58

385 51 10
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 57*


'''Nigeria'''

_primary 5a_
Zaune take tasa kanta akan table din kujeran ajin su tana kuka kaman wacce aka mawa dan iskan duka,

Duk yaran ajin sunyi shuru suna kallon ta kuma babu wanda ya kula ta acikin su kowa na aikin gabansa dukda cewan kuka bai barin su suyi concentrating

"Shiyasa bana son a had'a ni da yar jaririya wallahi!Amma an kama an had'a mun yarinyan da ko yaye bata wuce ba!"shine abinda wata wacce bazata wuce 10-11 ta fad'a da turanci tana kallon mai kukan

"Tou an ce miki wannan ta sha nonon ne?? Ko baki nan lokacin da tace maman ta bata zama da su bane!?"Wata ta sake fad'a cikeda neman tsokana itama cikin turanci kasancewan ba'a hausa a makarantan su gashi kuma ba dukkansu ne hausawan ba

Wata mai rubutu daga chan dungu ne ta juyo tace"Ai Mamana ce mun tayi maman ta guduwa tayi daga gida ta shiga duniya kuma har yau bata dawo ba, kuma tasan bazata tab'a dawowa ba tinda gashi ma wai kawar mamana ce zata auri baban ta!"

Dariya suka sa lokaci daya suna cewa"ke gwanda ki share hawayen ki saboda gaskiya muke fad'a baki da mama!"

Wani irin kuka ta sake fashewa dashi wanda hakan yasa suka yi tsit saboda sun tsorota ba kad'an ba

Gabadaya teachers din sun fito wajen block din cikin mamakin kukan da sukeji, itakuma homeroom teachern su ta shigo ajin da sauri

Direct wajenta ta nufa cikin turanci take cewa"Zulfa! Are you sick!?"

Kanta ta d'ago wanda duk ya gama chabewa da majina, Zufa dakuma hawaye

Teachern ne ta d'auki beautiful handki din da yake wajen gefen jakan baby ta goge mata fuska dashi

Yarinya sai ajiyar zuciya take saukewa fuskan nan yayi mugun jaa har wajen karan hancin ta ma haka

Tab'a jikin ta tayi taga babu zafi sai ma uban sanyin da yayi kaman gawa

Cikin sauri ta cire hannun ta tana kallon babyn, tsoro ne ya shige antyn nan ta d'auki wayanta ta kira guardian dinta saboda ita a tunanin yarinyan tana shirin mutuwa ne saboda yanayin jikin ta

Gani tayi ba'a d'auka ba hakan yasa ta kira dayan numbern gidan su Babyn

"Hello. This is Zulfa Mourad's teacher! Please your attention is urgently required!" Shine abinda ta da lokacin da akayi picking

Aiko hankalin ZulynMourad ba karamin tashi yayi ba da taga kiran teachern jikan ta

Waya ta d'auka ta kira babynZuly tana ce mata ta su had'u kawai a gaban makarantan su Baby saboda daman babynZuly zata zo gida ne

Agaban makarantan kuwa suka had'e saikuma ga motan M² ya iso saboda yaga kiran teachern yar sa kuma yasan abinda ba'a saba bane shine tsoro yakama shi kardai ace yarinyan ba lafiya ne shiyasa ya taho a saba'in

👑👑SHUGABA👑👑Où les histoires vivent. Découvrez maintenant