Baby's Coming

398 45 1
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 42*

'''#Baby'sComing💃💃'''
✏️Ambulance ne yazo ya kwashe ta inda sauran suka mara musu baya

Dukkansu ma babu wanda ya tina da kiran mazajen kowannen su tayi jugum idanuwa sunyi jaa saboda tausayin AzeeeChocon

A cewan su tana mugun shan wuya, doctorn ne ya fito yake cewa su biyo sa office

"Ina mijin ta??"ya tambaya ganin dukkansu mata

"Ohhh kad'an bamu aron waya mu kira su!"Maman su ta fad'a

"Pumpkin🤧"ta fad'a cikin shesheka lokaci da ya d'auki wayan

Banji miye akace daga dayan bangaren ba naji tace

"Muna asibiti ka taho da Masoyi!"tana gama fad'in haka ta katse wayan sannan ta mik'a mai

Cikin rashin kwanciyar hankali babynMourad tace"ka fad'a mana miye same ta, saboda gwanda mu fad'a wa mijin ta da kanmu in ba so kake ayi admitting mun yaya ba!"

"Erh ka fad'a mana zamu fad'a mai!"Smallie ma ta fad'a

"A scanning dinmu mun lura cewan tana da karaya a kafarta wanda bai gama warkewa ba!"..."eh amma yayi 2½ months yanzu"

Numfasawa yayi yace"tasake karyewa akan karayan kafanta!"

"Miye kake nufi??"mamansu ta tambaya gaban ta na mugun bugawa

"Nufi na shine dakyar ta iya taka wannan kafan da kanta!"

Zaro idanuwa sukayi atare da jin abinda doctor ya fad'a

"Kuma!"..."kuma miye??"suka tambaya cikin had'in baki

"Mun samu tana da ciki amma....

"Amma miye.??" M² da isowansu kenan ya tambaya a hargitse

"Am sorry to say ya zube!"

Luuuuu yayi a sume nan babansu yayi saurin tare shi ajikinsa

A gaggauce aka bashi gado shima, tashi daya da aka gwada Bpn sa aka ga yayi mugun hawa

Nan fa hankulan su yayi mugun tashi, BabynMourad kuka harda majina

Inda ZulynMourad kuma ta d'auki laifin gabadaya ta d'aura wa kanta saboda acewarta itace ta aiki AzeeeChoco, da bata aike ta ba da bazata fad'o ba

Mourad ne ma yake kwantar mata da hankali yana ce mata ai ba laifin ta bane duk abinda ya faru da mutum tou kaddarar sa ne haka

Ita kuma Smallie babu abinda ta iya cewa saboda she's kinda shocked da abinda ya faru

Awa uku chur ya d'auka a kwance kafin ya tashi kuma har lokacin bata farka ba

Wayan Smallie ne ya dawo da hankulan su saboda gabadaya babu mai magana kowa yayi nisa acikin tunani

"Anty!"Sahibah ta fad'a a hankali

Lumshe idanuwan ta tayi tace"Uhmm??"

"Kiyi hakuri!na yarda ke maman mu ce"..."ya wuce"ta fad'a a takaice..."miye same ki??kina ina ne yanzu??"..."ina asibiti!"..."mene?? Asibiti?? Baki da lafiya ne small mom??miye same ki??" Ta jera mata tambayan ba tare da ta ja numfashi ba

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now