15

393 43 4
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 15*


✏️Yanzu ya za'ayi naci wannan zab'en dake karato mu?? Naga shi dinma wanda muke neman takara dashi ba'a baya ba , kuma yana da jama'u sosai?" Wani mutumi ya fad'a cikin Karaya

Dariya wanda ake fad'a wa ya bushe dashi yana cewa"ai Kaine baka d'ago abin ba tintini Abdullahi, tin yaushe nake fad'a maka akan ka shigo cikin kungiyar mu, ai nasan da yanzu baka da fargaban komai!"

"Haba miye kake fad'a haka Hamisu!? Ni fa na riga na fad'a maka baxan tab'a had'a Allah da kowa ba! Shi maji rokon bayin sa ne, baxan tab'a bari kwadayi da son abin duniya yakai ni ga halaka ba! Kuma kar ka sake fad'a min irin wannan maganan" Abdullahi ya karasa cikin fushi tare da mik'ewa yana barin wajen

Tab'e baki Hamisu yayi yana cewa"wai kai wanda yasan abinda ya dace kou?? Kaii!banma san miyesa nake son ya shigo cikinmu ba, kuma sai kazo ka neme ni da kan ka

Hamisu dai da Abdullahi abokai ne sosai, lokacin suna kanana Abdullahi ya nuna yana son harkar siyasa sosai shikuma Hamisu Allah ya yi shi da shiga abinda bai shafe sa , har Allah ya had'a sa da Mr. Dakhil

Tou a lokacin ne aka shigar dashi cikin kungiyar asiri, ba da dad'ewa ba yayi wani mahaukaciyan kud'i wanda suke tsorotar da talauci

Gabadaya yen anguwan su babu wanda bai sha mamaki ba,amma kuma ko irin tunanin cewan yana cikin kungiya bai tab'a zuwa musu ba

Abdullahi ma ya sha mamaki sosai amma shidin kasa tambaya sa yayi

Kasancewan Hamisu yana da baki yasa kungiyar ta sake hab'aka da manya manya yen siyasa da masu kwadayin abun duniya ta sanadiyar sa

Ba b'ata lokaci aka bashi babban matsayi a cikin kungiyan

Tou bayan shekaru Ashirin(20) lokacin kud'i ya zauna a hannun Abdullahi amma kuma ko rabin bai kai ba, Hamisu yace su shiga harkar siyasa tare

Nan kuwa yayi na'am dashi, daman kuma yawancin yen villan suna cikin kungiya shiyasa ma.basu wani sha wuya kafin suka samu shiga ba(daman kuma komai sai kana da hanya)

Tou a halin yanzu shirin zab'e ake yi wanda ko wannen su da takarar da yake nema

★★★★★★★★★★

✏️✏️Shiru palon ya d'auka, inda su kuma suka hau kalle-kalle

"Tambayan ki fa nake yi?" Baba Malam ya fad'a cikin kulawa

Daga gefen su suka ji tana cewa"nima fa aiki Sarauniyan mu ta sa ni!"

Cikin tsoro suka hau matsawa daga wajen, su na mai takurewa waje guda

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now