PAGE 02

268 6 0
                                    

Eman...🥀

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Episode 2

  Hankali a mugun tashe umma ke jijjigani hawaye na wanke mata fuska,alokaci daya ta nemi fushin datakeyi dani ta rasa,musamman yadda nake fitar da Numfashi a wahalce ne ya k'ara d'aga mata hankali,kuka ne Sosai ya kufce mata tana fadin

"Allah ka yafe min ka fitar dani daga wannan mawuyacin halin,ya Allah i turn to you in repentance ka yaye mini damuwata ka Tashi kafad'un Eman kasa hakan ya zamto kaffara agareta.."

nurses biyu ne suka fitar da Umma bisa doctor's order,a wata cushion chair suka zaunar da ita,ta zauna shirim tana sauke ajiyar zuciyah masu nauyi,har yanzu hawaye basu daina zubo mata ba,wannan wacce irin kaddara ce me shirin tarwatsa zuciyar ta?wacce tayi silar yankewar farin ciki acikin rayuwarta?ahankali ta juya baya tana kallon hjy kwaise wacce ta dafa kafadarta,alhaji ya zagayo yana kallonta da narkekken idanunshi wanda suke d'auke da tsantsar tausayin umma,with so much empathy yake kallonta kafin ya tsugunna agabanta yana me riqo hands dinta,atake hjy kwaise ta d'auke hannunta daga shoulders din umma tareda d'age kanta sama zuciyarta na balbala da wuta,asannu ya miqar da umma suka koma doguwar cushion mai girma ya zaunar da ita sannan yace

"Hajiya Bismillah zoki zauna".batareda nuna damuwar komai ba ta zauna,ta tabbatar yanayin da umma ke ciki ne yasa alhajin aikata hakan agaban idanunta,he wouldn't dare to do that on a Normal day,shiyasa tasamu space din uzuri tabashi acikin zuciyarta.

Maganar shi ce tasa ta juyo ahankali tana kallon yadda yake lallashin umma cikeda tsantsar damuwa,duk matan alhaji babu wacce ke kawowa matsayin ta farmaki irin umma,duk masifar mummy da makircinta ko gezau bai girgiza hjy kwaise ba saima Karin matsayin data samu awurin alhaji,Mama ce taso kawo mata farmaki saide ba awani dad'e ba komai ya daidaita awurin ta,bata hana Alhaji aure ba amma babu matar data isa ta kwace matsayinta acikin zuciyar shi,she didn't let that happen for years.

"Kiyi hakuri Fatima,Allah yana tare dake,in shaa Allah Komai zai daidaita,every thing happens for a reason,there's reason for and behind everything,wannan abin daya faru abune da babu wanda ya isa ya hana faruwarsa saboda rubuce yake inside the book of your destiny,saboda haka kada ki damu,very soon Allah zai yaye miki damuwarki izuwa farin ciki mara fasaltuwa".

Sosai umma ta kara fashewa da kuka,love and support din data rasa kenan her whole life,har sai lokacin da Allah ya kawo mata Alhaji ciki rayuwarta,ya zamto kwallon tauraro ya haskake rayuwarta da mafi  hasken haske,Murya adashe tace"Eman has brought us shame,she managed to tarnish our reputation,with all my defensive strategies,ko amafarki ban tab'a tunanin hakan zai faru dani ba,I'm so disappointed,gashi tana can cikin mawuyacin hali,adduar mu kadai take bukata".

Cikeda rashin gamsuwa Alhaji yace

"Ban yarda eman zata aikata haka ba,zuciyata takasa yadda,duk da ga lamarin azahiri kowa yana kallo,amma zuciya ta takasa aminta da hakan,Eman har gobe mutuniyar kirki ce awurina".

Yakarashe maganar yana kallon hajiya kwaise wacce ke jinjina kai alamar gamsuwa da zancensa.Tace"addua kawai zamu cigaba dayi,Allah ya kawo haske cikin lamarin ".sai alokacin umma ta kalli gefen da hjy kwaise take,cikeda girmamawa tace"afuwan,bamu gaisa ba,barka da rana fatan kunzo lafiya".

Karamin murmushi Hjy kwaise tayi tace"ba komai,fatan mu Allah ya tashi kafadun Eman".

suka amsa da amin atare Alhaji Na kallon yadda Umma ta fita hayyacinta,kallo d'aya ya mata ya tabbatar akwai yunwa atare da ita,miqewa yayi batareda yace komai ba yafita,hjy kwaise da umma suka bishi da idanu,Dr Mansoor mai kula da eman ne ya karaso inda suke.

Murya asanyaye yace"eman is doing okay,Karku damu khair in shaa Allah".

shiru umma tayi wani bakin ciki Na turnuqe ta,hjy kwaise tace"Toh Alhamdulillah,Allah ya bata lafiya".ta tabbatar labarin abinda yafaru da Eman ya zagaye unguwar su harma da danginsu,cikeda damuwa ta kalli hjy kwaise tana son tambayarta amma ta kasa,ahalin da ake ciki kunyar kowa takeyi,Alhaji ne kawai take iya maganar dashi daga faruwar lamarin jiya zuwa yau,tana ganin ta gaza wurin yima Eman tarbiyya,wanda hakan ya zama babban kalubale arayuwar su gabadaya,she doesn't want to think about the future,saboda daga dukkan alamu it's not a good one.

EMAANWhere stories live. Discover now