14

375 37 3
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*Page 14*

✏️Zaro idanuwa matan tayi cikin tashin hankali

"Subhanallah waye miki haka?? A ina kika ji wannan ciwon haka?? Kar dai wa'inda suka d'auke ki ne??"

Gyada kai tayi tana matse hawaye saboda zafin da take ji dalilin rik'e mata hannun da matan tayi

"Gaskiya ya kama ta akai ta asibiti ayi scanning din hannun saboda yanda nake ganin san nan toh inaga jijiyar akwai wanda ya tsince!"matan ta fad'a cikin tausayawa

Zaro idanuwa Amaya tayi cikin firgici inda maman Amaya ta hau salati harda su hawaye

"Kyanta akai ta asibiti yau dinnan saboda kar hannun ya rub'e!"

Ihu Amaya tasa tana cewa"Wayyo Allah sun cuceni Wallahi,Allah zai saka m..."

Bata idda maganan ba taji an make bakin ta

Ihu ta tsunduma tare da dafe bakin ta da hannun ta mara ciwo kaman wacce aka watsa mata acid

"Me ya faru???suka tambaya cikin tashin hankali

Cikin kuka ta ce"Mari na akayi wallahi!"

Ai kuwa nan suka fara rige-rigen barin gefen ta saboda sun tsorata barinma da suka ga bakin ta ya kumbura lokaci guda

"Wayyo karku guje ni!" Ta fad'a gwanin ban tausayi, mata mai maganin bata san sanda hawayen tausayin Amaya suka fara gangaro mata ba

Cikin jarumta matan ta ce"akwai Kawu na malami ne, inaga mu kai ta wajen sa a mata ruk'iya amma kafin nan muje asibiti tukunna daga nan kuma mu wuce saboda da zafi-zafi ake dukan karfe"

Gyada kai maman Amaya tayi tare da taimaka wa Amayan ta mik'e, ba b'ata lokaci suka wuce...

Ana yin scanning din hannun, hasashen matan ya zamo gaskiya saboda har jijiyar hannun ta an tsinka

"Miye same ta haka??"Shine tambayan da likitan ya jefa musu ganin yanayin da take ciki amma kuma sauran jikin ta lafiyan su kalau

Ganin suna kallon juna yasa shi basarwa dukda yana kwadayin jin abinda ya same ta din

"Aiki za'a mawa hannu saboda yanda nake ganin san nan, in ya kara kwana 2 a haka tou ba makawa guntulewa za'ayi!"

"Innalillahi wa inna illahir Rajiun! Allahumma Ajirni fi musibatun!!" Su dinga nanata wa cikin tsananin tashin hankali

Cikin kuka Amaya tace"wayyo an cuci rayuwata a karo na biyu! Wallahi sai Allah ya mana sakka..."

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now