36

357 41 7
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*Shugaba_*

*Page 38*


✏️Afirgice ya farka yana salati cikin tsananin tsoro

Sanda ya duduba wajen yaga wayam babu komai, kallon ta yayi yaga yanda take zare ido ai sai abun yasake bashi tsoro

Kafadun ta ya rik'e gam tare da saita idanuwan sa acikin nata yace

"Miye kika gani??"

Da hannu take nuna mai daidai saitin da cup yake tana cewa"yazo da kan sa! Kuma ruwa ya zuba aciki!"

"Miye??...ya tambaya cikin neman karin bayani

"Cup da Jug!"

Sake kallon wajen yayi yaga cup din akan fridge yanda ya ajiye jiya

Cupping face dinta yayi tare da cewa"Relaxe! Cup din fa haka na barshi jiya, kalli ki gani!"...kallon fridge din tayi taga ya koma kaman na d'azu

Arude take cewa"wallahi yazo ! Na ganshi da idanuwa na!"

"You're just having an illusion and that's all!"ya fad'a cikin son kwantar mata da hankali

Girgiza kai tayi cikin rashin yarda da abinda yace saboda ita kad'ai taga abinda tagani!

"Oya calm down! Bari na d'auko miki kaya a d'akin ku! Make sure baki fita daga nan ba okay?"

Ahankali ta gyada kanta tana mai resting ajikin gadon tare da runtse idanuwan ta gam gudun kar ta sake gano wani abun...

Ahankali ya bud'e d'akin  yana s'auke ajiyar zuciyan ganin yemmatan sun koma bacci

Kaman wani mara gaskiya yaje ya bud'e closet din su yana neman kayan da AzeeeChoco zata sa,

Cikin sauri-sauri ya d'auki kayan tare nufan kofa fita kaman yanda ya shigo

"Ina kwana angon AzeeeChoco!?"yaji an fad'a daga bayan sa, zaro idanuwa yayi a tsorace saboda bai tsanmaci hakan ba

Dariyan mugunta BabynMourad ta sake cikin jin dadin ganin bata hana kanta komawa bacci a banza ba

Shafa gashin kansa yayi tare da juyowa yana sakar mata murmushin yak'e

Itama dariyar ta ta miyar murmushi irin na kama ka dinnan!

"Hope kun tashi lafiya!?"ta tambaya tana mik'ewa daga kan gadon

"Good morning!"ya fad'a a hankali!

Sanda tasha ruwa kafin tace"bata tashi bane kokuma har yanzu da sauran ku!"

Cikin borin kunya yace"bayan kun barta ita kad'ai a d'aki jiya bayan kun cemana tana hallucinating!"

"Ohhh ashe she's hallucinating! Then miyesa ka barta ita kad'ai yanzu!?"ta tambaya cikin rainin hankali

"Yaaa! Matata ce fa!"ya fad'a yana d'aure fuska

Dan zaro idanuwa tayi tace"Masha Allah! Allahu Akbar!Ashe matar ka ce! Ai gabadaya na manta!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now