👑SHUGABA👸 10

361 44 2
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 10*

✏️A hankali take bud'e idanuwan ta dalilin hasken da ya haska fuskar ta

Cikin mamaki take bin d'akin da kallo, ganin had'uwar sa da kuma tsaruwar sa ne yayi mugun burge ta duk da ba wasu abubuwan a zo a gani a ka zuba a d'akin ba

Sauka tayi daga kan gadon, nan ta nufi daya daga cikin kofan da ta gani

Bayi ta gani, a hankali ta shiga tare da d'auro alwala ga wani tsoron dake ziyartan zuciyar ta

Tana fitowa taga kulolin abinci ga kuma sallaya an shimfid'a mata

Cikin rashin kwarin jiki ta dau khimar din dake kan sallayan tasa

Tana idar da Sallah kamshin abinci ya cika mata hanci wanda hakan yasa cikin ta kukan yunwa

Jawo tire din tayi cikin dar-dar sannan ta bud'e kula daya daga cikin kulolin

Zaro idanuwa tayi ganin gudan kaza wanda yaji kayan had'i ,

Gefe-gefen ta ta soma dubawa cikin son tabbatar da babu mai kallon ta...



Sanda tayi nak har da gyatsa kafin ta mik'e tana tunanin inda maman ta ta shiga

"Hala tana waje!"ta fad'a tare da mik'e wa ta nufi dayan kofan


Cak ta tsaya tana bin wajen da kallo, notin kanta na tsincewa,gabadaya babu inda baya rawa a jikin ta saboda tsoron da ya ziyarce ta barin ma da taga wajen shiru ga kukan tsuntsaye sai tashi suke daga ko wani kusurwa kuma babu makawa akwai mugayen namun daji a wajen, tukunna ma ya aka yi tazo nan??

Aiko bata gama tunani ba taji gurnanin damisa, a saba'in ta koma cikin inda ta fito har da sa sakata

Tana shiga ta zame kasa a jikin kofan tare da fara kuka kasa-kasa,ganin kukan na neman fin karfin ta ne yasa ta rufe bakin ta da tafin hannun ta gudun kar damisan yaji muryar ta ,ga jikin ta sai kyarma yake yi

"Tin yanzu!?"taji an tambaye ta, cikin sauri ta ta fara waige-waige don ganin mai magana amma wayam babu kowa,

Bata gama tsinkewa ba sai sanda taji dariyan da Ara ta kece dashi nan itama ta saki kara tana mai kiran sunan Allah a zuciyar ta...

★★★★★

✏️✏️Wani irin ramewa Amaya ta fara yi saboda itama karan kanta bazata iya cewa ga yawan adadin da taje gaida hajiya ba duk da kuwa da kyar take sha

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now