New life

337 41 3
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 25*
'

''#Newlife'''
✏️Idanuwa babynMourad ta zaro da jin furucin da yayi

"Me kace yaya??"ta tambaya still bata bar zaro idanuwa ba,

Cikin sauri ya toshe bakin sa da hannu yana mai jin takaicin kansa

Ba tareda ya juya ba ya fara reverse cikeda jin kunya, itama da idanuwa take binsa tana kunshe dariyar da yake cinta

Sanda ta tabbatar ya fita sosai kafin cikin daga murya tace"sauran na kara ganin kafan mutum acikin d'akin nan,inba sai na bashi mamaki ba!"

Ko juyowa baiyi ba banda ma kara saurin da yayi,

Ganin yanda ya wani shigo mata kitchen yasa ta lek'a bayansa azaton ta ko an biyo sa ne

Cikin rashin yardan ganin yanda yake yi kaman mara gaskiya tace"Lafiya??"

Murmushi ya kakalo tare da shafa suman kansa yana cewa"lafiya kalau masoyiya!"

"Tou Allah yasa!"ta fad'a tana mai cigaba da abinda take yi, handmade juice ya fara kokarin had'awa inda ta ce mai ai tayi

"Zan iya tasting??"ya tambaya yana d'aukan cup

Kallon sa tayi kafin tace"sure!"

Murmushi ya sake mata tare da zuba juice din a cup

Daidai ya fara shan lemon kenan kaman ance ya juyo , aiko nan idanuwan sa ya sarkafe ana BabynMourad data kafe sa da ido

Wani irin furzar da juice din yayi yana sak'in tari mai karfi kaman mai shirin shid'ewa

Cikin tashin hankali suka yi wajen sa suna mai sannu harda Shugaba itama ba'a barta a baya ba

Sanda tarin ya lafa tukun ya hau share hawayen wuyan da suka fito mai

"Sisi na kiyi hakuri karki kashe ni da idanuwan ki!"ya fad'a cikin miyar da numfashi

Zaro idanuwa ZulynMourad tayi tace"Ke zaki kashe mun shi??"

Girgiza kai ta hau yi tana matsa baya, a hankali tace"daga kawai na kalle sa?? Nifa babu abinda na mishi!"

Zaro idanuwa yayi yace"kiji tsoron Allah sisi Wallahi wannan killer kallo kika mun ba kallo kawai ba!"

Wani irin matse idanuwa tayi alaman sai na fad'a, kafin ta fara gyaran murya cike da neman tsokana

Kirjin sa ya rik'e sannan ya watsar da hannun alaman zuciyar sa ya fashe

Tab'e baki tayi tana sakar mai harara at the same time kuma tana sakin murmushin mugun ta

Hannayensa ya had'a waje guda alaman roko harda wasu fuskan tausayi wanda hakan yasa Shugaba fashewa da dariya

Dukkanin su tsayawa sukayi suna kallon ta cikin mamaki

Nuna M² tayi tare da cewa"ka cigaba mana, kayi kama da abin dariya!"

Kallon M² ZulynMourad tayi tace"miye take cewa?"

Gyaran murya M² yayi tare da washe hakwaran sa yace"just making funny face!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now