13

349 35 1
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 13*


✏️Sharrrrr kakaji ta kwara mai ruwa a fuska,

Firgit ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, hannu yasa a fuskar sa yana goge ruwan da ta kwara mai

"Cinye ni" Ta fad'a cikin b'acin rai ganin yanda ya wani kura ta da idanuwa kaman wani sabon maye

Girgiza kai yayi tare da cewa" kiyi hakuri!"

Tsaki kawai taja tana gyara zaman ta akan kujera

"Ki dinga hakuri mana!"Ara ta fad'a cikin kwantar da murya

"Yauwa nace zan iya tambayan ki??"ya fad'a a hankali kaman ba shi aka gama ci wa mutunci yanxu ba ,gyada kai kurun tayi tana mai lumshe idanuwan ta

"Idan muka gama aikin nan miye za kiyi??"

Sanda ta gama b'ata mai lokaci kafin ta saki murmushin gefen baki tare da cewa"Zan bi sarauniya!"

"Ki bini! Zan aure ki!!"ya fad'a kaman a fixgi maganan daga bakin sa

A hankali ta bud'e idanuwan ta, ta sauk'e su akan sa,tana kuma maimaita maganan a zuciyar ta

"Zan baki dukkan kulawa da mace ke bukata,zan tarairaya ki,zan mantar dake damuwowin k..."

"Ya isa!" Ta katse sa cikin tsawa

Sunkuyar da kansa yayi yana mai jin haushin yanda ya tunkare ta, ganin yanda yayi yasa taji wani iri a zuciyar ta, kawar da kanta tayi tace

"Zauna!" Cikin sauri ya d'ago kansa dalilin jin yanda tayi magana cikin wani irin muryan da bai san ta da ita ba

A hankali ya zauna a kujeran gefen sa, ita kuwa ta wani kafe sa da idanuwan ta masu firgita mutane

"Ka bani labari!" Ta fad'a cikin isa

D'agowa yayi yace"wani iri kike so?"

"Bani kawai"ta fad'a a takaice

"Na bada dariya zan baki!"ya fad'a,murmushi ta sake da jin abinda ya fad'a

"Mahaukaciya ce ni??"ta tambaya tana kallon sa

Girgiza kai yayi tare da cewa"na isa na Kira ki da mahaukaciya!??"

"Ina jin ka!"ta fad'a kawai

Haka dai ya dinga bata labarai masu ban dariya amma mutumiyar ku ko baki bata bud'e ba,inba murmushin gefen bakin da ta saba sakewa ba

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now