👑SHUGABA👸 7

383 47 2
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 7*

✏️Ba ita ta samu farkawa ba sai lokacin da gari ya gama wayewa,Arsh kam ma gabadaya har ya gaji da tashin ta

Sauran gayun wajen ma sun sha mamaki irin baccin da tayi yau, saboda ka'idar ta ne tashin su da asuba'in fari amma yau har safiya tayi bata mik'e ba...

A hankali take bud'e idanuwan ta da suka yi mugun nauyi, ga wasu zufa dake karyo mata saboda wani irin zafi take ji

Jin kaman an mata lullub'i ne yasa ta tab'awa nan taga bargo ne

Sake ware idanuwan ta tayi da kyau tana bin cikin d'akin da kallo kaman yau ne ta fara kwana a cikin ta

Tsaki taja tare da zauna wa tana mai yin wulli da bargon jikin ta

"Ina kwana Shugaba!"Arsh ya gaishe ta a hankali

Maimaikon ta amsa mai ta bishi da kallon da yasa jikin sa yin sanyi saboda shima yasan laifin sa

"Bana son shishigi!"ta furta a kasan makoshin ta had'e da mik'e wa tana mai sa takalmin dake gefen gadon ta

Cikin rashin Jin dadi ya ce "Allah ya baki hakuri!

Ko iskan da ta kwaso shi bata Shaka ba tayi hanyan bayan gidan ta domin d'auro alwala

Kafin ta fito har ya fito mata da kayan da take yin sallah  saboda ba da kowani irin kayan ta take yin sallah bah gashi daman a yanxun ba wani kayan kirki bane a jikin ta shine dalilin daya sa Arsh lullub'e ta

★★★★★★★★★★

✏️✏️Zaune kowannen su suke akan kujeran cikin abinci, gaban su kuwa shak'e da abinci kala-kala

Shigowar Ammi(maman mourad) ne ya sa Zuly mik'e wa kaman yanda ta saba domin tarbo ta

"Ammi na Ina kwana!"ta fad'a daidai ta zaunar da ita akan kujera

Cikin Jin dadi Ammi ta amsa mata , nan sauran ma suka gaishe ta cikin ladabi

Komawa Zuly tayi ta zauna akan kujera

"Nifa Ku Kira su kar gyambun ciki ya kama ni anan!"ZulynMourad ta fad'a cikin turo baki kaman ba a gaban y'ayan ta da surukar ta take ba

Murmusawa dukkan su suka yi inda yaran suka fara dariya kasa-kasa

Shigowar wata kykyawar budurwa ne ya komar da hankalin su kan ta

Cikin hausar ta da baya fita sosai ta soma fadin

"Kar Ku cemin mafarki nake yi!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now