PAGE 36

115 3 0
                                    

EMAAN.......PAGE 36

     With a despairing look Fauxa ke kallon fuskar Sadeeq wacce in few hours ta canxa kammani kamar wanda ya daɗe yana jinya,xafafan hawaye ne suka xubo mata lokacin dataga hancinshi ɗaukeda oxygen yana jan numfashi daƙyar,even unconscious Sadeeq na tsananin jin jiki,runtse idanu tayi ahankali xuciyarta na ƙuna,seeing him on that hospital bed is devasting.and the fact that there is nothing she can do to help him hurts her even more....seeing him sick is the most painful experience for her,xubewa tayi aƙasa tana fashewa da kuka mai ciwo mai cikeda raɗaɗi da karya xuciyar mai sauraro,alameen ne yayi saurin riƙota hawaye na cika mishi idanu ,tausayin fauxa na ratsa xuciyar shi da gangar jikinshi in whole,yadda take kuka mai cikeda tsantsar damuwa ne ke ɗaga mishi hankali,unfortunately at this point baisan kalaman daxai yi amfani dasu wurin bata hakuri ba,gabaɗaya kanshi ya kulle ya rikice,he had  no idea on what to do at the moment,arikice hajiya kwaise tayi closing gap ɗin dake tsakanin su looking at Fauxa keenly with a trembling heart,tsantsar damuwar data gani atattare da Fauxa ne ke breaking heart ɗinta into tiny pieces,tun da ta haifi fauxa bata taɓa ganinta looking helpless ba irin yau,xaunar da ita alameen yayi agefen hajiya kwaise yana kallon fuskar Mamin wacce damuwa ta bayyana asaman ta,rungume Fauxa tayi iya karfinta trying so hard not to cry,idan tayi kuka me fauxa xatayi kenan?ahankali take rarrashinta da kalamanta masu ratsa jiki,"kiyi hakuri Fauxa,accept this with good faith,in shaa Allah Sadeeq xai samu lafiya"jinjina kai kawai fauxa keyi tana kuka mai tsanani,can ta miƙe tashiga ICU tana kallon Sadeeq laying on his sick bed almost lifeless,incident din daya faru daxu ne ke dawo mata vividly,she wished she can went back in time,tayi data-sanin reacting in that way,amma idan batayi hakan ba yaya xatayi amatsayin shi na mijinta datake bala'in so?hannunshi ta riƙo tana shafa gefen fuskar shi with so much love and affection,bakinta na shaking tace"wake up Sadeeq,we've a beautiful life ahead,ni da ƴaƴanka are in so much pain,you know I despise seeing you sick and in pain,my heart aches in your suffering,I'm feeling almost the exact way you're feeling at the moment,dan Allah ka buɗe idanunka even if it's for me or for the kids,ina cikin tashin hankali sadeeq, i don't wanna loose you....."kuka ne mai tsanani ya ƙwace mata saide kukan bame sauti bane amma mai karya xuciyar idaniyar dake kallo ne,tace"this is to remind you that no matter what,you'll always have my backing wannan alƙawari ne na daukar maka,dan Allah ko idanunka ne ka buɗe"tafada tana sake fashewa da kuka.Hajiya kwaise ta kalli gefen da alameen ke xaune but lost in thoughts,bata taɓa ganin alameen in this kind of situation ba,ayini daya ya rame idanunshi sun fada ciki,tsantsar damuwa ce ta bayyana asaman fuskarshi,wacce kallo daya zaka mishi kasan he's going through a lot,runtse idanu hajiya kwaise tayi ganin ƴaƴanta are going through so much pain yet she can't do anything about it,wannan dalilin ne yake ɗaga mata hankali,tace"alameen come closer"tana nuna mishi gefenta,ba musu ya xauna saide bai kalli fuskarta ba,yana avoiding eye contact da ita,saboda yadda idanunshi sukayi jajir kamar wanda ya shekara yana kuka,tace"who am i?"tayi mishi tambayar data sanya tunanin shi tsayawa cak,ya kalleta da hanxari cikeda mamaki,ta sake cewa"tambayar ka nakeyi,wacece ni agareka?"runtse idanu yayi yana jin yadda take mishi tambayar with so much pain,kalamanta babu komai acikinsu sai xallar bakin ciki,yace"you're my mother,my confident,my everything...."jinjina kai tayi tace"inde har dagaske haka nake awurinka then tell me  what your problem is".saurin kallonta yayi akaro na biyu gumi na keto mishi ta koina,ya daɗe baiga tayi laushi irin haka ba,gashi idanunta babu komai sai xallar damuwa wanda hakan ke sashi cikin garari,yana mutuwar son maminsa fiyeda xato da tsammani,yace"you're more than that to me Mami,na miki alkawarin zan fada miki amma let's deal with the problem in hand,Fauxa ce ke buƙatar lallami at this point"kallon datake mishi na gamsuwa ne da maganar shi,amma xuciyrta ta kasa samun sukuni,saboda ita uwace mai tsananin son ƴaƴanta,damuwar su na birkita mata lissafi,kukan su na ɗaga mata hankali,fatanta da burinta shine su dawwama acikin farin ciki mara gushewa,su shimfiɗa rayuwa mai cikeda inganci da farin ciki,amma rayuwa baxata taba kasancewa ahakan ba.tace"fito min da Fauxa daga wurin shi kafin ta samu matsala".jiki ba ƙwari alameen ya shiga ciki yana kallon yadda fauxa ke dirxar kuka saide bame sauti bane,tsanar Eman na karuwa akowani tafiyar lokaci acikin xuciyar shi ,this is all her fucking fault,ta dalilinta xukata dayawa ke cikin bakin ciki,he'll make her life miserable wannan alkawarine ya daukar ma kanshi,Sai Eman tayi kukan da babu hawaye acikin sa,shigowar alameen ce tasa fauxa saurin miƙewa tana ce mishi"he's not responding,nashiga uku na lalace,mijina alameen,ya zanyi?idan ya mutu me zan fadama ƴaƴan mu?"rungumeta kawai yayi yana jin hawaye masu zafi suna sauko masa,yayi dabarar fitowa da ita waje,lokacin su Hajiyar Sadeeq sunxo da babanshi Alhaji kabeer,Bilal na gefe rike da Anum,Asad na kwance ajikin hajiya kwaise,Anum na ganin mamanta ta xo da gudu Fauxa ta tsugunna ta rungume yarinyar iya ƙarfinta tana fashewa da kuka,meyasa tun farko Sadeeq baici albarkacin su Anum ba awurinta???,ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsar ta,hajiyar Sadeeq ce ta xaunar da fauxa assuring her all be well,sannan ta buɗe warmers tana dibar ma Fauxa abinci,Fauxa najin kamshin red stew wacce tasha different proteins taji xuciyrta na tashi,before you know it tafara kwarara amai awurin saboda batada strength din mikewa,hasalima bata San inda toilet yake ba,cikeda damuwa hajiya kwaise ta riketa tana fadin"hasbunallahu wani'imal wakeel"lumshe idanu fauxa keyi tana jin warin abincin yana hawa kanta ,dakyar ta iya furta"take the food away  "da sauri hajiyar Sadeeq ta matsar da abincin,fauxa nata sauke ajiyar xuciya,hajiya kwaise ce ta gyara mata jiki sannan ta kalli alameen tace"akwai boutique near by,siyo mata kaya"jiki asanyaye yatafi yasiyo,lokacin daya dawo har taga doctor anyi mata test,Mami ce tasa mata sabuwar abayar tana kallon fuskar ta wacce ta rine Sosai,ga hawaye sunki daina xubo mata,tace"kinji dai me doctor yace miki,Sadeeq will be fine in shaa Allah,dan Haka kidaina damuwa kodan lafiyar ki da lafiyar abinda kike ɗauke dashi"alameen yace"you mean..."...."she's 2months pregnant "Mami tabashi amsa kai tsaye kuma atakaice,baice komai ba domin azuciya yayi mata adduar samun lafiya.Abba ne ya shigo part din Umma bayan tafiyar su Alhaji Muhammad da mintuna kadan,kwance ya tarar da ita a parlor ta rasa meke mata dadi agidan duniya,tun safe take having this kind of feeling,xama yayi yana kallonta carefully yace"how are you feeling?"dauriyar mikewa xaune tayi tace"alhamdulillah naji sauki"yace"ma shaa Allah,ina Eman?"atakaice ta bashi amsa da "tana daki"musaddiq ne yashigo parlorn yana wasa,Abba yace"xonan auta kiramin Eman"gyada kai yaron yayi yashiga dakin Eman sede kallo daya ya mata yaga bata da lafiya Sosai,jiki asanyaye yace ma Abba"she's sick"Abba ya kalli umma yace"since when?"Umma dake gyara xama tana jin ƙarfin jikinta  alokacin tace"daxu da safe,ina tunanin malaria ke damunta".jinjina kai Abba yayi sannan ya koma part dinshi,numbar alameen yayi dialling yaji akashe,sai ya kira hajiya kwaise,suna xaune kan fauxa asaman laps dinta ya kira wayar,bayan sun gaisa ya tambaya jikin Sadeeq sannan yace"ba alameen wayar"karbar wayar alameen yayi,ta daya bangaren Abba yace"do you know your wife is sick?"cikeda rashin fahimta alameen ya maimaita kalmar wife acikin ranshi,ya kalli mami data kafe shi da ido,yaji gabanshi yayi mummunan faduwa,Abba yace"kayi min shiru,ko bakaji me nace bane?"adaburce alameen yace"ban sani ba"Abba yace"come and take her to the hospital "daga haka ya katse wayar ya bar alameen da baki asake,yafi 10seconds ahaka sannan ya ajiye wayar yana kallon Mami dake wurga mishi kallon tuhuma,dakyar ya mike yace"Abba na kirana"daga haka yafita daga asibitin xuciyar shi na ƙuna.driving yake yana tunanin yadda rayuwar shi ta jagule within few days.A main parlor ya tarar da Abba da mummy suna maganar events din bikin Afiya,wanda xa'a fara nan da 3 days,saida yajira suka gama maganar sannan ya kalli Abba me cewa"kada ka fadawa kowa maganar auren ku,I'll do that myself idan lokaci yayi,now go and take her to the hospital "daga haka Abba ya wuce part dinshi ya bar alameen xaune awurin kamar statue,yafi minti goma yana tunanin yadda xai iya kai Eman asibiti,shida ko ganinta baya kaunar yi balle yayi mata hidima,abu daya yaji xai iya yi shima saboda Abba ne yayi mishi magana,kuma ya tabbatar xuwa anjima xai nemi bayani daga wurin shi,part dinshi ya shiga ya dauki fasasshiyar wayar shi ya fita,sabuwar waya ya siya latest iphone sannan ya kira Dr Maryam wacce time to time take zuwa gida duba su hajiya kwaise idan minor cases arises ,atare suka shigo gidan ya nuna mata part din umma sannan ya wuce part dinshi yana dialling numbar Yasmeen wacce  ta mishi more than 10 missed  calls,yayi mamaki Sosai saboda normally one missed call kawai take mishi tun asali,tana kwance akan expensive Italian bed taga kiranshi,saurin picking tayi tana sauke ajiyar xuciya batareda cewa komai ba,shine yace"my yasmeen,how are you doing?"kukan shagwaba ta fashe da shi wanda yake gigita mishi lissafi,baya son kukan nan nata,yace"I'm sorry babe,nayi deserving punishment daga wurinki ,punish me my love "tana shesshekar kuka tace"ni kayi ignoring ko?"yayi saurin cewa"noo sweetheart,kinsan I'll never do that,unforeseen consequences ne sukayi arising "tana kukanta mai cikeda shagwaba tace"come right now,I want to see you "tana gama fadin haka ta kashe wayar without listening to his response.ajiyar xuciya ya sauke yana tunanin yakamata yayi mata abinda takeso,afterall shi me laifi ne awurinta,sannan yayi missing dinta beyond imagination,shiryawa yayi ya tafi ko takan dr Maryam dake part din Umma bai bi ba,hasalima ya manta da hakan acikin ranshi ....Dr Maryam ce ta yaye bargon da Eman ta lulluɓa dashi,takai hannunta tana tattaba wuyan eman xuwa goshinta to feel her temperature wanda yayi high Sosai,fuskar Eman ta kalla wacce hawaye ke sauka ahankali suna gangarawa down to her cheeks,few seconds tayi tana kallon nata tace"can you please tell me how you're feeling?"juya kai Eman tayi ahankali saboda tsananin ciwon dayake mata,lips dinta na shaking tace"headache and fever..."dubata dr maryam tayi thoroughly sannan ta mayar da bargo ta rufeta..Umma dake kwance a parlor tayi saurin miƙewa xaune tace"ya jikin nata?"xama dr maryam tayi tace"it's nothing serious,lemme get the drugs"fita tayi bata jima ba ta dawo da few drugs sai injection guda daya,Kukan Eman ne ya tsananta ganin allura ahannun dr Maryam,saurin runtse ido tayi tana jin shigar allurar cikin jikinta,cikin ikon Allah within few minutes tafara jin saukin xaxxabin,ciwon kan ma ya ragu sosai,Har daki Saliha takai mata abinci,Umma dake xaune agefen ta taxuba musu a plate sukaci,even though bawani ci tayi sosai ba,ta sha drugs sannan takwanta tana tunanin auren da aka daura mata da alameen ,even the thought of that makes her heart papiltate,har lokacin ta kasa daina kukan tausayin kanta dakuma tausayin rayuwar ta.
He spend more than two hours yana lallashin Yasmeen har ya samu ta sauko tadaina fushi dashi,asibitin ya koma ya tarar daga Mami sai Fauxa da Bilal,hajiyar Sadeeq takoma da yaran gida,xama yayi yana kallon fauxa wacce idanunta ke lumshe yace"how are you feeling?"murya can kasa tace"alhamdulillah "hajiya kwaise tace"tashi mu tafi",Fauxa ta marairaice tace"one more time pls"tafada tareda shiga ICU wurin Sadeeq wanda har lokacin bai tashi ba,hasalima sound din computer ce ke tabbatar da yana numfashi,as usual xama tayi ta riqo hannunshi tana kuka Sosai kamar xuciyarta xata fito waje,ta dade Sosai tana kallonshi sannan ta fita gabanta yana tsananta faduwa,sunan Allah take kira har suka shiga gida,Umma ce tafara shiga tayi mata ya jiki gamida tambayar lafiyar Sadeeq,,kuka Fauxa ta fashe dashi instead of answering Umma,ita tasan babban ciwo ne yakama Sadeeq but the stupid doctor is saying something else.basu dade da tafiya ba Dr Ammar yakira Alhaji kabeer xuwa office dinshi,saida ya kalli shi carefully sannan yace"to be honest babu abinda xamu iya ma Sadeeq awannan gaɓar,he's not responding to medication,we tried our possible best but he's yet to even lift his eyelashes which is very dangerous domin I'm afraid ya shiga coma"Gaban Alhaji kabeer ne yayi mummunan faduwa yace"are you out of your senses?kasan me kake cewa kuwa?"cire farin glasses dinshi yayi yace"Alhaji kabeer relax,I'm yet to tell you what should be done "yacigaba da cewa"Sadeeq is alive ka ajiye wannan acikin ranka,but cannot be woken up and he shows no sign of awareness and appears to be unresponsive,if I should be honest with you babu asibitin daxai iya warkar da Sadeeq akasar nan saide bansan wani iko na ubangiji ba,amma advicebly ku kaishi Mayo clinic dake US,sunada world class facilities and top notch services,I'm hopeful idan kuka je can Sadeeq xai iya tashi ya dawo normal kamar wanda bai taɓa ciwo ba"Alhaji kabeer da hawaye ke xubo mishi yace"what happened to him?"dr Ammar yace"yakamu da chronic heart disease da severe head injury "few Phone calls Alhaji kabeer yayi aka musu arranging tafiyar,hajiyar Sadeeq ce tabada shawarar abar Fauxa agida for the mean time,idan cikinta yayi kwari saita bisu nan da 2 weeks in shaa Allah,Abba naxaune afalo yana kallon News yaga kiran Alhaji kabeer,cikeda damuwa Abba ajiye wayar sannan ya shiga part din hajiya kwaise yana kallon Fauxa dake kwance hawaye sai sauka suke daga idonta. Xama yayi yana kallonta cikeda tausayawa,Hajiya kwaise na gefenta ta riqe plate ahannu mai cikeda abinci tana son ba Fauxa amma taki bata haɗin kai,Al'ameen na xaune shima yana lallashinta tayi banxa dasu,Abba yace"kiyi hakuri fauxa,ki dauki wannan kaddarar taki da kyakkyawar xuciya,Allah yana tare dake"ya kalli hajiya kwaise wacce jikinta yayi sanyi yace"gobe da safe xasu wuce da Sadeeq US,xasu kawo yaran anjima,try your best to calm her down "fauxa najin haka ta sake fashewa da kuka mai tsananin sauti tana danna kanta acikin pillow,hankalin Mami ne ya tashi ta rasa me xatace mata awannan lokacin,alameen kanshi ya rikice da irin kukan da fauxa keyi,asanyaye Eman tashigo falon tana jinta sama sama kasancewar har lokacin jikinta babu karfi,ko sallamarta basu amsa ba yadda hankalinsu ya tashi sosai,Zama Eman tayi ta dafa shoulders din Fauxa tace"Ya fauxa...."jin voice din Eman yasa ta saurin tashi ta rungume ta iya karfinta tana kuka mai tsanani,Eman couldn't help but cry alokacin,sunyi kuka mai yawa sannan Eman tace"enough ya fauxa,adduar mu kawai yake bukata awannan lokacin"gyada mata kai Fauxa keyi tace"meyasa xan daina kuka?how will i do that?"eman tace"but you've to"Fauxa tace"how?tell me how to "shiru Eman tayi tana sauke ajiyar xuciya tace"by trusting the almighty,Allah alone is sufficient for us Fauxa,ki koma gareshi in shaa Allah xaki samu sassauci"shiru fauxa tayi tana sauke deep ajiyar xuciya,tace"are you sure he'll be okay?"cikeda damuwa Eman ta gyada mata kai alamar tabbatar wa,alameen dake gefe yana jin kamar ya shake Eman ya huta,tsanarta ke yawo acikin xuciyarshi tana bin koina na jikinshi ,maganganun datake yi ynxu ke ƙona mishi rai,so yake ya yabar wajen amma he can't do that saboda fauxa,he promised to be there for her acikin kowani yanayi.Bayan magrib Fauxa tashiga part din umma tana kallon Eman dake kwance asaman kujera,tace"dauko hijab dinki muje"da dan mamaki Eman ta ɗago tana kallon Fauxa waccce xuwa lokacin ta daina kuka saide idanunta sunyi luhu-luhu,Eman tace"to"sannan ta sa dogon hijab dinta suka fita xuwa compound,hajiya kwaise na bayan motar alameen ta ce"ban San meyasa fauxa ke ƙaunar Eman ba,yadda take sakewa da ita ko dasu inteesar batayi,xuwa asibitin ma saida ta jajibo ta"shiru alameen yayi baice komai ba domin ya fada duniyar tunani,yana jin bai kyauta ma mamin shi ba,lumshe idanu yayi asanyaye yana kallon fauxa data xauna a front seat,Eman da gabanta ke tsananin faduwa ta bude back seat ta xauna tareda sunkuyar da kanta kasa,wani irin kallo hajiya kwaise ke mata tana ɗora naxarinta akan mixanin hankali,she detest yarinyar for what she does,atakure Eman ke xaune gabanta nata faduwa,ajikinta taji ana kallonta hakan yasa ta ɗago asanyaye tana kallon gefen Mami,saurin saukar da idanunta tayi ganin irin kallon da mamin ke mata,bawai kallon wulakanci bane amma kallone wanda kamar akwai abinda take son tabbatarwa  daga wurin Eman din,ahaka suka Karasa asibitin babu me cewa kowa komai,fauxa ce tayi saurin shiga wurin Sadeeq ko kallon Alhaji kabeer dake wurin batayi ba,alameen da Eman ne suka bita ciki,xama tayi saboda yadda kafafuwanta ke rawa,ayadda suka barshi daxu haka suka tarar dashi,dalilin daya sa hawaye fara sauko ma fauxa kenan,ta ɗan juyo tana kallon Eman sannan tace "kinga halin da yaya Sadeeq yake ciki ko?"tafada cikeda  karyewar xuciya,hawayen dake maƙale a idon Eman ne suka gangaro saboda tsananin tausayin Sadeeq,akan lips dinshi idanunta suka fara sauka wanda yayi fari alamar bushewa,difference din Sadeeq da gawa itace computer dake making sound alamar he's still breathing,duk me imani idan ya kalli sadeeq saiya xubar mishi da hawayen tausayi,kallonshi take remembering alot of this,abubuwan dasuka faru tsakaninta dashi ne ke dawo mata,tana tuna yadda yake nuna tsantsar ƙaunarta which she's quite sure baxata sake samun me kaunarta kamar Sadeeq ba,tana iya hango tsantsar soyayyar ta acikin idanunshi wacce babu algus ko sirki acikinta,he loves her with passion and every fibre of his being,runtse idanu tayi hawaye na xubo mata non stop,ta riƙe karfen gadon da karfi xuciyarta na bugawa da sauri da sauri,alameen dake can xaune yana kallon yadda Fauxa ke kuka kamar xata amayar da xuciyrta,unknowingly idanunshi suka sauka akan Eman wacce ta lumshe idanu tana kuka kasa-kasa,kamar ya tashi ya kikkifa mata mari haka yakeji saboda takaicinta,siririn tsaki ya saki yana ayyana cewar her turn is next inde cin amana suka sa agaba karshen su baxaiyi kyau ba...bakin Fauxa na rawa tace"till we meeet again Sadeeq,know that I'll always love you,don't ever think of giving up,saboda dani da yara will be patiently waiting for you "ta ɗora hannunshi akan mararta tace"I can't wait to break this news to you"tafada tana murmushi tareda kuka,runtse idanu alameen yayi yana jin maganganun fauxa har cikin ranshi.....




Dedicated to my lovely Mum UMMU FAISAK💕💕


Zaynabyusuf✍🏼
09037909996

EMAANDonde viven las historias. Descúbrelo ahora