PAGE 27

102 5 0
                                    

EMAN....PAGE 27

   "Na dade ina adduar Allah ya bani iko da kuma damar fada miki damuwata,kamar yadda kike son sani tun akaron farko,saide awancan lokacin ina tunanin abubuwa masu yawa,xuwa yanxu kuma abubuwa dayawa sun canja,wallahi fauxa ina tsananin sonki,kuma ke shaida ce,ina tsananin kaunar ki,bana so kiyi tunanin nadaina sonki ne ko kuma na rage"ya girgixa kai asanyaye yacigaba da fadin"har yanxu kinada babban matsayin da babu macen data isa ta mallake shi acikin xuciyata,you're my first and true love,wacce nake mutuntawa da darajawa,babu macen da xata kai matsayin dakika kai awurina,nasan abubuwan daxan fada miki xasu b'ata miki rai,they'll definitely break your heart,amma kisani i didn't mean to hurt your feelings,kinsan damuwarki babban tashin hankaline agareni,ina so Dan Allah ki fahimceni Fauxa,reason with me saboda ba yin kaina bane yin Allah ne,Allah ne ya kaddara min hakan acikin rayuwata,I never bargained for it".xafafan hawaye ne kawai ke xubo ma fauxa,xuciyarta na dukan ɗari-ɗari tana jin kanta na ciwo kamar xai tarwatse saboda tashin hankali,takasa apprehending abubuwan da Sadeeq ke fada,takasa tsayawa ta saurare shi balle ta fahimci me yake nufi,abu ɗaya ne ya tsaya mata arai shine yadda yake cewa he loves her more than any other woman,kenan akwai wata acikin xuciyar shi?akwai wata macen arayuwar Sadeeq dinta bayan ita?ji tayi kamar ana bubbuga mata Ƙusa acikin kwanyar ta,Saida yafara maganar yaji wani tashin hankali yana saukar mishi,ganin yanayin Data shiga yasa shi cewa"Calm down Fauxa,take it easy pls"hawaye masu xafi na wanke mata fuska yayinda xuciyrta ke ƙuna tace"continue yaya Sadeeq "tafaɗa da wata raunatacciyar murya wacce bai taɓa ji ba,runtse idanu yayi sannan yace"I don't want you to think wai laifin kine,it's not your fault at all,bakida laifi fauxa domin kina iya bakin ƙoƙarinki wurin faranta mini,you're trying your best to make sure banyi lacking komai ba,wallahi babu abinda kika rage ni dashi,kawai kaddara ce ta xo mana ahaka,saide ina fatan xamu cinye ta muna meyin tawakkali dakuma imani da Allah,all I want you to do is to find a small spot acikin xuciyarki and understand me dan Allah ki fahimce ni fauxa"ya karashe maganar yana saukowa kasa kamar wani me roƙon gafara,itadai fauxa kallon shi kawai take tana kuka,saide kukan mara sauti ne amma me karya xuciyar idaniyar dasuke kallon ta,wannan dalilin ne yakara daga mishi hankali,yace"I'm sorry you're going through this because of me,wallahi banida yadda xanyi ne,ni kadai nasan tashin hankalin danake ciki,wannan ce damuwar data sa mini hawan jini take farautar rayuwata,banida option din daya wuce Na fada miki because you're my best friend,banida wani aboki wanda na aminta dashi fiyeda ke"runtse idanu tayi tana jin kamar wuƙa Sadeeq ke sawa yana caccakar xuciyarta,wani masifaffan kishi ke taso mata ya tokare mata wuya,ga wata xaxxafar kaunar Sadeeq din dake kai kawo acikin xuciyarta,ji tayi kanta yayi mata nauyi kamar an ɗora mata dutsen dala akai,muryarta ashaƙe saboda yadda kirjinta ya riqe gam tace"yaya Sadeeq budurwa gareka?"ta faɗa cikeda ƙunar xuciya tana jin kamar ta mutu saboda bakin ciki,girgixa mata kai yayi alamar a'a sannan yace"I'm in love for the second time "kalaman Sadeeq ne suka kusa xame ma fauxa dalilin kisa batareda ɗigon jini ba domin sune suka sumar da ita,bai lura ba sai ji yayi tayi baya ta faɗa saman gadon,cikeda tashin hankali Sadeeq ke jijjigata abanxa,ya ɗauke ta kamar baby ya saka amota xuwa asibiti,kuka yake Sosai har suka karasa yana danasanin fada mata,Yana xaune a reception abin duniya ya taru ya mishi yawa,yana jin dama he can went back in time da babu abinda zai hana shi cigaba da b'oye mata hakan har xuwa wani lokaci,domin ya xurfafa tunani Sosai kafin ya fada mata amma sam bai kawo xata sume mishi ba,idan wani abun ya sameta fa?gaban shine yayi mummunan faduwa,wasu gumin tashin hankali suna karyo mishi,hawaye kuwa kamar an bud'e famfo,yanzu me xai kira gidan su fauxa ya fad'a musu ?shine bai sani ba,fatan shi shine ta farfado lafiya batareda wani Abu ya sameta ba,sannan babbar damuwar shi itace kada tafada ma wani maganar,Sosai ya shiga cikin damuwa mai tsanani,can ya mik'e yafara safa da marwa yana jin xaman kara mishi damuwa yake,yafi awa daya tsaye yana tunani,xuciyar shi Na wani irin xillo ya kalli dr me fadin"xaka iya shiga wurinta"wata sassanyar ajiyar xuciya ya sauke sannan ya shiga dakin da take,xaune ya ganta hawaye nata xarya akan fuskarta,ta nutsa cikin tunani mai xurfi saidai kallo daya xaka mata kasan tana cikin damuwa mai tsanani,xama yayi agefen ta tareda jawota ya rungume,sai alokacin tasan da xuwan shi,cikeda masifa da dukkan karfin da Allah ya bata ta hankadeshi tana fashewa da kuka mai sauti,bakin shi na rawa yace"pls fauxa,take it easy"banxa ta mishi tacigaba da kuka kamar ranta xai fita,bata tab'a xaton Sadeeq xai mata hakan ba duk yadda ta d'aukakeshi fiyeda komai aduniyarta,duk yadda take kaunarshi take kula dashi da son ganin farin cikin shi,yet she's still not enough sai da yaje ya nemo wata,hannunta yake son rikewa amma hakan ya gagara gashi yana fargabar kallon kwayar idanunta wanda suke jefo mishi wasu kallo masu ma'anoni daban-daban,shi kanshi yaji tsoron kallon da fauxa ke mishi,da karfi ta furta"stay away from me sadeeq,stay far away"tafada tana riqe kanta mai masifar ciwo,dama akan wata tsinanniya yake shan maganin hawan jini?dama damuwar wata ƴar iska ya saka azuciya har take ɗanɗanar xafin damuwar tashi?she couldn't help but cry,she's feeling useless alokacin,wani irin kuka mai karfi takeyi takasa cewa komai,duk yadda Sadeeq yake tunanin abin ya wuce wurin,bai yi tunanin fauxa xata ɗaga hankalinta har haka ba,tun kafin ma taji wacce yake so kenan,bai taɓa shiga irin wannan tashin hankalin ba sai yau,stammering din dole yafarayi yana cewa"I'm sorry fauxa,pls calm down ki tsaya ki fahim ce ni"wani irin ihu ta mishi tana fadin"bana son ganinka yaya Sadeeq,just get out of my sight "ta fada tana nuna mishi exit,baxai iya bayyana damuwar daya ke ciki ba,yakasa yin komai alokacin Shide yana tsaye yana kallonta kawai,gaban shine yayi mummunan faduwa sanda tace"kira min eman"ya wani xaro idanu kamar xasu fito waje saboda shock din dayaji,baida option din daya wuce tafiya gidan nasu,Allah yaso lokacin hajjo tayi bacci Eman na bedroom dinta,umma ce taxo jikinta asanyaye saboda ya fada mata fauxa na asibiti amma dan Allah kada tafadawa kowa,yanxu xai tafi da eman domin ta taimaka mata,ita dai umma kallon shi kawai takeyi cikeda damuwa ganin gabadaya ya fita daga cikin hayyacin shi,dogon hijab eman tasa sannan tafito falon,turus tayi atsaye tana mamakin ganin Sadeeq,umma tace"gata nan,Allah ya kara lafiya yasa su sallameku yau din"eman dai kallon shi take har lokacin da yafita daga part din umma tana binshi a baya,a main parlour suka ci karo da Al'ameen,ya tsaya kawai yana kallon Sadeeq din wanda ya ɗage kanshi sama ko kallon gefen da Al'ameen yake baiyi ba yayi fitar shi,still yayi yana kallon eman sannan ya kaɗa kai ya shiga part dinshi.
Eman was short of words,yadda yake sauke ajiyar xuciya yana gudu da mota ne ya bata tsoro,har lokacin bai ce mata komai ba,saide lokaci-lokaci yana kallon gefen datake,hakan ne ya sata cikin matsananciyar damuwa,gabanta na wani irin faduwa tace"yaya Sadeeq what happened?"juyowa yayi yana kallonta,yana tabbatar ma kanshi she's worth every sacrifice,saboda so ɗaya tak yake mata,wanda ya mamaye mishi xuciya yake jin baxai iya rayuwa babu ita ba,agefe daya kuma fauxa na maƙale aranshi,tausayinta na nukurkusar xuciyar shi,at this point bai San me xaiyi ba,yana cikin asalin chakwakiya wacce Allah ne kadai zai iya fitar dashi,har suka karasa asibitin bai ce mata komai ba,yana tafiya tana binshi abaya har suka karasa dakin da fauxa take,koda suka shiga ta had'e kai da gwiwa tana rusa kuka saide bame sauti bane,atake eman taji kwalla na cika mata ido,tace"Ya fauxa"!da sauri fauxa ta ɗago fuskarta tayi jage-jage,ganin Eman yasa ta kara fashewa da kuka,sai kawai ta miko mata hannu alamar taxo,da sauri Eman taje suka rungume fauxa najin wata yar karamar nustuwa na ratsa ta,kukan da Fauxa ke yi ne yasa Eman xubar da hawaye,takasa cewa komai sai patting shoulders din fauxa takeyi alamar rarrashi,fauxa tace"nashiga uku Eman,na lalace pls help me"ta furta hakan ahankali tana sake fashewa da kuka,Eman tace"meya faru dake ya fauxa?innalillahi wainna ilaihi raji'un "fauxa tace"yaya Sadeeq ne Eman,ya gama da rayuwata,ya cuce ni"gaban Eman ne yayi mugun faduwa,fauxa tacigaba da fadin"Ina cikin damuwa da tashin hankali Eman,ban tab'a xaton Sadeeq xai iya kallon wata da sunan soyayyah ba sai gashi har kaunarta takai matsayin da xata saukar mishi da hawan jini saboda tunanin Yarinyar,wallahi kirjina xafi yake xuciyata suya takeyi,na rasa me zanyi eman,pls tell me mexanyi?"ta fada tana riko hannun eman,aduniya Eman ji tayi ta tsani kanta da rayuwarta,Fauxa is going through this ta dalilin ta,sai kawai ta fashe da kukan bakin ciki da takaici,haka suka taru suna kuka Shide Sadeeq na tsaye acan gefe yana kallonsu yana jin zuciyar shi na kuna.Eman tace"kiyi hakuri ya fauxa,mubi komai asannu"Fauxa na girgixa kai tace"baxaki fahimci pain dina ba,wallahi ji nake kamar kirjina ba'a jikina yake ba,ya mini nauyi mara misaltu wa,kaina kuwa kamar ana kwankwasa min shi,I'm in pain,in so much pain "tafada tana cigaba da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,jiki ba kwari Sadeeq yaje office din dr suka xo suka ma fauxa allurar bacci,tana rungume ajikin eman bacci mai nauyi ya dauketa,Sadeeq ya sauke ajiyar xuciya yana kallon eman wacce ke kallon shi alokacin,saida ta gyarawa fauxa kwanciya sannan tafita reception.Ta had'e kai da gwiwa tana fashewa da matsanancin kuka,bata tab'a jin haushin kanta irin yau ba,ina tunanin ta yatafi alokacin da Sadeeq ke furta mata kalmar so?kafin ta ba kanta amsa taji ya xauna agefenta,kamar an xira mata allura tayi saurin mikewa ta koma can gefe,ya juyo da mamaki yana kallonta,can yace"magana xamuyi "tana sharce hawaye tace"babu wata magana data rage tsakanin mu yaya sadeeq,na dade ina fahimtar dakai illar aikata hakan,yanxu ka kalli me hakan ya jawo tun kafin tasan ni ce wacce kake so,I'm advising you in no circumstance xaka fada mata cewar ni kake so".kallon ta yayi Sosai sannan yace"that's impossible Eman,miye amfanin fada mata I'm in love for the second time din?idan ban fada mata you're my second love ba wa xan ce mata?"a hargitse Eman tace "I don't know,but don't mention my name "yace"ambatar sunanki yaxama dole "arikice eman tace"bakaga halin da ya fauxa ke ciki bane?"yace"ni bakiga halin danake ciki ba,and mind you ina son matata fiyeda tunanin ki sannan I care for her Sosai,so don't tell me how to take care of my wife,she's my wife,my first love and my true love"ya cigaba da fadin"dole zan fada mata kece wacce nake so akaro na biyu,i don't care anymore,the most important thing shi ne yanxu tasan akwai wata acikin xuciyata,kuma I promise you saina fada mata ke nake so kuma nakeda muradin aure"mikewa eman tayi tace"go ahead and tell her,amma kasani wallahi bazan tab'a auranka ba! Bazan xauna dakai amatsayin miji ba,that I promise you,gara Na mutu wallahi saboda ni akwai ragowar imani axuciyata,fauxa na cikin wannan halin kake fada min haka,kabani kunya!.".ta fada afusace sannan ta koma wurin fauxa tana kuka kasa-kasa.Wani jiri ne ya mamaye ma Sadeeq ido,ya mike dakyar yana dafa bango ya shiga consultation room yana sauke ajiyar zuciya,kanshi kamar an daura igiya an daure saboda tsananin ciwon kai,dr Ansar ya auna bp dinshi yaga ya hau Sosai,sai kawai ya Mike ya fita,Dakin da eman take ya shiga,yana kallon ta yace"are you sadeeqs sister?"asanyaye ta gyada mishi kai alamar Ehh,yace"follow me "yayi gaba tana binshi abaya har suka shiga office din dr ansar,taga Sadeeq na xaune ya dafe kai,dr ansar yace"kunsan Sadeeq nada hawan jini wanda yake kokarin rikidewa ya koma ciwon xuciya?"dafe kirji eman tayi tana girgixa kai ,yace"last two months yafara xuwa saide kullum ciwon nashi karuwa yakeyi,nace mishi ya daina tunani amma yaki,yanxu jinin shi ya hau Sosai saboda damuwa,bansan mecece matsalar shiba balle nayi advising dinshi yadda yakamata,sai yau Allah ya hadani da ke yar uwarshi,dan Allah ki sanar ma iyayenku halin dayake ciki,wallahi yana bukatar taimakon gaggawa"gwiwa biyu akasa Sadeeq ya sauko yana riqe hijab din eman,yana kokarin passing out yace"repeat yourself eman,kinga sai na mutu na huta da wannan bakin cikin..."yana kaiwa nan ya sume,taimakon gaggawa aka bashi saide shi Intensive Care Unit aka kaishi saboda yadda xuciyar shi keyi,eman ta tsorata Sosai da yanayin Sadeeq sai kawai ta fashe da kuka ta dora hannu akai tana kuka mai tsanani,tana Data sanin fada mishi hakan sannan dayan bangaren fauxa ce ke cikin damuwa ta dalilinta,tabbas su hajiya kwaise sunyi gaskiya duk inda taje saita xama matsala arayuwar mutane,gashi yanxu both fauxa and sadeeq are suffering because of her,dr Ansar ne ya kirata tashiga office dinshi har lokacin tana kuka,ya kalleta Sosai sannan yace"last words din Sadeeq ya nuna min cewar ba kanwar shi bace ke ta jini,kamar ma saboda ke yake cikin damuwar"eman na kuka ta gyada mishi kai,tana son tattauna problems dinta da wani domin su samu solution,sai kawai ta bud'e ma dr Ansar cikinta ta bashi labarin komai tana yi tana kuka,shi kanshi dr ansar ya girgixa da wannan lamarin,asanyaye yace"abubuwan dakika fada min ya tabbatar min da Sadeeq is suffering from obsessive love disorder "Xaro ido eman tayi dr ansar yacigaba da fadin"OLD wato obsessive love disorder can be treated,zai iya warkewa daga wannan cutar idan har ya bi matakan dasuka dace,abin damuwar shine ya kamu da hawan jini,kinga kenan dole akiyaye shigar shi cikin damuwa,musamman ke,kece xaki tabbatar ya daina shiga damuwa balle yayi tunani,nikuma xan rika bashi drugs wanda xasu riqa taimaka mishi,na fahimci akwai matsala mai girma idan kika amince da soyayyar shi,amma maganar gaskiya inde lafiyar shi ake so hakan yakamata ayi,a aura mishi ke kawai inde ana son shi da lafiya da kuma tsahon rayuwa,irin haka ne sai xuciyar shi ta buga abanxa"tunda dr ansar yafara magana eman batace komai ba sannan bata daina kuka ba,dr ansar ya dora da fadin "Amatsayina na babban mutum,uba,kuma likitan xuciya,ina me shawartar ku akan bashi muradin xuciyar shi,ni dakaina xanje na fahimtar da Abban naku kuma nasan xai fahimce ni,karkisa damuwar abinda mutane xasu fada akan hakan,kiyi focusing akan lafiyar Sadeeq,ni xan shige muku gaba domin tabbatar da Sadeeq ya samu cikar burinshi da kuma cikakkiyar lafiya,domin shima ya cigaba da rayuwa cikin salama da farin ciki".Tun da Al'ameen ya shiga part dinshi yakasa thinking straight,mikewa yayi xaune saboda ya kasa bacci,jikin shi ne ke mishi wani iri kamar wani abu ya faru,tunanin fauxa kawai yakeyi,yadda yaga Sadeeq na shisshige ma eman ne ya daure mishi kai,musamman awurin Kamu,ya fahimci duk wasu moves din Sadeeq din,jiki ba kwari ya xura white color jallabiya ya dauki car key,yana kulle part dinshi yake dialling numbar fauxa bata d'aga ba,ya kira ta Sadeeq nan ba'ayi picking ba,gaban shi ne yayi mummunan faduwa take ranshi ya fada mishi tabbas something is fishy,gidan fauxa ya je mai gadi ya bud'e mishi gate,bai sauka daga cikin motar ba yake tambayar,"masu gidan Na nan?"cikeda damuwa mai gadin yace"sun tafi asibiti,hajiya ce ba lafiya"gaban Al'ameen ne yayi tsananin faduwa,yace"Fauxa ba lafiya?wani asibitin suke xuwa?"mai gadin ya mishi kwatance ko tsayawa jin karashe baiyi ba ya figi mota yana driving recklessly,gumi na xubo mishi duk da sanyin Ac,alla-alla yake yaga halin da fauxa ke ciki,aduniya yana kaunar fauxa fiyeda misali,tafiyar minti 30 ce takaishi asibitin,ko tsayawa kulle motar baiyi ba yashiga reception yana nishi kamar wanda yayi gudun thousands of kilometres,tsayawa yayi cak yana kallon Eman dake xaune a reception ta xabga uban tagumi gakuma hawaye nata xubo mata,yaji gabanshi ya fadi,jikinshi yayi sanyi,asanyaye ya karasa inda take saide yakasa ce mata komai,ita kuma ta nutsa can cikin duniyar tunani,ji yayi kafafunshi sunyi sanyi ya xauna agefenta yana sauke ajiyar xuciya,bata ankara ba taji muryar Al'ameen ta sauka cikin kunnenta,yace"how's fauxa doing?wheres she?"gaban Eman ne ya fadi ta kasa hada ido dashi,bakinta na rawa tace"tana bacci"yace"jikinta fa?"saida wasu xafafan hawaye suka xubo mata sannan tace"da sauki"shiru ne ya biyo baya nawani lokaci,kamar an fada mishi  wani abu sai ya sake kallonta yace"where's Sadeeq?"ya tambaya a bit furious,gaban eman ne ya bada daram!ta rasa me zatace mishi alokacin,ya sake furta"kaini wurin dr dayake kula da fauxa"nan ma shiru eman tayi tana jin gabanta na faduwa,bata son dr ansar yaga Al'ameen dan ta tabbatar sai maganar ta fito,saboda Dr ansar ya tabbatar mata he'll try his possible best,ahankali yace mata"are you deaf?answer me "tsuru _tsuru tayi kamar wacce tayi ma sarki karya,sai kuma suka daga kai atare jin an ambaci sunan Al'ameen,koda suka juya fauxa ce tsaye tana rusa uban kuka,Alameen yayi saurin mikewa ya tarota tana kokarin faduwa ya riqeta Sosai ranshi na baci xuciyar shi na tafarfasa,tace"kaji abinda Sadeeq ya min?"wani b'acin rai ya tsinci kanshi aciki mara misaltuwa,ji yake kamar yaje duk inda sadeeq din yake ya shak'e mishi wuya,amma ya tabbatar ma kanshi Sadeeq ya tab'o shi kuma wallahi he'll surely teach him a lesson tun kafin yasan abinda Sadeeq din ya mata,yayi alkawarin daga wannan lokacin fauxa baxata sake zubar da hawaye akan shi ba!...

Sai ana hakuri dani,nasan yayi kadan,ayi hakuri ayi manage😴

Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now