47

258 50 6
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 47*


*#Wattpadians dina! Wannan page din naku ne! Ina yawan bin comments dinku sorry I couldn't reply them amma ina jin dadin su sosai-sosai! Thank you...Much Love😘❤️*

Kafin ta karasa fita gabadaya na rik'o skirt dinta da sauri

A hanzarce ta juyo ta kalle ni"Karki fita! Ina jin karnin jini!"

Na fad'a ina zaro idanuwa, kawar da idanuwa ta tayi daga kaina saboda tasan zan iya controlling dinta da ido kuma bazata so hakan ta kasance ba saboda yayana dake chan d'akin sa shi kad'ai

Cire hannu na tayi daga skirt dinta tace"Khatoon yayan ki yana d'aki kar wani abu ya same shi! Gwara naje na taho dashi sai mu taru a waje daya!"

"Toh muje tare!"na fad'a da sauri

Girgiza kanta tayi sannan ta shafa kaina tace"ki zauna anan ki jira ni! Karki yarda ki fito har sai nazo!"

"A'a!".."zan dawo gareki! Kawai dai ki jira ni anan ki cigaba da kiran numbern baban ku ko za'a dace!"

Bata jira na sake wani maganan ba tayi ficewar ta da sauri

Kasancewan wutan palorn a kunne ne yasa ake ganin komai a sauk'ake

Cikin sauri mamanmu ta shiga d'akin yayana

Akan kujera ta same shi awajen reading table dinsa yasa headphone akai yana game a PS akan system dinsa

Da sauri ta cire headphone din tare da mikar dashi, a tsorace yake kallon maman tasa

"Miye faru??"ya tambaya, ko amsa shi bata yi ba ta jawo sa suka fita waje don nufan inda Khatoon take

"Gasun chan!"wani ya fad'a yana nuna maman, freezing suka yi lokaci guda atsorace

Har kasa aka ja dukkansu biyun inda maman take tambayan su da turanci akan su waye ne

Ihu da nake ji ne yasa ni yaye labulen daya rufe katuwar glass dake manne ajikin d'aki na wanda zaka iya ganin komai daga wajen kaman kana kallon TV kad'an ina lek'awa

Zaune ogan su yake akan royal chair din palorn mu! Agaban sa aka zubda mamana dakuma yayana

"Wow! Ashe wanke hannu ka tab'a ne matar tasa!"Ya fad'a yana lasan labban sa kaman wani tsohon kwarto

Cikin jarumta maman mu tace"waye ne ku?? Miye kuke nema??"

"Murya mai d'adi!"ya sake fad'a cikin rainin wayo

Gyara zaman sa yayi da kyau yace"ina Flash da mijin ki yazo dashi gida?"

Cikin rashin fahimta tace"Flash?? Wani flash kuma??"

"Karki b'ata mun lokaci kaman yanda mijin ki yayi!"

"Mijina??"ta tambaya a hankali

"Eh mijin ki! Ki fad'a mun inda flash din yake kar na illata miki wannan ajebottern kin nan!"ya fad'a hankalin shi kwance yana nuna yaya na da zufa ke karyo masa daga durkushen da yake

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now