👑SHUGABA👸

628 45 0
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
*_Cigaban Zulfa_*

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*_Page 4_*

✏️Sanda aka fara karb'an pepopin kafin ta dawo cikin ajin, wajen zaman ta ta nufa had'e da zaunawa

"Kafin na kirga uku kowa ya bad'a nasa" sukaji M² ya fad'a

"Wayyo Allah K'awata ban gama nawa ba,amma ga naki ki na gama!" Amaya ta fad'a cikin rashin jin dadi tare da bayar da wanda tayi ma ta

Cikin b'acin rai shugaba ta karasa mata nata wanda a lokacin har M² ya fice abun sa

Mikewa tayi tare da mara mai baya,jin kaman ana bin sa ne yasa shi kara sauri saboda baya son takuri

Shigan sa mota yayi daidai da karasowar ta ,ba tare da ya kula da wacce take gefen motan sa ya rufe murfin motan

Runtse idanuwan ta tayi da karfi tana jin zafi har cikin tsakiyar kanta

Nan da nan wasu gumi suka fara karyo mata ta ko ina musamman ma goshin ta
chan kawai ta bud'e idon ta da suka yi wani irin fari

Ajiye wayan sa yake Shirin yi a kasa idanuwan sa ya harba da takadda ga kuma jini a jiki

Bin abinda ya rike takaddan yayi da idanuwa inda zuciyar sa sai yankewa yake yi kaman wanda ake sa reza ana yankasa

Zaro idanuwan yayi cikin tsananin firgitan ganin wasu kyawawan yatsu biyu wanda suka jike da jini ke rike da takaddan

A rikice ya kalli tagan motan sa, wanda ya gani a wajen ne ya sa shi zaro idanuwa tare da bud'e motan da sauri

Boyayyen ajiyar zuciya ta sauke yayin da aka bud'e darin motan

Kasancewan hannun ta bashi da wani sauran karfi ya sa ta sakin takaddan a cikin motan tare da juyawa da sauri

Ganin zata wuce yasa shi rik'o hannun ta wanda hakan ya sa haddasa wa hannun nata ciwon da yafi na lokacin da murfin motan ya datse ma ta hannu

"Ya Illah! Ki yi hakuri danAllah bansani bane shiyasa "Ya fad'a cikin tsananin kulawa ga wani bugu dake fizgar sa

Jan hannun ta ya shiga yi yana fad'in"Muje na kai ki asibiti a duba miki!"

Ganin yana Shirin Jan ta ya sa ta fauce hannun na ta daga cikin na sa

Dunkule hannun nata mai ciwo tayi wanda hakan yasa shi runtse idanuwan sa saboda radad'in daya jiyo ma ta

Hannun ta mara ciwo ta nuna sa da shi , ko miye ta tuna oho kawai na ga ta girgiza kai tare da wucewa abin ta

Bud'e idanuwan da ya runtsa ya yi, wayam yaga babu kowa a gaban sa

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now