54

291 48 5
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 54*


✍️Allah ne yayi ya isa asibiti da wuri da sai dai muce Allah ya jikan Fareed

Lokacin da aka zo kiran enuwan sa don asanar musu da cewan yayi hatsari sai aka samu akwai security akan wayan

Ba bata lokaci suka hau mishi abinda ya dace,kasancewan ya buga kirjin sa dakuma kansa a jikin steering mota shiyasa ya shiga dogon suma

Gashi kuma dama Shazia ke yawan kiran sa a waya shiyasa kira bai shigo ba saboda itama ta kanta take yi

Gabadaya kunyan sa take ji sosai, she's not too ashame to face her a matsayin ta na shegiya, lokacin da taji cewan ita ba yar baban ta bane abin bai wani dame ta ba saboda farincikin cewan da akwai aure a tsakanin ta yayan ta da ya cika ta

Sai yanzu da tayi zaune tana reflecting akan abun tayi tunanin cewan maybe fa yace bazai auri shegiya ba!

Tunanin hakan ne ya mugun karya mata zuciya har take Jin bazata iya kiran sa ba duk da cewan hankalin ta ba'a kwance yake ba game da cewan bata ji daga gare sa ba

Sai bayan kwana biyu tayi Shahada ta kira sa, aiko daman jira nurses din suke yi a kira a wayan

Cikin sanyin murya tace"Yaya na!"

"Assalamualaikum!"taji wata siririyar murya ta fad'a daga dayan bangaren

Maimakon ta amsa sallaman sai tace"bangane ba?? Miye wayan yayana yake yi a hannun ki?? Don kun kwana tare bai nufin kinada lasisin tab'a wayan sa!"

Kallon wayan nurse din tayi cikin mamaki, watsar da maganan tayi tace"ina kiran ki daga asibiti! Yayan ki yayi hatsari shekaran jiya kuma har yanzu bai farfad'o ba gashi akwai security akan wayan sa shiyasa bamu kira ku ba!"

"Hatsari kika ce? How bad is it?? wani asibiti ne??" Ta tambaya muryan ta na rawa sosai

Fad'a mata sunan asibitin tayi tare da ward din da yake, ai kafin ta ajiye wayan sai gata ta shigo a hargitse ko takalmi babu a kafan ta

Da mamaki nurse din take kallon ta ganin yanda ta shigo kaman wata sabuwar Kamu

Idanuwan ta da suka sauk'a akan Fareed dake kwance ta zaro tare da rufe bakin ta da hannu

"Yaya na ne haka??"ta tambaya kafan ta na rawa

"Subhanallah!" Nurse din ta fad'a ganin hannun Shazia na jini da alaman drip ta tisge daga wajen

Da sauri ta dauk'o tray dake d'auke da disinfectant wipes,

Kamo hannun ta tayi tace"Hannu ki na jini! Bari nayi treating miki kafin yayi worse!"

Fixge hannun tayi tace"akwai wani abu mai suna worst ne bayan halin da yayana ke ciki!?"

Karasawa tayi jikin gadon tana Jin kwalla na ciko mata a ido, jikin sa ta bi da kallo taga sashi daya a kone!

Abin ne ya bata mamaki har bata san lokacin da tace" miye samu jikin sa haka!?"

"Ke ba matar sa bane dama??" Nurse din ta tambaya saboda a zaton ta matar sa ce,gyada kai tayi kafin ta sake girgiza kanta tace

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now