👑👑AUTHOR'S NOTE 2👑👑

1.8K 83 2
                                    

👑👑SHUGABA👑👑

@MHIZZPHYDO

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

"Maganar gaskiya tin randa aka kawoki nan nafara sonki, duk dukan danake miki Allah yaga bada son raina bane, in kin yarda zaki bani kanki wlhy Zan fitar dake ayau" idanuwanta dake lumshe ta bude fesss sai akanshi, zuciyarta wani Irin suya yafara tinda ta shiga wannan wajen yanzu kwana biyar kenan amma ko uffan batace bah cikin tsananin bacin rai wanda ko kadan bazaka gane ranta a bace bane tace

"Lallai Yaron nan ka cika mara kunya ...baki bude yake kallonta cikin mamaki soboda yasan dayayi auren wuri toh lahh shakka da ya ajiye sa'ar ta ji yayi tace...

"Erh mana kai mara kunya neh wato nufin ka in aka ajiye uwarka zaka iya saduwa dait... Bata karasa bah ya wanketa da marin dayayi sanadiyar fitan kyallen daya rufe rabin fuskarta

Atsorace yayi baya sanadiyar ganin abinda bazai iya misiltawa bah, "daman abinda yasa take rufe rabin fuskarta kenan?"yafada acikin ranshi jikinshi na wani Irin rawa...

       ★★★★★★★★

"In baka sakeni bah Zan kasheta" tafada tana daukan baby daga keken wasanta

"Sai miye in kin kasheta??ai yar kice! Waye da asara?" BabynZuly tafada cikin dacin rai

Kallon fuskar yarinyar tayi gabanta yayi mugun faduwa soboda kamanta da tagani tareda baby, amma tsantsan taurin zuciya Irin nata yasa takai bakinta kusa da na baby tace

"M² Ina gargadin ka a karon karshe M² in har na kirga uku baka sake ni bah kasheta zanyi babu ruwana dani na haifeta"

        ★★★★★★★

Dariyan mugunta yayi yace"Daman kina duniya?"

Fararen idanuwanta ta kura mishi tace"baka manta dani bah daman?"

"Taya za'ayi namanta da wanda tasa nadawo dan ta'adda ?... Ya naga kin rufe rabin fuskar ki?" Ya tambaya cikeda zolaya hade da yin dariyan k'eta

Lumshe idanuwanta tayi sannan ta budesu wanda alokacin sunyi wani Irin fari na ban mamaki soboda bacin rai, yatsa daya ta nuna mishi cikin muryan bada umarni tace"kar ka yarda mu sake haduwa da kai soboda wani haduwan mu ba zaiyi kyau bah ma'ana komai zai iya faruwa kuma kar ka manta ko anan na ga dama zan iya kashe ka!!

        ★★★★★★

Hannun su na rawa suka hau budewa, cikin tsananin firgici suke kallon kujeran da take zaune inda hannun ta kawai suke gani tana shafa kan Zakin ta wanda yake ta zaro harshe...

Bayan sun gama budewa Arsh ya karba na mai Jan kaya wato Zad boy shima cikin firgici yake kallonta shi Sam arayuwarshi baitaba cin karo da mace irinta bah.

Gabadaya babu digon tausayi acikin ranta in fact batasan miye tausayi bah...

Juyawa yayi wajen su Zad boy inda banda kuka babu abinda sukeyi

Ahankali yataka zuwa gabanta, idonta a lumshe yake kaman mai bacci amma azahirin gaskiya dukda tabasu baya babu abinda bata gani

Cikin sanyin murya yace" SHUGABA danAllah a dan sausauta wa Zad boy hukuncin ya mai tsauri dayawa"

Ganin ko bude ido ba tayi bah ya sashi barin gaban ta cikin sanyin jiki

Cikin dakewar murya yace"Danish!!, Ka kawo kayan aikin nan"

Cikin tsananin firgici Zad boy yafara magana" danAllah karku cire min azzakarina ku yafe min bazan sake bah!!!"

cikin kidima Amaya dake sharban kukan nata hukuncin take kallon kujeranta sai asannan tasan nata hukuncin farilla neh akan na Zad boy nan da nan taji ta karaya taji duk fansan datake nema ya bace gabadaya taji ta yafe musu

Ganin sun nufoshi ana kokarin danne shi tace" ku dakata inace soboda sun min fyade kuka yanke mana wannan hukuncin to  Ni Amaya nayafe musu don haka kubarmu mutafi"

Mikewan dasuka ga tayi neh yasa su Arsh sunkuyar da Kansu zuciyansu duk ba dadi amma babu wanda ya isa yakara furta ko da kalma daya yanzu

Cakk numfashin su Zad boy yadauke dalilin ganin wanda basu taba zato bah....

       ★★★★★★★

"Señorita wlhy ina mugun sonki kibani dama plsss"yafada cikin sanyin muryanshi wanda bashida maraba dana babanshi

Kallonshi takeyi cikin takaicin abinda yake fada cikin muryanta mai kamada na iyayi dakuma bada umarni tace" baka da hankali wlhy!!!....

kallonta sukeyi gabadayansu cikin mamakin wace Irin mutum ce ita, Wani katon hoton dake manne ajikin garu takalla tace... Nifa *Ubanka nakeso bakai bah*...

        ★★★★★★★

Shafa fuskarta yayi dakyar yace" ke ta daban ce acikin duniyar nan soboda bantaba ganin ko jin makamanciyan ki bah,kina da abubuwan ban mamaki da dama shiyasa nake sonki,na sadaukar dakomai nawa soboda ke and kinsan miye yafimin dadi?....sanin bazata yi magana bah yasashi cigaba da fadin... Soboda Zan mutu akan cinyar wacce na dade ina dakon sonta"

Kallon shi takeyi cikin tsananin tashin hankali amma Sam bazaka ceh tana cikin tashin hankali bah , wani Irin tsoro takeji, tasan tasha kashe mutane da hannunta, tasan ta kashe mutane da dama kuma agabanta suke mutuwa sannan take sa abawa zakinta namansu ,bayan tsawon lokaci bata taba jin tsoron kar wani yamutu bah sai akanshi cikin muryanta mai dadi tace

"Bazaka mutu Arsh"lumshe idanunshi yayi cikeda jin dadi soboda ko kadan bai zata zatayi magana bah gakuma yanda takira sunanshi sai yaji kaman duk duniya nan babu wanda ya iya kira sunanshi kaman ita kasancewan abinda bata saba ba cos in zata kirashi saidai tace _kai kokuma tayi gyaran murya_lallai yau ranan sa'an shine dukda yana gab da cikawa  ,abin mamakin hawaye yaga a fuskarta daidai sanda ya bude idanunshi ai bai farga bah yaga tafashe dakuka tareda rungumoshi zuwa kirjinta

"Wlhy ko ma waye bazai ci bulus bah nayi alkawari saina kashe koma waye daya harbe mun kai"tafada cikin kukan data manta yanda akeyin shi juyar da idonta dasuka kara fari tayi dukda uban kukan datake yi  caraf idanuwanta suka sauka cikin na....

   ★★★★★★★

"Kai daya nono daya koda biyu dakuma cinyan dama nake bukata!"wani jibgegen Kato yafada cikin katon muryan shi

"Angama ranka shi dade... Amma na mace kake so kokuma namiji?" Wani dake rike da takarda da biro yatambaya cikin labadi

"In son asamu neh inason na Farar mace wanda shekarunta bazai haura 20 bah!"...

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now