38

302 53 6
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 38*

✏️Sake kallon Smallie tayi sosai irin waye dawo dinnan kafin tace"nan fa?"

Kallon juna sukayi a lokaci daya saboda gabadaya basu d'ago miye take nufi ba

Ganin basu fahimce ta ba yasa tabi wajen da kallo, ganin cewan asibiti ne yasa ta lumshe idanuwan ta kaman mai bacci

Kus-kus da suka fara yi ne yasa ta bud'e idanuwan ta tace"bana so!"

Nan wajen yasa ke d'aukan shuru, gabadaya sun gama cika da mamakin ganin irin personalities din ta

Tunani ne yakama ZulynMourad lokaci daya tare da tausayin d'anta saboda tasan ba karamin fama za'a sha ba

Shigowan doctorn ne ya fargar dasu, wajen AzeeeChoco ya nufa cikin harshen turanci yake cewa

"Masha Allah! Har farka kenan!"

Ko iskan da ta kwaso shi bata shak'a ba sai ma sake lumshe idon da tayi

Kaman tasan miye zaiyi tace"kar ka tab'a ni!"

Ahankali ya miyar da hannun sa dake niyan isa ga hannun ta don ya duba Pulse dinta

Haka kawai yaji kaman umarni ta bashi kuma yasamu kansa ta bi, saboda yanayin yanda tayi maganan

"Za'a duba ki ne fa!"M² ya fad'a cikin dar dar

Sanda tagama b'ata musu lokaci kafin dakyar tace"Mace!"

Cikin hanzari BabynMourad ta fara kokarin rik'e hannun ta tana cewa"tana nufin mace take son ta tab'a ta!"

Dan kawar da kai tayi saboda yanda muryan BabynMourad ke shiga chan cikin kwakwalwar ta

Shuru Babyn tayi aranta tana cewa"za'a sha fama kam!"

Bud'e idanuwan ta tayi ta saita wa BabynMourad din wanda hakan yasa ta matsawa baya tana rik'e bakin ta da hannu saboda a tunanin ta a sarari tayi maganan shiyasa aka bata killer look

Cikin mamaki suke binsu da kallo musamman ma yanda Babyn tawani zaro ido

Kawar da kai tayi kurun tana sauk'e ajiyar zuciya, ahankali gudun kar tayi kuskure BabynMourad ta fara yi a hankali wajen tab'a ta , kaii hatta numfashi ma rik'e wa tayi, sai wani zaro ido takeyi abin gwanin ban dariya amma ba halin yi saboda tsaro

Allura aka kawo nan tace sai mazajen dukka sun fita kafin zata bari a mata, badan babu yanda suka iya ba suka fice cike da zulumi acikin zuciyoyin su

Ana mata allura kuwa bacci yayi gaba da ita dukda cewan ba ta ci abinci ba

Fitar da ita Doctors din suka yi zuwa wajen yin test kaman yanda BabynMourad ta bukata

"Babu fa abinda yake damunta!Kuma memoryn ta bai dawo ba sai ma wani loosing memoryn da tayi sanadiyan fad'uwan da tayi!"Doctorn ya fad'a yana kallon dukkansu da suka zuba mai ido

Gyaran Murya Mourad yayi tare da mik'a mai hannu sukayi musabaha sannan ya mai godiya tare da ce musu su fito daga office din kar mai jinyan ta farka basu nan....

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now