PAGE 06

148 5 0
                                    

Eman...🥀

Page 6

  Jiki ba kwari umma ta zauna tareda dafe kanta mai tsananin ciwo,so take tadaina jin zafin da zuciyarta ke mata,so take ta samu sassauci acikin zuciyarta me balbala da wuta,hakika ta shiga cikin garari da matsalar rayuwa amma wannan matsalar tafi kowacce tayar mata da hankali,tashiga cikin matsin rayuwa sanda take auran babana,tasha wahala Sosai,babana ya gana mata azaba,Duk wadannan tashin hankalin su biyo bayan wanda na jefata aciki yanzu,'yarta d'aya tilo aduniya ce ta lalace agaban idon ta?innalillahi wainna ilaihi raji'un tafurta  tana mikewa tsaye wasu hawayen na zubo mata,hjy kwaise dake tsaye ce ta zauna,tabbas tausayin umma ya kamata Sosai duk da kishin dake tsakaninsu,tace"kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai,shi kadai zai miki magani".gyad'a kai kawai umma tayi batareda tace komai ba,domin ita kadai tasan zafin da zuciyarta ke mata,ba wanda zai fahimci halin datake ciki sai ita,ita kadai tasan ne ke zarya acikin zuciyarta,takasa thinking straight tunda abin ya faru,tana bukatar kad'aicewa ita kadai na tsahon lokaci sannan tana bukatar hutun ganin eman datakeyi akai akai,ita kadai tasan me takeji idan ta bud'e idanu taga Eman akusa da ita...Shigowar Abba rai abace yasa hjy kwaise gyara zama tana kallon yadda yayi kicin kicin da fuska,ko ba'a fada ba tasan an fada mishi abinda ya faru,tana mamakin yadda yake daukar damuwar Fatima da eman ya d'ora akanshi,gabadaya ya damu kanshi akan matsalar su shine abinda bataso.Batareda yace komai ba ya shiga bedroom din umma kai tsaye ko kallon gefen da hjy kwaise take baiyi ba,mikewa umma tayi jiki ba kwari tabi bayanshi tana jin wani jiri na d'ibarta,da wani kallo hjy kwaise tabi bayan umma sannan ta mike tafita.
Agefen gado ta tarar da Abba yana gyara wrist watch dinshi,fuskar shi ahade,saita zauna akasan Abba tana share hawaye tace"kayi hakuri Abba,nikadai nasan me nakeji".shiru yayi yana kallonta sannan yace"anjima Fauza zata zo ta tafi da eman".tace"Abba gidan Fauza kuma?"gyada kai yayi batareda yace komai ba.
Zuwan hjy kwaise ne ya yasa mummy matsawa tabata wuri,rai bace tace"waya fadawa Abba abinda yafaru?sanin kanku ne zai shiga cikin damuwa?kunsan baya wasa da lamarin eman dana uwarta".
Mama tace"kema kina complain balle mu da aka mayar ba komai ba?bamusan inda ya jiyo ba"tafada tana kyabe baki,mummy tace"bansan me fatima da tsinanniyar Yarta suka mishi ba yake kaunarsu,daya shigo fa ko kallon inda damuke baiyi ba balle gefen da 'ya'yanmu suke".takarashe maganar cikeda takaici.
Shiru hjy kwaise tayi itama taji zafin abinda Abban yamata,amma bazata magantu da maganar ba agaban su mummy,a inda tayi musu zarra kenan,baka jin cikinta ko da wasa saide idan ita taso.
Wayarta dake ring ta kalla,sunan Fauza ne ya fito saita gyara zama sannan ta d'aga wayar,bayan sun gaisa Fauza tace"anjima zanzo,dan Allah Mami kisa ayimin dambu".
"Toh,ai da kinyi zamanki tunda weekend ya kusa,sai na aiko miki dashi".cewar hjy kwaise tana muskutawa ta gyara zama.
Anty Fauza tace"hala bakuyi maganar da abba ba".
"Wace magana?"ta canza harshe izuwa shuwa tana kallon mummy wacce ke sauraron maganar datakeyi.
"Ya kirani akan batun Eman,zata zauna awurina for some time,idan umma ta sauko saita dawo".gaban hjy kwaise ne yayi mummunan faduwa tace"what?"tareda mikewa tashige part dinta zuciyarta na suya,meyasa abba zai yanke wannan hukuncin batareda yaji nata ra'ayin ba,eman ta zauna a gidan Fauza a wani dalilin?wasu shegun gumi ne suka feso mata,jikinta Na tsuma tanajin kamar tayi tsuntsu ta cimma Abba a bangaren umma ta zazzage mishi kwandan bala'in da bata tab'a yiba tsahon shekarun dasukayi.

   "Haba eman ya zaki b'ata rawarki da tsalle?meyasa kika zab'i wannan rayuwar?kinsan illar fushin uwa akan d'anta?anya kinason gamawa da duniya lafiya?kuka fa umman ki keyi akanki,bayan fushin data d'auka dake,ki rufawa kanki asiri ki bi duk hanyar data dace ki bawa ummanki hakuri,wallahi tana fushi dake fushi mai tsanani"cewar anty Habiba tana goge mini jinin dake goshina,ina jan majina nace "anty habiba ina cikin tsananin damuwa,wacce bazata misaltu ba,babban tashin hankalina shine fushin da umma keyi da ni,wallahi kullum da wannan damuwar nake kwana nake tashi,banda masaniya akan abinda yafaru sharri aka min dan arabani da Aliyu sannan a guntule siririyar fahimtar data rage tsakanina da umma,anty habiba ki taimakeni".nakarashe ina fashewa da kuka mai tsanani,itama kukan tafara tana cewa"taya zakice sharri aka miki eman,wannan wacce irin k'addarar rayuwa ce?tundaga titi fa kika zo gida kafafuwanki ba takalmi,kanki bud'e...."saurin datse bakinta nayi ina cigaba da kuka mai ciwo,ni eman ce na aikata wannan aika aikar amma bansan lokacin danayi ba,I can't remember na tab'a shan any sort of intoxicants,"idan kince bakisan hakan ya faru ba nacikin dakinki da muka gani fa?suma duk baki San dasu ba?".
Innalillahi wainna ilaihi raji'un nake furtawa cikeda tashin hankali,"trust me,wallahi banda masaniya akai,Allah ne shaidata kuma shine zai wanke ni daga d'aurin zato".
Shiru anty habiba tayi tana goge hawayenta nace"sunyi nasarar rabani da Aliyu,sun shiga tsakanina da iyayena da 'yan uwana,sun rabani da kowa ,yanzu ina zansa rayuwata?daga ina zan fara?".
Zama anty habiba tayi tana cewa "eman da abinda muka gani zamuyi amfani,dole mu yarda da abinda muka gani koda kuwa sharri ne,amma idan halinki ne ay bazaki fasa ba".
Cikeda damuwa nace"abinda nake son umma ta fahimta kenan,amma gabadaya bata kaunar ganina,yanzu ina zanje Na daina b'atawa umma rai?".Shiru anty habiba tayi sannan ta mike ta jawo akwatina mai girma,kayana ta hada set goma sha biyar da hijabs da veils,takara dauko wata jakar ta zuba duk abubuwan bukata ta,nide kallonta kawai nakeyi amma hakan datayi yayi mini dadi,koba komai zan ba umma sarari tayi clearing head dinta,sannan rashin ganina zai sa ta sauko daga inda tahau na fushi dani.
Tabangaren hjy kwaise hankalin ta gabadaya atashe yake,kosu inteesar da afnan dasuke gaisheta batabi takansu ba,gabadaya tunaninta da nazarinta ya tafi izuwa hukuncin da Abba ya yanke Na zaman eman agidan Fauza,ta manta dawani dambu sai safa da marwa take a tsakiyar falonta,ko shigowar Suraj da Nurain falon bata jiba ,saida Nurain ya dafa shoulders dinta,kamar wacce ta tashi a bacci tayi saurin juyowa tana kallonsu,hankalinsu ya tashi ganinta cikin damuwa,ba shiri sukayi cilli da manya manyan ledojin Welcare dasuka riqo suna tambayar lafiyarta,murmushi tayi tace"karku damu,ku zauna kuji".aduniya hjy kwaise batada abokin shawarar dasuka wuce 'ya'yanta.
"Ai wannan ba abin tayar da hankali bane Mami,khair In shaa Allah"cewar suraj,nurain yace"haka ne".sai alokacin ta danji sanyi aranta sannan ta tambaye su ya iyali?da alhamdulillah suka amsa sannan suka cigaba da fira.
"Yaushe na wajen Salima zasu zo amatso da date din bikin tunda an fasa yin Na eman?".Suraj ya tambaya Nurain yace"a'a tukunna dai har yanzu basu tattauna da yaya ba"
"To ku fada mishi mana tunda shi Al'ameen din baya nan".cewar hjy
"Zamuyi magana dashi,duk abinda yace zamu sanar miki".cewar Nurain yana tambayar"Yaushe zai dawo ne?".acikin watan nan yake sa ran dawowar".
Taliya mai rai da lafiya Salima ta dafa musu ta zuba a babban tray,sukaci gabadaya suna hira,hakika hjy kwaise tayi kokarin had'e kan'ya'yanta suke kaunar junansu.
Bangaren umma suka shiga da leda cikeda chocolates,musaddiq auta  yakarba cikeda murna sannan yashiga bedroom din umma,zaune take kan sallaya tana jan carbi ya shigo,"umma su yaya nurain Na falo,kinga chocolates dinda suka kawo mana".murmushin yak'e ta sakar mishi sannan ta mike ta fita falon,cikeda girmamawa suka gaisheta Ta amsa tana sunkuyar da kai,gasu tamkar 'ya'yanta suke amma kunyar su takeji ba kadan ba,suma sun fahimci hakan sai basu ce mata komai ba gameda abinda yafaru tunda sunyi mata jaje akaron farko,ruwa da drinks ta kawo musu masu sanyi,kadan kadan suke tab'a hira kusan gabadaya hirar akan yaran gidan ce,tace"ya labarin yayanku?gabadaya yayi scarce baa jinsa Kota waya".
Nurain yace"yazama busy Sosai amma karshen wannan watan muke sa ran dawowar shi,kinsan zai dade idan ya dawo sannan yakara komawa".
Umma tace"Allah ya dawo mana dashi lafiya "suka amsa da amin.
Adaidai nan na fito falon,mutuwar tsaye nayi ina kallon su,nakasa cewa komai kuma Na kasa motsawa daga inda nake,kallo daya umma tamin ta d'auke kanta,Nurain yace "hajiya Eman ba magana?"samun kaina nayi da kasa tsayawa on my feet,nasamu wuri Na zauna inajin azababbiyar kunyar su nace"Ina wuninku "nai musu jam'i ina kokarin mikewa tsaye,ganin kamar banason maganar yasa sukayi shiru suna kallona har na wuce ma ganinsu,ajiyar zuciyah umma ta sauke tana kallon Nurain da Suraj,few minutes suka kara sannan suka fice suna jinjina girman lamarin eman.
  "Maman eman halan su waye sukazo?"Cewar anty habiba,"yaran hjy kwaise ne ".jinjina kai anty habiba tayi sannan tace "zan tafi da eman tayi mini kwana biyu".kyabe baki ummma tayi tace"gidan Fauza zataje bisa umarnin Abba".ajiyar zuciyah anty habiba tasauke tana jin dadin yadda yayarta tasamu support daga wurin Abba,tace"dan Allah kidaina sa ma kanki damuwa,ita damuwar nan bazata warware miki matsala ba saide ta jawo miki ciwo kinga anyi two zero kenan".gyada kai umma tayi tace"Allah ya warware mana".
Tunda nakoma daki ban kara fitowa ba,inata tunanin makomar rayuwata,gabadaya banajin dadin rayuwar,babban burina shine auren Aliyu amma yabi ta shanun sarki,ina cikin wannan tunanin umma tashigo dakin,gabana yayi mummunan faduwa domin nasan babu magana me dadi atsakanin mu,tun kafin tace wani abu nafara zubarda ruwan hawaye
Tace mini"sauran ki kara jawo mini magana agidan Fauza,tunda burinki shine kiga ina cikin damuwa da tashin hankali,ki kashe ni ki huta eman.."saurin rufe bakin umma anty Habiba tayi tana girgiza mata kai,ko kallon gefen anty habiba batayi tacigaba da cewa"kibari nafada mata abinda ke raina habiba kamar yadda ta aikata mini San ranta".
"Maganar ki masifa ce agareta tunda ba alheri zaki furta ba yaya,dan Allah kiyi hakuri".cewar anty habiba tana fitar da ita daga dakin,kuka mai sauti na fashe dashi ina jin dama na mutu na huta da wannan tashin hankali,ina jin sanda su amir suka fitar mini akwatina saina mike na zura hijab dina har kasa nabi bayanshi,a babban falo na tarar da kowa nagidan,bani da yadda yazanyi yasa naja gefe Na rab'e,amanata abba yaba aunty Fauza ta amsa mishi Sosai sannan tace"abba Eman Tamkar su inteesar ce agareni,in shaa Allah bazata rasa komai ba awurina".Sosai nake kuka kamar amaryar da za'a kai gidan miji,umma ko falon bata fito ba saboda bakin ciki,hjy kwaise taja baya Sosai dan ko kalma daya bata furta ba.
A motar mijinta Land Cruiser black color muka tafi gidanta dake Race course,tunda na shiga motar nake kuka mara sauti har muka karasa gidan,ta ina zan fara rayuwa agidan anty Fauza?
Mijinta Sadeeq ne ya shigar mini da akwatina itakuma ta riqeni muka shiga ciki,'ya'yanta Anum da Asad sunyi bacci,dakinta takaini tana cewa"eman pls feel at home".mijinta dake ajiye min kaya yace"eman kukan Na miye ne?bakya son zama damu ne?"ahankali na girgiza kai sannan na share hawayena ina tunanin yadda zan fara rayuwa agidan anty Fauza.

*Tofah readers,akwai cakwakiya a rayuwar Eman,wani irin zama eman zatayi agidan anty fauza?🤔hmmmm bakina da goro muje zuwa*.

Zaynab Yusuf ✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now