27

291 44 2
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*Page 27*


*Faeexetion, wannan page din naki ne! Ina jin dadin comments dinki😍Allah ya bar kauna❤️*

✏️Kallon su suka miyar wajen M² suna jiran yayi magana saboda azaton su memoryn ta ya dawo ne

Girgiza kai yayi yana shan ruwan gabansa a hankali, jin basuyi magana ba yasa tace

"Ko sunan bai muku dadi bane??"

Babansu ne yayi caraf yace"Kaii inji waye?? Ai sunan ki asalin dadi gare sa! Shin kuwa ya fad'a miki ma'anar sunan??"

Kai ta girgiza sannan ta kalli M² tare da rik'o hannun sa tana cewa

"Mourad fad'a mun ma'anar sunana!"

Kansa ya shafa tare da sakin wani laulausar murmushi wanda ya karawa fuskar sa kyau dakuma kwarjini

Kaman mai tsoron magana yace"sunan ki na Nufin  precious,cherished!"

Dariya tasa cikin jin dadin yanda yake fad'in ma'anar sunan nata

"Wow! Yaya ka iya zab'i Wallahi!"

"Yauwa sisi inada korafi!..."miye ne??"..."miye sa zaki barta da kayan zak'i?? Kinsan iya yawan chocolate din da taci a yanzu kuwa??"

Yatsine fuska tayi kafin tace"tou laifi na ne??ai inace ita ke d'auka da kanta ba ni ba? Tou sai na hanata haka kurum macizai su dinga fito min acikin mafarki na?taab ba ruwana ni!"

Shiru wajen na wasu dakiku kafin baban su ya mik'e yana hamdalan abincin da suka ci

Azizat ce ta fara mik'ewa tabi bayan sa da sauri wanda hakan yasa suka kalli junan su cikin mamaki kasancewan basu saba ganin irin hakan ba

Ai basu yi kasa a guiwa ba suka mara musu baya batare da sun tattara kwanukan kan dining ba

Agefen sa suka sameta ta zauna sai kokarin game take yi awayar sa

Gadayansu suka zauna suna kallon ta

"Nace ba! Kasamun nickname!"

"Nickname?"..M² yayi wuf ya chab'e maganan...kallon sa tayi tare da turo baki tana cewa"Nifa ba da kai nake yi!"ai shikenan magana ya Kare!"

M² ya fad'a inda sauran suka fara kunshe dariyar su"sisi! D'akin ku daya da ita! Duk abinda taga kinyi shi zatayi! Haba try to lay some good examples mana amma gabadaya yarinyan nan duk abun da kike yi take imitating! adai yi kokari a gyara halin inba haka ba, in kin haihu baxan dinga barin y'ayan ki suna zuwa min gida har su kwana ba saboda tsaro!"

Ganin zata yi magana yasa shi mik'ewa da sauri yana yin hanyar d'akin

"Ai wallahi ka dawo na baka amsa tinda kai ba radio bane!"

"Ai naga ba tambayan ki nayi ba kawai advice nake baki!" Ya fad'a tare da hayewa sama da  sauri

"Zaka sauk'o kasame ni ai!" Ta fad'a cikin huci, wayar ta da ya fara ruri ne yasa ta komawa ta zauna

Sanda taja tsaki da taga Mr stalker ke kiran ta kafin ta d'auki wayan kaman bazata d'auka ba shuru tayi batare da tayi magana ba......

★★★★★

✏️✏️Murmushi mai sauti yayi yana gyara zaman sa akan three seatern palorn su

"Emmata na!" Ya fad'a a hankali kaman mai jin tsoron magana cikin muryar dake sanyaya zuciyar ma'abociyar jinsa

Sanin cewan ba lallai tayi magana ba yasa yayi gyaran murya tare da cewa

"Ki shirya anjima zanzo!"..."zaka zo ina??"ta tambaya da sauri

Murmushi yayi tare da katse kiran, kwanwarsa dake aikin kallon sa cikin mamaki ne tace

"Bros! Miye nake ji haka??badai ka fara soyayya ba? Nadauk'a you're only interested in men fah!"

Lumshe idanuwan sa yayi yace"ban tab'a tunanin zan iya son wata y'a mace arayuwa ta ba! Ko uwar da ta haife ni banson ta! Amma kallo daya namata naji in ba ita sai rijiya"

"Hmm kodayake ba laifin ka bane! Kaidin ba Yaro bane yanzu! Amma ya zakayi dani??" Ta karasa maganan da tambaya cikin son danne kishin dake cinta

"Na dad'e da fad'a miki cewa maganan mu bazai tab'a yiyuwa ba! Ke fa yar babana ne! Duk iya shegena bai kai har da zan dinga kwanciya da half sista na ba! Hakuri kawai zakiyi balle ma kinsan ni bana sharing!"

Cikin sauri ta dawo wajen sa tare da mawa kanta masauki akan cinyar sa

Kaman zata yi kuka ta fara cewa"haba bros karmuyi haka dakai! Wallahi ina son ka sosai! Kuma da kake cewa bazaka yi sharing ba, tou ka sani nidin nan wa kai kawai nake tanadin kaina,ban tab'a bawa wani namiji dama ba, sai dai kawai romance! Ni ko sau daya zamuyi bandamu ba saboda nasan zaka dawo nemana da kanka!...ta fad'a tana rik'e fuskar sa sosai, a hankali yakai bakin sa daidai nata kaman zaiyi kissing dinta, sannan yasake dariya tare da d'aga ta daga kan cinyar sa suka mik'e

Rik'o rigarsa tayi tana bashi wani irin kallo mai narkar da zuciya

Jin alamun ana kokarin bud'e sliding glass yasa shi jawo ta jikin sa sosai, inda ita kuma tafara kokarin kwace kanta saboda sanin wacce take zuwa

Ba ta hankara ba kawai taji bakin sa acikin nata, zaro idanuwa tayi cikin tashin hankali

Itakuwa cak ta tsaya tana binsu da mummunan kallo cike da b'acin rai mara iyaka, ganin yana kokarin zubewa da yar ta akan kujera kuma agaban idanuwan ta yasa ta kiran sunan sa da karfi

"Fareed!"... Sanda ya tsotsi lips din ta kafin ya kai bakin sa daidai kunnen ta yana cewa"yar iskan karya kawai!"sannan ya  hankad'a ta kan kujera

Wani irin murmushi yayi tare da kefta mata ido daya sannan yayi hanyar d'akin sa don shiryawa

"Miye nake gani haka Shazia?? Ban hana ki kula wannan Yaro ba??"

Numfashi Shazia ta miyar tare sunkuyar da kanta cikin rashin jin dadi

"Yar banzan yarinya! Inma iskancin kike jin yi sai ki rasa wanda zakiyi dashi sai wannan mara kunyan??"

Mik'ewa tayi tare da turo baki tana cewa"mutum na chan an dawo dashi nan, nan dinma baza'a bari yayi abinda yake so ba!"

Ta fad'a tare wucewa da sauri gudun kar maman nata ta bata duka a baya

Zama maman tayi a kan kujera cikin rashin sanin abinyi da sauri ta mik'e tare da wucewa...

"Nace ki dinga sallama in zaki shigo min d'aki!"ya fad'a a dakile batare da ya juyo ya kalli matar baban sa ba

"Miye kake nufi da Shazia?"ta tambaya bayan ta rufe kofa

"Miye nake nufi da ita kokuma miye kuke nufi dani gabadayan ku?"

"Kaga Fareed bazai yiyu ace ka ci ka zo ka ci y'ata ba! Bazan tab'a lamuntan hakan ba!"

"Ki gyara maganan ki ! Ko kin manta fyade kika mun ne??"


*MHIZZPHYDO...*
'''16th. July.2020''

*#Vote,*
*#comment&*
*#Share*

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now