Unforgettable memories

292 47 5
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 45*

'''#Unforgettable Memories'''
✏️Dayake an riga an sanar da su baba Malam shiyasa ma suna sauk'a Ustaz dakuma D'ansa wato Humayyah mijin Smallie suka je taro su a airport

Direct kuwa sashen baba Malam aka shiga dasu, sosai yayi mamakin ganin yarinyan baya

"Ai mun tab'a had'uwa da ita!"ya fad'a yana kallon su bayan sunyi exchanging gaisuwa

Cikin mamaki Mourad ya tambaye sa inda ya santa saboda a tunanin sa har gidan su ya sani ne

"Wata ce na raka wajen ta neman gafara!"

"Neman gafara??"M² ya tambaya a tsorace

"Erh! Wai ta mare ta shine hannun ya gauce" rik'e babansa yayi da sauri cikin tsoro

"Ya haka mai sunan baban sa??"Malam ya tambaya ganin yanda M² ya tsorata lokaci guda

Cikin rawar murya yace"na mareta a bisa kuskure!"

"Ya Salam! Kar dai shiyasa ta dawo haka??"Malamin ya tambaya

Gyada kai yayi cikin mutuwar jiki da tsananin nadama

"Mun d'auka kasan ta ne sosai Malam!"Mourad ya fad'a ganin M² zai iya kofsawa da yanda yake yi dinnan

"A'a! Amma tinda matar D'an ka nasan yakamata iyayen ta su fad'a muku halayen ta

"Bata da lafiya! Bata iya tuna komai! A hanya muka tsince ta! Yanzu ya kai shekara shekara daya da rabi!"

"Allahu Akbar! Amma wani hanzari ba gudu ba! Miyesa kuka d'aura mai aure da ita?? Wannan ai wa'inda suke tare da ita suna da hatsari sosai ninan shaida ne!" Baba Malam ya fad'a

"Innalillahi wa inna illahir Rajiun! Allahumma ajirni fi musibatun!"M² ya furta a hankali

"Kwantar da hankalin ka! InshaAllah babu abinda da zai faru mara kyau!"

Kwana uku chur ta d'auka tana bacci kafin alluran ya sake ta

M² yayi wani irin ramewa kaman ba shi ba! Tana farkawa aka fara mata ruk'iya ana bata magani, dakyar da sud'in goshi Ara ta yarda ta lafa saboda cewa tayi sai M² yayi daman tana tab'a jikin ta gashi dama kuma haushin sa takeji sosai

Kullum kuwa suna part din Smallie,babynta ma bata da wani kukan rashin ganin uwarta saboda na musamman baba Malam yace kar a matso da babyn wajen ta saboda tsaro kuma hakan kuwa akayi

Babynzuly kuwa kafa daya suka fara sakewa kafin daga baya suka sake dayan...

Smallie ce ta lura da kallon kaunan da Sahibah ke jefa wa danUwanta wanda yake yin wasa da baby

Tab'a ta tayi tace"wannan kallon fa?
Girgiza kai tayi tare da mik'ewa tana cewa

"Small Mom miye za'a dafa da rana??"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now