PAGE 30

124 4 0
                                    

EMAN...PAGE 30

Ahankali yake shafa beard ɗinshi yana kallon Hajiya kwaise yana mamakin furucinta,shifa har yanxu bai fahimci inda xancen ta ya dosa ba,hasalima yakasa apprehending maganganun nata,can dai yace"nifa Mami ban fahimci me kike nufi ba"gyara xama tayi tace"miye abin rashin fahimta a maganar tawa?cewa nayi bana son kallon da kake ma Eman,ni bance ka riqa mata kallon banxa ba,cewa kawai nayi babu ruwanka da shiga lamarinta,ni fa banason ka xafafa ƙiyayya akanta"kallonta yayi yana jin xuciyarshi na ƙuna,ambatar sunan Eman kawai yana saukar mishi da ciwon kai,yace"dan Allah Mami enough about that girl"hjy kwaise tace"nide nafaɗa maka banaso"murya asanyaye yace"it's alright then".tacigaba da faɗin"sai kuma kaji Afiya tasamu miji,biki nan da wata ɗaya,narasa saurin me sukeyi"shiru yayi baice komai ba domin damuwar Fauxa ta cika mishi xuciya,can ta kara cewa"Allah ya sanya alheri da albarka shine fatan mu"miƙewa yayi yana faɗin"Amin"tayi saurin cewa "ya naga kana shirin tafiya bamu gama magana ba"yana daga tsayen yace"I'm having serious headache Mami,kuma anjima inada Meeting da state Government".tace"Subhanallahi garin yaya?"yace"too many things going through my mind"tace"kamar me fa?"yace"my businesses ofcourse,abubuwa sun min yawa,it might be possible xan rage yawan hutun nawa"tsuke fuska hjy kwaise tayi tace"kaje kasha magani ka kwanta,Allah ya sawwake "da amin ya amsa sannan ya fita daga part din.ta bishi da kallo tareda sauke ajiyar xuciya.da Umma suka haɗu a main parlour,yana kallonta yake jin tsanar Eman na mamaye mishi xuciya,da murmushi kwance asaman fuskarta tace"yaushe ka dawo?ɗaxu na aika  akace baka nan"gyara tsayuwarsa yayi sannan yace"yh i came back not too long,hope all is well?"gyaɗa mishi kai tayi tace"dama xan tambaya ne ko kana  buƙatar wani abu".sai alokacin ya sakar mata ƙaramin murmushi yace"I'm good alhamdulillah "daga nan ya shige part ɗinshi yana jin xuciyar shi na suya,she's the reason daya sa yayi taking issue din lightly with Eman,duk da har yanxu bai gama yanke shawarar abinda xaiyi ba wanda xaiyi affecting both their lives,amma aganinshi that is the best way to handle the situation.kwanciya yayi ya rufe ido kamar me bacci,har lokacin yana ganin Eman da Sadeeq atsaye suna magana,ya sauke Numfashi mai nauyi xuciyar shi babu komai banda tsanarsu wacce take ƙaruwa akowanni second din tafiyar lokaci,abun dayafi ɓata mishi rai shine cin amanar Fauxa da sukayi ko kunya basu jiba,ay ana barin Halas dan kunyah,musamman idan suka duba relationship ɗin dake tsakanin Fauxa da Eman,she's just like their sister,haka suke treating ɗinta from day one,basu taɓa nuna mata banbanci ba,ya tabbatar dalilin dayasa Fauxa ta amince da Eman awurinta kenan,saboda yasan Fauxa farin sani,ta yadda da Eman Sosai shiyasa tayi trusting ɗinta with her family and husband,ya runtse ido yana jin this is the highest level of cin amana daga wurin mutane biyun data aminta dasu,shiyasa baya San Fauxa tasan da wannan maganar,yasan xata shiga cikin tsananin damuwa da baƙin ciki mara misaltuwa,Eman and Sadeeq are trying hard to ruin her life shikuma baxai xuba musu ido ba,xai shayar dasu ruwan mamaki nan bada jimawa ba.Da sallama umma tashiga Falon Abba tana kallon fuskar shi da damuwa written all over his face,tun fitar su Alhaji Marshal yakasa ƙwaƙƙwaran motsi saboda mamaki da al'ajabi,lamarin dai saikace ana acting film,yana mamakin yadda wasu mutanen suka mayarda rayuwa very complicated,xama umma tayi gabanta na faɗuwa,ta daɗe bataga Abba cikin yanayin tashin hankali irin wannan ba,lokaci ɗaya taji jikinta yayi sanyi dubaga yadda yakirata hankali tashe,sake kallon shi tayi akaro na biyu taga gabaɗaya ma baisan da shigowarta ba,Sosai ya faɗa cikin duniyar tunani mai nisa,asanyaye tace"Abba gani "xuciyarta na wani irin bugawa da karfi,runtse ido Abba yayi yana juya kai cikeda damuwa yace"kiyi hakuri da abinda xan faɗa miki Fatima,nasan anyi miki ba daidai ba amma kiyi hakuri"tsura mishi ido kawai tayi tana kallonshi cikeda mamaki,can dai ya aro courage yace"bansan meyasa Aisha(mummy)batada hankali ba bare zurfin tunani,taya xa'ayi Aliyu yazo neman auren afiya bayan abinda yafaru?"gaban Umma ne yafaɗi ta xaro ido,bata san lokacin data miƙe tsaye ba cikeda tsananin mamaki tace"Aliyu ne yaxo neman auren Afiya?Aliyu da aka fasa aurensu da Eman ?"asanyaye Abba ya jijjiga mata kai alamar tabbatar wa,hakika Umma ta daɗe bataji maganar data girgixa taba irin wannan,komawa tayi taxauna amma takasa furta kalma ɗaya saboda mamakin lamarin,har lokacin kan Abba na ƙasa saboda kunyar Umma yakeji mara misaltuwa,wani irin cin amana ne wannan?daƙyar Umma ta iya aro jarumta tace"Allah ya sanya alheri"sai alokacin Abba ya ɗago yana kallon ta cikeda tsantsar tausayi mai narka xuciya.Yace"Ina Eman din?"umma tace"tana ɗaki"yace "kiramun ita"jiki ba ƙwari umma tashiga part ɗinta tana jin xuciyarta babu daɗi,ta rasa a ma'aunin daxata dora wannan lamarin wanda babu tsari dakuma hankali acikin shi,lokacin data shiga Eman Na kwance tana duba handouts,umma ta tsaya tana kallonta na wani lokaci tana jin tausayin Eman din,yau ce rana ta farko dataji abun ya tsaya mata rai saboda tasan dole Eman taji babu dadi,amma yaya xatayi?koma meya faru Eman ce taja dan haka dole tayi bearing consequences ɗin,ji tayi bakinta yayi nauyi sai kawai ta karasa cikin ɗakin ta xauna agefen Eman,da sauri Eman ta ɗago tana kallon Umma,lumshe ido tayi ahankali sannan Umma tace"Abba na kiranki,saide abinda nake so dake shine duk abinda ya fada miki ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddararki,kada ki tayar da hankalinki saboda duk abinda ya faru kece mai laifi,dan haka you've to bear the consequences,you should put that at the back of your mind "tana kaiwa nan ta miƙe tafita daga ɗakin,da kallo Eman ta bi Umma sannan ta miƙe jiki ba ƙwari tanajin gabanta Na tsananin faɗuwa,ahankali kamar me counting steps take tafiya har ta karasa falon Abba,ayadda Umma ta barshi anan Eman ta tarar dashi,yana xaune but lost in thoughts,da sallama tashiga ta xauna asaman carpet,kanta na ƙasa tace"Abba gani"dagowa yayi ya kalleta yana jin nauyinta na shigar shi tausayinta na ratsa mishi xuciyar,dakyar ya iya gathering courage yace"Eman"ɗagowa tayi ahankali tace"Na'am Abba"yace"kiyi hakuri da abinda zan fada miki,wanda na tabbatar bazai miki dadi ba,amma ki dauki ahakan as part of your destiny,ki sa aranki cewar Haka Allah ya tsara miki sannan ki rungumi hakan with good faith,Allah zai kawo miki wanda yafi Aliyu in shaa Allah"hawayen dake maƙale a idon Eman ne suka gangaro mata,Abba yacigaba da fadin"I tried my best wurin ganin hakan bai faru ba,Afiya ƴata ce kuma tanada haƙƙi akaina,bai kamata nayi forcing dinta tayi abinda ranta baya so ba musamman akan maganar Aure,wanda suka isa dani sun bada goyon bayan ayi abinda takeso,haka iyayen mahaifiyarta sun bada goyon bayan ayi,haka ma uwarta,kuma ita Afiya ta tabbatar min shi takeso kuma takeda muradin Aure,sannan shima Aliyun ya tabbatar da ita yakeso xai aura,takowani ɓangare nasamu rinjayi shiyasa na amince badon raina yaso ba,kuma badon xa'a ƙulla abin arxiki ba,fatana shine ki ɗauki wannan alamarin da kyakkyawar xuciya"tunda Abba yafara magana Eman ta xuba mishi ido tana kallo saikace taga wata samuwar halitta,kamar taga Alien haka take kallon Abba,gumi masu ɗumi na karyo mata takoina,ga wani side headache daya saukar mata,xuciyarta tayi baƙiƙƙirin da baƙin ciki da takaici,hawaye suka fara xubo mata kamar an buɗe famfo,bakinta ne yayi mata nauyi ta kasa cewa komai,Abba dake can gefe ya miƙe yaƙaraso daf da ita yana cewa"beautiful things awaits you Eman,matukar kikayi haƙuri sai kin dafa dutse kin sha ruwa"daga haka ya shiga bedroom dinshi feeling guilty,da ace akwai hanyar da xai bi domin afasa auren da tuni yabi,baiyi tunanin hajjo xata amince ba ga mamakinshi kuma yaji tace tunda yarinya ta dage abarta tayi abinda takeso.Eman tafi minti ashirin xaune awurin tana kuka mai karya xuciyar mai sauraro,tana jin xuciyarta na suya,meyasa Aliyu xai mata haka?why would he punish her ta wannan hanyar?ya rasa wacce zai aura sai Afiya?wacce suke gida ɗaya?wannan feeling dinne ya kusa tarwatsa mata xuciya,tana kuka ta mike jiki ba ƙwari tafita daga falon,a entrance sukaci karo da Alameen xai shiga part din Abba,ya watsa mata kallon tsana sannan yace"are you blind?"sai alokacin ta dago da jajayen idanunta tana kallon fuskarshi wacce babu alamar rahama asaman ta,ya saki wani banxan tsaki sannan yace"be careful with me"yana fadin haka ya hankade curtains din falon ya shige,tafi minti biyu tsaye awurin tana kallon wucewar shi,can ta girgixa kai sannan ta koma part dinsu,afalon Umma ta xauna tana kuka,Umma dake bedroom tana jinta saide batasan me xata ce mata ba awannan lokacin da komai ya lalace,ganin babu me lallashinta yasa ya mike ta koma bedroom dinta
tacigaba da kukan baƙin ciki da takaici dake fitowa daga ƙasan xuciyarta me ci da wuta,baƙin cikin daya saukar mata da xaxxabi ga ciwon kai mai tsanani,acikin wata 3 rayuwarta ta tarwatse beyond repair,and it's hardly  rayuwarta ta dawo back to normal after what she went through domin har yanxu da ragowar son Aliyu acikin ranta,ta jima tana kuka kafin wani wahalallan bacci ya dauketa.
Mummy ce ta shigo falon Umma afusace rai ɓace tana huci take faɗin"fito fatima yau ayita ta ƙare,nagaji da bita da ƙullin dakike min acikin gidan nan"da mamaki Umma ke kallonta,haka hjy kwaise da taxo wucewa ta saki baki tana kallon mummy,mama na gefe tana ƙunshe dariya, itace ta gama yima mummy famfo cewar idan tayi sake sai Umma ta xuga Abba an fasa auren.tacigaba da faɗin " baƙin ciki da hassada da ƙyashin ki agareni sun isheni,daga jin Afiya xata Auri Aliyu shine kika tayar da hankalinki kina xuga Abba akan kada ya amince to wallahi kinyi kaɗan,wanda ya fiki ma yayi kaɗan balle ke!"ta nuna Umma tana cigaba da cewa"ki fita harkata acikin gidan nan kafin na yaga miki rigar mutunci,babu ruwanki da lamarina,aure kuma kamar anyi angama saide baƙin ciki ya kashe ku keda ƴar ki,aikin banza kawai harara a duhu"hajiya kwaise ce tayi saurin shiga tsakiyarsu tana mamakin wannan lamari,sai alokacin tasan da maganar me kamada almara,ta rasa me xatace saboda mamaki,mummy Na kumfar baki tace""Nide nafaɗa miki da babbar murya ki fita harkata data ƴaƴana acikin gidan nan,else duk abinda ya faru have yourself to blame"wani takaici ne ya tokare ma Umma wuya,tace"are you threatening me?"tayi tambayar tana ƙarasawa daf dasu even though hajiya kwaise ta shiga tsakiya,mummy tace"duk yadda kika dauka haka dinne,nide nafada miki"murmushin takaici umma tayi sannan tace"na dade banga mara kunyah irinki ba Aisha,wacce ta kwashe kayanta daga gaban manxo,macuciya kuma maci amana wacce babu komai axuciyarki sai hassada,baƙin ciki da ƙyashi,bari na tabbatar miki da magana guda ɗaya,har yau har gobe har jibi har tashin duniya na gaba yayi gaba na baya saide tsintar hula,nayi miki nisan da baxaki taɓa kamo ni ba saide ki ƙare abayana,mijin dakike ikirarin Afiya tasamu naga dai Eman ce tafara saninsa ƙaddara tafaru wacce ta hana auren nasu,shine yanxu kuka shiga kuka fita akan shi yaxo xai auri Afiya,nayi miki nisa Aisha,mijin ma sai wanda ƴata ta kawo kuka ƙwace,shine har kike da guts din faɗa min magana?ke yakamata nacema ki fita harkata agidan nan,kuma shirun danake miki ba tsoro bane gudun magana ne,amma daga rana me kama ta yau mu xuba mugani shege ka fasa sannan tsakanina dake xa'aga mai ƙurarren asali,get your filthy body out of my sight,fitar min daga falo"sakin baki mummy tayi tana mamaki,haka hajiya kwaise da mama,basu taɓa tunanin Umma nada baki haka ba sai yau,mama ce taja Mummy suka fita daga part din mummy sai kallon umma kawai takeyi tana jin tsanarta na saukar mata kamar ruwan sama,hajiya kwaise da mamaki ya cika ta takoma part dinta ta xauna tanata tunane-tunane,can dai ta mike tashiga part din Abba,lokacin yana xaune da Alameen suna tattaunawa akan business din alameen wanda Abba yayi investing few years ago,yayi mamakin ribar daya samu domin ba kaɗan bace,anan yakara tabbatar da Alameen is super rich,mai ya rage yanxu banda Aure?yaso ya mishi maganar sai mummy taxo mishi da maganar Afiya wacce ta sage mishi gwiwa ta sa jikinshi yin sanyi.xama tayi tana fadin"Sannu da hutawa Abba"yace"Yawwa"yana cigaba da baiwa Alameen shawarwarin yadda xaibi ya kara expanding business dinshi,anan Alameen ke fada mishi cewar yanada experts masu mishi hakan.Duk wannan budurin da akeyi hajjo na ɗakinta  tana bacci.

"I'm asking you,who's the girl?" Fauxa ta tambaya akaro na biyu muryarta Na rawa,sabbin hawaye na xubo mata,xaro ido Sadeeq yayi yana kallonta,bai San me xaice ba awannan lokacin,ganin yadda jikinta ke rawa yasa shi riƙe ta tana kokarin ƙwacewa saide ya hanata damar yin hakan,ya kwantar da kanta a ƙirjinshi tana jin yadda heart dinshi ke beating da sauri,runtse ido tayi tana girgiza kai,tace"fada min wacece yarinyar "Tana jin yadda ya sauke ajiyar xuciya mai nauyi sannan yace"meyasa kike tambayar abinda xai bata miki rai?I don't want to hurt your feelings no more,dan haka just keep that question aside"saurin dagowa tayi tana kallon fuskar shi mai dauke da damuwa tace" i don't want to see you in pain no more,inason ka dawo Sadeeq dinka Na asali,mai yawan fara'a da yawan magana,wanda baya ɓoye mini komai na rayuwar shi,I want my old yaya sadeeq not this recent one"bai San sanda kwalla ta cika mishi ido ba,saboda bai yi tunanin abinda xata fada ba kenan, Fauxa na mishi soyayyar ban mamaki,bai gama mamakin hakan ba yaji tasake fadin"babu abinda  baxan iya maka ba arayuwa to make you happy,your happiness is my number one priority and concern,xanyi supporting ɗinka awannan kudurin naka with pure heart da kuma kyakkyawar fahimta,I just want to know who the girl is".saurin owning lips dinta yayi maimakon ya bata answer,saboda hankalinshi bai kwanta da maganar ta ba,duk da ya tabbatar da tana mahaukacin son shi but he's doubting her,tunanin shi yana bashi Alameen ne ya tsara mata hakan,tayi niyyar shunning kiss din sai takasa,saboda yadda gangar jikinta ke welcoming din Sadeeq kamar sun shekara basu hadu ba haka takeji,yasan wannan ne weakness dinta shiyasa yayi mata hakan domin ya rufe mata baki,Fauxa Is very curios,may be tafara haɗa bakin xaren ne but she wants to be sure akan lamarin tunda abun is very sensitive,dole sai tabishi ahankali kuma cikin tsari,tunanin dayayi kenan which is totally opposite da abinda ke ran Fauxa,ita harga Allah she's ready to that for him,koda hakan xaiyi costing farin cikin ta,ai lafiyar shi itace gaba da komai,sosai maganganun Dr Ansar suka tsaya mata akai,suka maƙale acikin xuciyarta,duk wani tunani daza tayi sai ta dauko maganar Dr Ansar ta sa aciki,hakan ne ya hanata tayar mishi da hankali gakuma alameen dake gefe yana lallashin ta.uwa uba tsananin son Sadeeq din datakeyi bana wasa bane.
Ahankali Eman ta buɗe ido tanajin xafin xaxxabin ya ragu Sosai,hakan yasa gumi suka tsastsafo mata,kanta ne bai dena ciwo ba har lokacin,asanyaye take kuka kasa-kasa,tanajin takaici dakuma baƙin cikin sauraran Sadeeq data rinqayi,tayi tada-sanin tsayawa na minti ɗaya tareda Sadeeq ɗin,tabbas ayanxu ta tabbatar da cewar akwai abubuwan da baxaka fahimta ba har sai hakan ya faru dakai,misalin abinda yafaru da ita ayanxu tana jin kamar xuciyarta xata tarwatse,tana imagining pain dinda Fauxa xata shiga alokacin data fahimci son da Sadeeq ke mata,akullum tana ɗora hakan akan mixanin hankalinta ashe tunaninta baida xurfi,saida Afiya ta ɗanɗana mata xafin shi sannan ta tabbatar da ta tafka babban kuskure data tsaya tana jin wasikar jakin Sadeeq,wannan tunanin ne yakusa exploding xuciyarta,ta riqa kuka kamar ranta xai fita,kamar ta cire xuciyarta ta ajiye agefe takeji,kanta kuwa kamar ya faɗi saboda tsananin ciwo,daƙyar Eman ta miƙe tana jin jiri ta jawo jakarta ta dauko karamar wayarta,tana kuka take dialling numbar Fauxa,ta tabbatar alhakin Fauxa ne yafara kamata tun yanxu,fauxa na kitchen tana girki taji wayarta Na ring,ganin Eman ce me kira yasa ta sauke ajiyar xuciya,tace"Eman,sai yau kika tuna dani?"sai kuma tayi shiru jin Eman Na dirxar kuka,gaban fauxa ne yafadi tace"kuka Eman?what happened?"so take tabata hakuri amma ta rasa ta hanyar daya kamata ta fada mata hakan,tana shessheƙar kuka tace"afiya is getting married to Aliyu".wayar Fauxa ce ta silale ta faɗi daga kunnenta saboda tsabar firgici da tashin hankali,saurin dauko wayar tayi arikice tana kaiwa kunnenta,bakinta na rawa tace"what?!!!Kinsan me kike fada kuwa?"kuka Sosai Eman ta fashe dashi takasa cewa komai,sai kawai ta ajiye wayar agefe tacigaba da kuka,silalewa Fauxa tayi tai xaman daɓaro akasa tana jin hawaye suna xubo mata,takasa yadda da maganar Eman,wani kalar cin amana ce wannan?takasa apprehending hakan sai kawai ta mike ta kashe gas din takoma bedroom din Sadeeq tana kallonshi hankalinta gabadaya baya jikinta,wani tausayin Eman ne ke ratsa ta,meyasa Aliyu da Afiya xasu mata haka?meyasa su Abba xasu yadda da auren?why is Eman going through this kind of pain?why is she always suffering??,Sadeeq ne yayi saurin tasowa ya riqota suka xauna agefen gado,yace"meya faru?"tana sauke ajiyar zuciya tace"yaya Sadeeq Emaann..."sai kuma takasa cewa komai,gaban Sadeeq ne yafadi yayi saurin sakinta xuciyar shi Na wani irin bugawa yace "what happened to her?"yayi mata tambayar data daure mata kai,wacce ta tabbatar mata cewar akwai wani abu acikin tambayar,dubaga yadda yayi reacting ta san ba ƙaramin damuwa yayi ba da maganar tata,sai kawai ta tsura mishi ido tana jin jikinta nayin sanyi....

Masu posting a groups ku cigaba da yi,saboda mutane na damuna ta pc kuma bana iya replying,dan Allah idan kunji ana tambaya kuyi kokarin turawa.

Zaynab Yusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now