kumburerren kafan ta take kallo tana cewa"ai gashi kafan ta kumbura"

"Miye same ki a kafan??"suka tambaya cikin had'in baki saboda bai musu bayanin takamamen yanda abin ya faru ba

Ido suka had'a da M² taga yana had'a hannun sa alaman rok'o irin karta fad'a dinnan

Baki ta turo kafin tace"ai maciji ne ya sare ni!"

Arazane cikin had'in baki suka ce"mene??"

"Dagaske ne??"maman sa ta tambaya cikin neman k'arin bayani

Sanda ya shafa gashin kansa kamin yace"haka tace! Amma ni ban ga komai ba!"

Shuru sukayi suna tunanin ko hallucinations dinta ne suka dawo

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now