34

350 46 8
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*Shugaba_*
*_SAN(Uwa ta gari)_...(na kud'i ne)*

'''Dafatan munyi Sallah?? Allah ya maimaita mana... nakuma ga message dinku nagode sosai Allah ya bar kauna'''

*Page 32*

✏️Zaro idanuwa Jahida tayi cikin tashin hankalin ganin Shazia ta chakka wa kawarta kwalba

Matsowan da Jahida ta fara yi cikin tashin hankali wajen ta yasa ta nuna wa Jahidan kwalba tana cewa

"In kika kuskura kika matso wallahi wannan fuskar kin nan sai na chanza mai kammani!"

Tsayawa Jahida tayi tare da rik'e fuskar ta da hannuwan ta biyu cikin tsoro

Rigar Kamilah ta chukume tana cewa"na tsane inji wata y'a mace ta ce tana kaunar yaya na! Wai yama kuka had'u har kuka fara soyayya??"

"Shazia!... Fareed ya kira ta lokacin da ya shigo da karfi ganin zata yi musu kisa acikin gida

Yana karasowa wajen ta ya bata mari mai zafi wanda yasa ta sakin kwalban akan beautiful leg din ta,itakuma Kamilah ta zube akan kujera cikin azaban zafin ciwo

Rik'e kumatun ta tayi tare da kafe sa da idanuwan ta cikin mamakin sa

"Baki da hankali ne??in ta mutu fa!?"Fareed ya tambaya cikin sanyin murya ganin yanda take kallon sa kaman taga sabon hallita

Lumshe idanuwan ta da tayi yayi daidai da silalowar hawaye da cikin Idanuwa ta

Hanci taja tace"soyayyar ku awaje bata yi ba har sai kace ta shigo cikin gida saboda hankali na ya tashi??ban tab'a tunanin zaka iya hurting dina da sanin ka ba! Am highly disappointed!" Ta karasa cikin kasalalliyar murya sannan ta juya ta fara kokarin tafiya at the same time kuma ta rik'e kirjin ta

Ai ko karasa fita daga palorn bata yi ba ta zube a kasa warwas!

Cikin tashin hankali yayi wajen ta yana kiran sunan ta

"Innalillahi wa inna illahir Rajiun! Ya furta da karfi lokacin da jini yafara fitowa daga cikin bakin ta

Ihun su da maman Shazia taji yasa ta shigo cikin palorn da sauri

"Shazia! Look! Look at me!"ya fad'a yana buga kumatun ta amma ina tuni tayi Nisan kiwo a duniyar suman da take

Ba tare da ya kula da hargagin da maman Shazia keyi ya cicib'eta tare da yin waje da ita

Ganin Kamilah dake kukan takaicin ciwo dakuma yanda Fareed ya kyale ta ita da take zubar da jini da yawa ya d'auki kanwarsa ya k'ona mata rai sosai

Taya ta sukayi itama suka yi asibiti da ita...

Kansa a d'aure ajikin gadon da Shazia take yake tunani, gabadaya ya rasa miyesa ma ya kasa tafiya ya barta da maman ta!

Wani irin tausayin ta ne yake tsargar mai!wannan wani irin so kanwar sa ke masa? Son aure?? Ba son yenuwanta ba! Shifa yayan ta ne kuma uban su daya da ita! Mik'ewa yayi da sauri tare da ficewa daga ward din wanda hakan yayi daidai da bud'ewar idanuwan ta

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now