PAGE 09

148 4 0
                                    

Eman...🥀

Page 9

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Lumshe ido Rafee'ah tayi hawayen bakin ciki suka gangaro suna d'iga akan hannunta,ta jingine kai da bango tana jin zafin maganganun mummy suna damun zuciyar ta me tsananin rauni,ta kalli sadeeya wacce ke zubar da nata hawayen bakin cikin,bakinta wanda ya mata nauyi ta bud'e tace"ban San meyasa mummy ke haka ba,mu dinnan bamuda ikon yima kanmu komai sai abinda Allah ya kadarta faruwar shi agaremu,miye laifin mu akan abinda bamuda ikon yima kanmu?meyasa mummy ke tashin hankalinta akan abinda batada ikon yimana har sai lokacin da Allah ya kaddara faruwarsa?"tayi tambayar da ita kanta batada masaniya akan amsoshin su,sai tacigaba da fadin"Aure yanada matukar amfani kuma sunnah ce mai karfi amma jinkirin Aure ba laifin mu bane,Shi aure lokaci gareshi kuma bazaka tab'a wuce lokacinka ba,har yanzu lokacin mu beyi bane shiyasa muke zaune agida,kuma ina miqa godiya ta ga Allah daya sanya rashin auren bai sa muna aikata alfasha ba,wannan ba abin farin ciki bane?azamanin nan da saide muce innalillahi wainna ilaihi raji'un,Allah ya karemu ya kamemu agidan iyayen mu,ya suturta mu ya kiyaye mu daga fadawa tafarkin shaidan,ya sanya mana tsoronshi da tsoron abinda mutum zai tarar ranar gobe kiyamah,maimakon mummy tayi farin ciki da haka take sab'anin hakan,saboda gasa da buri take kokarin tarwatsa mana rayuwa?karki manta babu biyayya awurin sab'on ubangiji,Tsantsar biyayya ga Allah shine Ka kasance a gurin da Allah ya umarce ka da kasancewa, sannan kuma ka kauracewa duk wani gurin da Allah ya haneka da kasancewa acan, hakan shine tsantsar biyayya ga Allah,kinga abinda Mummy tace muyi ya sab'a da tsantsar biyayyar mu ga ubangiji,shisshigema samari da duk abinda mummy tafada basa cikin addininmu,if there's something I'll never compromise is my deen and aklaq saboda nasamu mijin aure".
Tsananin kukan da Sadeeya tayi yasa muryarta dishewa,jiki ba kwari tace"ni abinda ban fahimta ba shine titi zamu fita mu riqa cewa azo a auremu azo a aurenmu?matsalar mummy  sune
hangen abun wani,gasa dakuma son zuciyah,batason d'an wani ya cigaba tayaya Allah zai bar nata su motsa?da ace zata tsarkake zuciyarta daga ciwon hassada da tuni damuwarta tazo karshe,abinda ke damuna shine fushin datakeyi damu tana fada mana kalamai marasa dadi wanda idan bamuyi wasa ba zasu bi har zuriar mu suyi naso,shi bakin uwa kaifi gareshi shiyasa ake son uwa ta dinga  shima d'anta albarka kamar yadda Mami keyi,ta gatanta 'ya'yanta ta riqe su gam da hannu biyu gashi rayuwarsu ta samu daidaito".haka suka cigaba da jajantama juna abubuwan dake damunsu musamman akan jinkirin Aure!.
Mtsww ta zabga tsaki a karo na biyar zuciyarta Na tafarfasa,ita sai yaushe zata ga irin wannan ranar arayuwarta?yaushe zataga wannan abin alherin ya sameta?sai kace 'ya'yanta sune suka fi kowa bakin jini aduniya?ace gasu su hudu kowacce ta isa aure amma sun tasata agaba basuda niyyar motsawa,ko irin zuciyar nan basuda ita dazasu tashi tsaye su San halin dasuke ciki,abin bakin cikin shine Afiya ce kawai ke fahimtar ta,wannan wacce irin masifa ce ta sameta arayuwa?ita haka zata zauna sede taga ana aurar da 'ya'ya banda ita?mikewa tayi da niyyar fita har takai bakin kofa saita ja burki,falo take son zuwa sai tafasa saboda yabon da akema angon Salima,wani lokacin ma gani take kamar dan a b'ata mata rai akeyi,haka ta zaune jugum adaki kamar mujiya sai zare idanu take tana huci,ita yakamata ace hjy kwaise tasa cikin komai ba umma ba wacce yarta ta janyo mata abin kunyah,umma ce ya dace ta b'uya acikin d'aki ba ita ba,da wannan tunanin ta mike akaro na biyu ta fita duk da haushin hjy kwaise dake damun zuciyarta,gabadaya ta tashi hankalinta akan lamarin da batada ikon sawa ko hanawa.
Zama tayi acikin kishiyoyin tana tsine ma umma acikin ranta me cewa"gaskiya Salima tayi goshi kuma tayi sa'ar samun miji kamar Naseer,fatan mu shine Allah ya tabbatar musu da alheri ya kawo Na 'yan baya".
Jiki Na bari mummy ke watsa ma umma harara tace"wannan ay munafurci ne da cin fuska,ki fito fili kice Allah yakawo ma 'ya'yana miji,dadin abin dai kema taki har yanzu tana gabanki,gara su da mutuncinsu yarki fa?".
Da mamaki umma da hjy kwaise ke kallon mummy,karamar dariya mama tayi wacce abun yayi ma sugar,hjy kwaise tace"dadina dake rashin fahimta,kema kinsan ba haka take nufi ba,addua tayi maimakon ki amsa da amin kin fara attacking dinta,fata nagari dai lamiri".
Mummy tace" nasan dani take,toh aniyarki tabiki,in shaa Allah sai kowa yayi mamakin wanda 'ya'yana zasu aura,taki kuwa sede ta tsufa agabanki da banzan hali".banza umma ta baiwa ajiyarta ko kallon gefen da take batayi ba,tacigaba da d'aga wata atampa sky blue color tace"hjy harda hkg ?gaskiya yayi kokari,".da gayya umma tafada saboda ta k'untatawa mummy kuma tayi nasara domin mummy fushi tayi Sosai kana ta miqe tashige daki tana tunanin yadda zatayi maganin umma,harga Allah ta tsani umma tsana mai tsanani,kuma saita cusa mata bakin ciki mara misaltuwa.
Da rakiyar idanu umma tabita tana danne zuciyarta me balbala tana ci da wuta,maganar mummy ta b'ata mata rai matuka,saita sauke ajiyar zuciyah tana cigaba da tunanin Zuci,bata kara cewa komai ba hjy kwaise da Mama ke firar su,sallamar Ya Sadeeq ce tasa umma dagowa gabanta yana tsananin faduwa,kasancewar Ya Sadeeq din be fiye zuwa a irin wannan lokacin ba,sun fi zuwa bayan magrib shida ya Fauza inde bawani abunba akeyi agidan,zuciyarta ce ta tsinke damuwa ta bayyana Sosai acikin idanunta,harshenta na hardewa ta amsa gaisuwar shi tareda tsare shi da idanu,mikewa hjy kwaise tayi tace mishi"Bismillah "suka wuce parlon ta,mama ta kyabe baki tace"uhmm,masu mijin 'ya".ko kallo bata ishi umma ba bare ta tanka mata,gabadaya tunanin umma na kan zuwan bazatar da ya Sadeeq yayi,Allah yasa ba wani abin bane ya faru,part dinta takoma ranta ajagule.
Kimanin mintuna ashirin da biyar sallamar ya Sadeeq ta sauka acikin kunnen umma wacce ke lazimi,abinda ba kasafai yafiye yiba shine shiga part dinsu,anan ta tabbatar da akwai matsala.
Cikeda damuwa tace mishi"me eman tayi".yadda tayi maganar with broken heart ne yasa tausayinta ya kamashi,"bakomai umma ki kwantar da hankalinki,nazo isar da sakon Eman ne".
"Sakon me?"ta tambaya tana zaro idanu,yayi karamin murmushi sannan yace"sakon ban hakuri tace na kawo miki,dan Allah umma kiyi hakuri kidaina fushi da ita".
Shiru umma tayi tana kallonshi batareda tace komai ba,domin Allah ya sani bata San maganar eman sai tazama dole,shirunta ne yasa ya Sadeeq marairaicewa yace"yakamata dai a duba lamarin".yana gama fadin haka ya mata sallama ya fita bayan ya ajiye mata wata yar madaidaiciyar leda,mama dake sa ran zai shigo ya bata tata ledar ta doka tsaki tana fadin"Allah wadaran naka ya lalace ",part din mummy tashiga domin labarta mata,mummy ta rike haba cikeda mamaki tace"lallai Sadeeq bashida mutunci,nima fa bai shigo mini ba".mama tace"wai contract yasamu babba shine yazo tasa mishi albarka ".kamar an caka mata wuka haka mummy taji shigar maganar,kowa na cigaba arayuwa banda ita,yanzu hjy kwaise ta kara musu zarra kenan,tafi su agidan miji sannan 'ya'yanta sunfi nasu nesa ba kusa ba.
Ko rufe baki basuyi ba hjy kwaise tashigo da leda guda biyu,ta mik'a musu tana fadin"Sadeeq yace abaku".kyabe baki mummy tayi tace"Sadeeq yabani mamaki,ya shiga dakin fatima amma yakasa shigowa nawa dakin".
"Ba haka bane,ta yiwu sauri yake"hjy tayi saurin kare Sadeeq,tab'e baki sukayi basu ce komai ba har hjy takai bakin kofa sannan tace"baku gode ba kenan?"
"Mun gode"suka fada atare suna yatsine fuska.
A main parlor taga Abba na kokarin shigewa part din umma,kallon shi take cikeda mamaki,itafa ta manta yaushe rabon daya shiga part dinta balle part din su mummy,saide kowacce ta same shi abangaren shi,amma abin mamaki shine yau ce rana ta uku datake ganin gilmawar shi a part din umma,har ta mike zata shiga sai wata zuciyar ta haneta ga aikata hakan,saita juya tashiga part dinta tana tunanin zuci,Tabangaren Abba ba komai ne yasa yake yawan duba umma ba saidan abinda ya faru,saboda tight schedules dinshi sai weekend yake samun hutu.
Tana nan zaune inda take ya shigo,bata motsa ba amma ta shimfida kyakkyawan murmushi akan fuskar ta,a duniya tayi dace,saide tayi fatan dacewa a lahira,yadda Abba ya tsaya mata ya damu da damuwarta bakowani miji ne zaiyi hakan ba,ita shaida ce domin azaba kawai ta sha a aurenta nafarko.
Cikeda girmamawa ta gaishe shi ya amsa yana jin dadin murmushin datayi,ayanzu burin shi shine yaga bata cikin damuwar komai tadawo fatima ta asali mai yawan dariya.Hira suka tab'a ta nishadi bai yadda sunyi zancen abinda ya shafi eman ba ko abinda zaisa mood dinta ya canza,duk da yasan komai nisan jifa k'asa yake saukowa sannan komai nisan dare gari zai waye haka nan duk daren dadewa saita sauko daga inda tahau na fushi da Eman.
Ya Sadeeq ne yafara dawowa har lokacin ina daki ina aikin kuka,sallah ce kadai ke katse mini shi,ko abinci na kasa dafawa gabadaya na fita hayyacina,kamar ya Sadeeq yasani yataho da takeaway din small chops,ya shigo bakin shi d'auke da sallama yana bin falon da kallo wanda ya dan sauya kamanni,hakan baya rasa nasaba da rashin gyaran dabai samu ba kwana biyu,dakinshi yashiga yayi wanka tana kallon time,5:30pm yagani sai ya sauke ajiyar zuciya tareda zama cin snacks din,wata zuciyar tace go and check on her,yanzu responsibility dinka ce,jiki ba kwari yayi knocking dakina tareda bud'e wa alokaci daya,ya sauke idanunshi akaina,sai ya dan hade rai yana kallon yadda na kudundune acikin bargo,ko wanka ban samu damar yiba,gabadaya namanta da komai sallah ce kawai nake tunawa sai tunanin dazai iya mini illa,hannu yasa ya ja bargon yace"tashi zaune".ba musu Na zauna tareda sunkuyar da kaina kasa,so nake nayi magana amma banida strength din cewa komai,yace"kinci abinci?"d'aga kaina nayi alamar ehh,yace"karya,eman yaushe kika fara karya?".still shiru nayi nakasa magana kuma nakasa kallonshi,yafita bai wani jima ba ya  dawo hannunshi d'auke da karamin tray,snacks ne aciki da ruwan tea,yace"ki daure kici kiyi wanka".gyada mishi kai nayi batareda nace komai ba shikuma ya fita yana kallona kamar me yin nazari,samosa biyu naci naji cikina ya cushe,saina yanke shawarar yin wankan,Sosai naji dadin jikina araina nace dama tun dazu nayi,ban shafa komai ba Na zura rigar material dina peach color,nakoma na kwanta lokacin shida ta karasa,sai bakwai saura Ya Fauza ta dawo.tashigo dakin lokacin ina sallah saita fita,saida tayi sallah tayi wanka sannan ta dawo,sanye take dawata black abaya mai kyau Tayi rolling medium size veil gwanin ban sha'awa,su Anum na biye da ita suma sunyi nasu gayun,tace mini"sorry eman,mun barki ke kadai"tana kare mini kallo,murmushi nake son yi amma nakasa,tace"tashi ki shirya,yau awaje zamuyi dinner"Tana gama fadin haka tafita su Anum suka bi bayanta,sun lura da yanayina shiyasa basa shige mini,ta yiwu kuma ya Fauza ce ta musu magana.
Idan San raina za'a bi ba inda zani,banason fita gabadaya amma babu yadda na iya,hijab dina mustard yellow na zura,dariya su Anum suka fara mini sanda nafito,ya Fauza tace"wear something light ".
Ba musu  Na dauko mayafi,ta kalleni dakyau tace"ko kefa".shiru nayi still kaina akasa muka tafi,amota sai fira suke gwanin ban sha'awa nide banida tacewa wai b'arawo ahannun mata,gusto resto yakaimu,Ya Fauza tafara duba menu din tana tambayar su Anum me zasu ci,ta kalleni Sosai sannan tace "what do you want to eat?".
Ahankali na furta"something hot and spicy".
Tace"nice choice "tana murmushi,saurin sauke idona nayi kasa lokacin da muka hada ido da ya Sadeeq,ya saki karamin murmushi yana cewa"yaushe nazama surikin ki?"ya Fauza tace "tana abu kamar budurwar kauye ba".dariya su Anum sukayi nikuma na rausayar dakaina gefe bance komai ba,Asad yace"ya eman ta zama kurma".hararar wasa Na mishi fuskata babu yabo babu fallasa,Sosai nasha hot and spicy ramayun feeling every taste of it,kuma  ya taimakama appetite dina,ahankali na sauke idona akan ya Sadeeq dawani saurayi tsaye akan mu,bayani yayima ya Sadeeq cewar abashi damar gwada sa'ar shi akaina,saukar da kaina nayi nacigaba da cin abinci ina ma saurayin kallon mahaukaci,ya Sadeeq yace"she's not in her rightful state of mind".saurayin yace"give me your number sai mu riqa communicating".wani kallo ya Sadeeq yayi mishi bece komai ba,Ya Fauza tace "090——"tafada mishi numbar ta,ya Sadeeq yace"numbata ya tambaya not yours,taya zaki ajiye numbar stranger awaya?"da mamaki take kallon yadda Ya Sadeeq yayi fushi lokaci daya, "afuwan,I'm sorry"baice komai ba yacigaba da cin abincinsa shikuma saurayin dako kallon kirki ban mishi ba yayi ma ya Fauza godiya sannan yabar table dinmu,ya Sadeeq bai kara cewa komai ba tunda abun yafaru,tunanin zuci kawai yakeyi yana nazarin dalilin Fauza nason Had'a eman da saurayin bayan abinda yafaru dani recently?

Hmmm 🤔 bamu fara ba,mun dai kusa shiga cikin labarin eman mai cikeda tausayi da sark'akiya.

Zaynab Yusuf✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now