👑SHUGABA👸 6

368 49 0
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*_Page 6_*

✏️"Dawla Khatoon kuma?" M² ya tambaya cikin mamaki

Mama sa ce ta kalli constable da kyau ta ce"Kuma a ina kace ka samu wannan?"

"A cikin motan sa ne ranki shi dad'e!"ya bata amsa

Gashin kan sa ya yamutsa kafin ya ce"Ya Salam! wannan super woman din da ta taimake ni neh!"

"Ka mana bayani yanda zamu gane"baban su ya fad'a cikin shafa masa kai

Gyada kan sa yayi kafin ya fara basu labarin abinda ya faru har zuwa lokacin da ta buga mai kai ya suma

"Oh Allah! Amma Yaya ka ji kunya wallahi!"babynMourad ta fad'a cikin zolaya

"Babu wanin nan wallahi nasan da kece tsoro ne zai fara kashe ki a wajen!"

Dariya dukkan su suka sa inda dan sandan ya musu sallama tare da jaddada musu cewa inshaAllah zasu kama koma waye da yake da hannu akan abinda ya sami M²...

Zaune yake akan gado mai matasan d'akin sa ,sai kallon maman sa dake faman had'a mai kayan sa a jakar tafiyan sa take

Gyaran murya yayi ya ce"masoyiya!"

D'agowa tayi ta kalle sa tare da sakar mai murmushi tana tambayan sa yanda aka yi

Gashin kansa ya shafa kafin yace" ya aka yi mu kadai kike Haifa??"

Wani irin karrarawa ne ya buga a kan ta wanda hakan yasa ta zaman da bata shirya ba

"Allah da ba mu kadai kike Haifa ba, naso a ce muna da kanne ko kuma yayu"ya fad'a yana kallon fuskar ta

Wani yawu mai d'aci ta had'iye kafin ta kakalo murmushin yak'e ta ce

"Akwai abinda kuka rasa ne a rayuwan ku?? Na d'auka wannan soyayyan da muke nuna muku bazai bari kuyi kad'aicin rashin kanne ba! Amma yanzu ji abinda kake tambaya ta!"

"Masoyiya wannan soyayyan yayi yawa! Wallahi masoyiya na san da muna da yawa da bazai yi yawan da ace ko daushe tunanin mu na makale a cikin kan ki ba, watarana na kan Lura har manta da kan ki kike yi in kina tare da iyalen ki kuma na Lura ke mai son y'ay'a ce amma miye sa baki sake haihuwa ba!"

A hankali ta ce"Allah bai bani wani ba masoyi ya zanyi?"

Girgiza kan sa ya fara yana cewa"A'a masoyiya ban san ki da karya ba DanAllah kar ki sa na fara tunanin karya kike mun"

"Ni uwarka ce fa, ka yarda dani! Allah da so samu ne na haifi yara 20 wallahi farincikin da zan yi bazan iya misaltawa ba amma Allah mai yadda ya so, mai bawa wanda yaso ya hana ma wanda ya so! Kuma ko da ku ishirin na haifa soyayyan da zan baku bazai tab'a kasa wannan ba"ta fad'a had'e da mikewa

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now